Oct 22, 2017 07:16 UTC

Suratur Rum, Aya ta 9-13 (Kashi na 731)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

---------------------------------------/

To Madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraen karatun aya ta 9 da kuma aya ta 10 a cikin suratul Rumu:

 

أَوَلَمْ يَسِيرُوا فِي الأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ كَانُوا أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَأَثَارُوا الأَرْضَ وَعَمَرُوهَا أَكْثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَاءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانَ اللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
 

9-Shin me ya sa ne ba za su yi tafiya a bayan kasa bas u ga yadda karshen wadanda suka gabace su ya zama? Sun kasance sun fi su tsananin karfi. Sun kuma noma kasa sun kuma raya ta,kuma manzanninsu sun zo musu da ayoyi abayyana,to Allah bai kasance Mai zaluntar sub a ne,sai dai kuma kansu suka zamanto suna zalunta.

 

ثمَّ كَانَ عَاقِبَةَ الَّذِينَ أَسَاؤُوا السُّوأَى أَن كَذَّبُوا بِآيَاتِ اللَّهِ وَكَانُوا بِهَا يَسْتَهْزِؤُون

10-Sannan kuma karshen wadanda suka munana ya kasance mummunan sakamako,dan su karyata ayoyin Allah ,kuma sun kasance suna yin izgili gare su.

A cikin shirin da ya gabata kun ji cewa; Allah ya bukaci wadanda bay i imani ba da ranar tashin kiyama da su yi tunani da nazari a cikin halittar sammai da kassai da halittar su kansu ta haka za su fahimci wannan duniya an halicce ta ne cikin hikima da buri kan gaskiya.To wadannan ayoyi na cewa; me ya sa ba mu daukan darasi a cikin abubuwan da suka wakana a baya? Me ya sa ba za mu yi tafiye-tafiye ba a bangarori daban daban na wannan duniya domin ganewa idanunmu abin da ya faru kan al'ummomin da suka karyata da daukan darasi ? Mutane da al'ummomin da suka mallaki manyan lambuna da gonaki da arziki da dukiyoyi masu yawan gaske ba iyaka amma a dalilin karyatawa da musanta gaskiya  sai munanan ayyukansu ya bayyana da karshensu yay i muni ba shakka. An hallakar da su ne karkashin sakamakon ayyukan da suka aikata na son rai da bijirewa karbar gaskiya da kiran shiriya na annabawa da manzonni. Saboda haka a al'adar musulunci kamar yadda ake hukumta zalunci kan wani haka ake hukumta zalunci kan kanka da kuma dukan biyun . Wannan sabani koyarwar yan baruwanmu da addini  da suka bawa mutum yanzu da zabi ya aikata duk abin da ya ga dama matukar ba zai shafi cutar da waninsa ba  amma a musulunci hatta cutar da kanka zalunci ne kuma b aka da hakkin cutar da kanka balantana waninka kuma wannan koyarwa ta yi daidai da hankali da adamtakar mutum.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko: yin bulaguro da ziyarce-ziyarce zuwa yankun da sassa na wannan duniya da ganewa ido abubuwan da suka faru a tsawon tarihi yana taimaka mana a rayuwa da daukan darasi.

Na biyu:Tarihi yana ci gaba ne da sabawa karkashin tsari da daukan darasi a rayuwa.

Na uku:sa'ada da jin dadin al'ummmomi ba kawai ta hanyar karfin iko da dukiya da ci gab aba ne wannan a zahiri ke nan amma sa'ada ta gaskiya tana karkashin imani da Allah da Manzonninsa da aikin mai kyau da dacewa.

Na hudu:nacewa kan aikata sabo da maimata aikata sabon ,na kai mutum ga mummunan sakamako da karyata gaskiya da yi wa gaskiya izgili.

*******************MUSIC***********

To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 11 zuwa ta 13 a cikin wannan sura ta  Rum:

 

اللَّهُ يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

 

11-Allah ne Yake farar halitta sannan Ya mayar da ita bayan mutuwa,sannan kuma gare Shi za a komar da ku.

 

وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يُبْلِسُ الْمُجْرِمُونَ

 

12-Kuma ranar da alkiyama za ta tashi, a wannan ranar ne kafurai za su yanke kauna daga rahama.

 

وَلَمْ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَائِهِمْ شُفَعَاء وَكَانُوا بِشُرَكَائِهِمْ كَافِرِينَ

 

13-Ba kuwa su da wasu masu ceton su daga abokan tarayyar ta su, za su ma kasance masu kafirce wa abokan tarayyar tasu.

Karkashin ayoyin kur'ani mai tsarki ,mutuwa ba ta nufin karshen rayuwa a wannan duniya  kuma kabari wani shimge ne da muke bi a wannan duniya domin isa wata duniya wato Lahira. Kamar yadda haifuwa da uwa key i wa da ba yana nufin karshen rayuwar mutum a cikin uwa ba illa wata hanya ta isa ga rayuwa a wannan duniya. Wadannan ayoyi na cewa: haihuwa da mutuwa a wannan duniya bay a karkashin ikon mu ba ne haka dawwama da akasinta duk suna hannun Allah ne da zartar da abin da ya ga dama kamar yadda zai sake tayar da mu a gobe kiyama karkashin iko da iradarsa ko mun so ko mun ki dole a tayar da mu. Saboda mu yi aikin da zai ceto rayuwarmu a gobe kiyama ba aikin da za mu ciza yatsa ba da yin nadama a lokacin da ba ta da wani amfani.,

Wadanda kuke ganin za su taimaka maku a lokacin da kuke neman taimako to a gobe kiyama ba za su iya taimaka maku da komi bas u ma ta kansu suke  domin aikin da suka aikata bas hi da bambanci da na ku aiki. Hatta su mushrikai da suke ganin gumaka ne za su kubutar da su da yi masu ceto a ranar kiyama ,a ranar za su fahimci duk wani abu da bas hi da rai  da karfin tafiyar da lamura a wannan duniya bas hi da wani amfani a kanran kansa balantana ya taimakawa waninsa.Bayan guiwarsu ta karye da yin nadama gaba da baya ,uwa uba hatta fatar rahamar Allah da lutifinsa ya shafe bas u yi  saboda tun a wannan duniya sun karyata annabawa da manzonni .Kaicon su kuma tabewa ta kai tabewa a wannan rana da kowa ke fatar gamuwa da rahamar Allah.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

Na farko:tsari da halittar wannan duniya da abin da ke cikinta sun fara ne daga Allah kuma a gare Shi ne za mu koma baki daya kuma sha'afa kan hakan zai kai mutum ga babbar nadama ta karshe.

Na biyu:Duk wani jin dadi da farin cikin masu sabo da banna a wannan duniya ne don haka kar su birge mu domin a ranar lahira za su dandana gudarsu.

Na uku: a ranar kiyama kauna da dangantakar da aka kula ba kan gaskiya da tushe na hakika ba za ta koma ta rikide da gaba da kyamarjuna kuma duk wani wanda ya rungumi wani mai ceto ba Allah  da waliyansa bay a tabe a wannan rana.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags