Oct 22, 2017 07:23 UTC

Suratur Rum, Aya ta 14-19 (Kashi na 732)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC***************

To madallah jama'a masu saurare a yau za mu fara shirinmu ne da sauraren karatun aya ta 14 zuwa aya ta 16 a cikin suratul Rum:

 

وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ

 

14-Kuma ranar da alkiyama za ta tashi a wannan ranar ne mutane za su rarrabu.

 

فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَهُمْ فِي رَوْضَةٍ يُحْبَرُونَ

15-Sannan wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi ayyuka nagari,to su za a faranta musu rai cikin aljanna.

 

وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَلِقَاء الآخِرَةِ فَأُولَئِكَ فِي الْعَذَابِ مُحْضَرُونَ
 

 

16-Amma kuma wadanda suka kafirta suka kuma karyata ayoyinmu da haduwa da ranar lahira,to wadannan za a halartar da su cikin azaba.

Wadannan ayoyi na bayani kan mutane zuwa gungu biyu a ranar tashin kiyama.Gungun farko su ne ma'abuta imani da ayyukan kirki da suka yi ayyukan alheri da neman yardarm Allah a wannan duniya da kuma suka bi umarnin manzonninsa da suka zo mana da shiriya  . Sai kuma gungu na biyu da ya kafircewa ni'imar Allah da kiran shiriya manzonni da annabawa . Kuma wannan gungu na biyu shi ne gungun wadanda suka aikata sabo da banna a rayuwarsu ta duniya. Abin da a wannan ake fifita mutane da su kamar shekaru,ilimi,jinsi da launin fata ko harshe da yare da kudi da makami da daraja ta zahiri da sauransu to a ranar tashin kiyama bas u da kima ko kadan da tasiri ,kawai abin da ake la'akari da kuma yake tasiri a ma'auni  shi ne imani da ayyukan alheri da mutum ya aikata a wannan duniya  sai kuma dayan ma'aunin kafirci da mummunan aiki. Abin lura a nan imani sai an hada shi da ayyukan alheri zzai sa mutum ya shiga aljanna  amma shi kafirci kadai ya isa ya kai mutum shiga wutar jahannama ko da kuwa bai aikata wani sabo ba a rayuwarsa.Dalili shi kafirci a karan kansa zalunci ne da jari babba na kai mutum shiga wuta don haka mu yi hatta.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko: Kiyama rana ce ta bambance mutanan kirki da lala wato mutanan da suka aikata ayyukan kirki da wadanda suka aikata banna .

Na biyu:ayyukan alheri shi ke da kima da daraja  kuma shi ne tushe da madogara da ya samo asali daga imani da yardarm Allah.

Na uku: karyata ayoyin allah da ranar kiyama yana daga cikin ruhin kafirci da jayayya ta mutum kafiri.

Na hudu: makomar mutum a lahira tana karkashin ayyukansa na alheri da imaninsa a wannan rayuwa ta duniya.

 

Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 17 da 18 a cikin wannan sura ta Rum:

 

فَسُبْحَانَ اللَّهِ حِينَ تُمْسُونَ وَحِينَ تُصْبِحُونَ

 

17-Ku tsarkake Allah da yin salla sanda kukashiga lokacin maraice  watau sallar Magariba da lisha. Da kuma yayin da kuka wayi gari watau sallar Asuba.

 

وَلَهُ الْحَمْدُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَعَشِيًّا وَحِينَ تُظْهِرُونَ

 

18-Yabo kuma nasa ne a cikin sammai da kassai da kuma yayin da kuka yi yammaci watau sallar la'assar da kuma shigowarku lokacin garjin rana watau sallar azahar.

Wasu daga cikin masu fassara sun yi imani cewa: wadannan ayoyi ya kamata a rika karanto su a cikin salloli na wajibi a cikin salloli na rana ko na dare da cewa;  a cikin dare ko safiya da lokaci na azzahar da la'asar mutum ya kasance mai tunawa da allah da yi masa hamdala wato godiya da kuma tasbihi kuma ya nucu kan wannan lam,ari na ambaton Allah da gode masa. Saboda  duk wani abu mai rayuwa da linfashi  yana karkashin ikonsa  da kudurarsa kuma wannan alama ce ta ilimi da kudurarsa maras karewa.  Idan mutum yana son yi nisa da kaucewa ayyukan shirka ya kasance mai yawaita yin tasbihi a rayuwar ta zucci da harshensa da kuma tunaninsa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Godiya yin tasbihi ga allah  ya dace a kowane lokaci da guri da duk yanayi da mutum ya samu kansa.

Na biyu: Tasbihi ga allah yana tsarkake Allah da duk wani datti da gurbatar tunani.

*************MUSIC*********

To Madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 19 a cikin suratul Rum:

 

یخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَيُحْيِي الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَكَذَلِكَ تُخْرَجُونَ
 

 

19-Yana fitar da rayayye daga matacce kamar dantsako daga kai ,yana kuma fitar da matacce daga rayayye kamar kwai daga dan tsako , kuma yana kasa bayan bushewarta .kamar haka kuwa ne za a fito da ku.

 

Wannan ayar wani maida martini ne kan shagube da karyatawar da wasu ke yi kan abkuwar mai abkuwa inda wannan ayar ta kawo misali na rayu da mutuwa a wannan duniya da cewa; ta yaya za a tayar da masu rai bayan sun mutu a ranar tashin kiya to abin mamaki yadda suke mamaki  hakan ga wanda ya halicci kowa da kowa kuma hatta a wannan duniya Allah yana samar da mai rai daga matacce da kuma samar da matacce daga mai rai  kuma haka wannan rayuwa take tafiya a wannan duniya dare da rana kullum. Kamar yadda ake rana kasa bushahhsiya da tsiirre da suka bushe da sabkar da ruwan sama da sake raya su su yi shanwa shar.Hatta ruwan da muke sha a kullum bas hi da rai amma da zarar ya shiga jikinmu sai ya zama kwayoyin halitta da rayuwa .Wasu kuma sun fassara wannan ayar da yadda ake samin kafiri daga mumuni da kuma akasin haka a samu mumuni daga kafiri.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Idan mutum yana da tunani da hankali da aiki da hankalinsa bai dace ba yayi shaku kan lamarin tashin kiyama saboda allah yanada karfi da kudurar zarta da abin da yafi lamarin tashin kiyama kuma shi ne ya halicce mu da farko sake tayar da mu ba zai bas hi wahala ba amma ga mai hankali.

Na biyu:a tsari na ryuwa a wannan duniya abubuwa na kewayawa ne daga mai rai zuwa matacce da kuma matacce zuwa mai rai.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags