Oct 22, 2017 07:30 UTC

Suratur Rum, Aya ta 20-22 (Kashi na 733)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah za mu fara shirin nay au ne tare da sauraren karatun aya ta 20 a cikin wannan sura ta Rum.

 

وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ إِذَا أَنتُم بَشَرٌ تَنتَشِرُونَ

 

20-Yana daga ayoyinsa cewa: Ya halicce ku daga turbaya, sannan kuma sai ga ku mutane warwatse a bayan kasa.

A cikin shirin da ya gabata mun yi bayani ne kan kudurar Allah ta raya matacce daga mai rai da kuma yadda yake kashewa da rayawa. To wannan ayar da sauran ayoyin da za su zo bayanta suna bayani ne kan kudurar Allah  a halittar halittu  musamman mutum  da cewa: tushan halittarmu mu mutane  da kmuke rayuwa a doran kasa a yanzu  daga kasa ne wadda ba ta da rai. Har ila yau wannan ayar tana nuni ne kan tushen abin da aka halicci mutum da shi wato turba da aka halicci kakanmu tushen duk wani mutum a wannan duniya daga kasa ko turba kamar yadda wasu ayoyin kur'ani suka yi nuni da hakan .Hatta abinci da mutum ke ci da rayuwa da shi wannan ayar ta yi nuni da shi  da cewa: kai tsaye ko ba kai tsaye ba mutum na samin abincin da zai ci ne daga kasa  da wannan ke nufin daga kasa muke haka abincinmu da shanmu daga kasa kuma a gare ta ne za mu koma.

Idan mutum yayi dubi kan halittarsa da yadda rayuwarsa ke gudana da kuma yadda aka halicce shi da kuma aka halicci wannan duniya  daga kasa maras rai  amma Allah ya samar da kyayoyin halitta da kuma samar da ci gaban ilimi a fannoni daban daban da raya kasa da tafiyar da lamarin ta cikin tsari da hikima  da kawo sauye-sauye da canje-canje  da ke taiumakawa mutum a lamurran rayuwa da ci gabansa wannan wani lamari ne na ban mamaki da al'ajabi.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da fahimtar wasu abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:mutum ya san kansa wani mataki ne na farko na sanin Allah kuma mutum shi ne halitta mafi girma da daraja da Allah ya halitta a doran kasa.

Na biyu:dukanmu mutane daga kasa aka halicce mu kuma a kasa za mu koma don haka kar mu yi ko nuna jiji da kai da dagawa.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun aya ta 21 a cikin wannan sura ta rum:

 

وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

 

21- Yana kuma daga ayoyinsa cewa Ya halitta muku matanku daga kanku don ku samu nutsuwa gare su Ya kuma sanya soyayya da jin kai tsakaninku ,hakika a game da wancan lallai akwai ayoyi ga mutane masu tunani.

Har yanzu nuna kan Magana da bayani kan halittar mutum inda wannan ayar da muka saurara  tana daya daga cikin ayoyin da ke bayani kan girma da daukaka da kudurar Allah  wanda ya samar da dokar auratayya da cewa:Allah madaukakin sarki cikin hikimarsa ya samarwa kowane mutum aboki ko abokiyar tafiya don taimaka masa a lamarin tafiyar da rayuwa da samar masa da nucuwa da kwaciyar hankali da rayuwa a kusa da shi koi ta. Bugu da kari ya samar da soyayya da kaunar juna a tsakanin ma'aurata da shakuwa da juna ,daya y aba son rabuwa da dan uwansa a tsawon rayuwarsa. Wannan hadi tsakanin mace da namiji  na nuni da daya cikon kamala ne na dayan. Kuma wannan kauna c eke taimakawa wajen yawaita da binkasar bil adama da iyali da samar da al'umma mai girma da rayuwa ta zamantakewa  mai armashi da girma da binkasa da ci gaba ta dukan bangarorin rayuwa da addini.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da fahimtar wasu abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:mace da namiji tushensu guda ne sabani masu ra'ayi sabanin haka.

Na biyu:a koyarwa da al'adun musulunci ,rayuwar iyali it ace rayuwa kuma ma'aurata da rayuwar aure na samar da kwanciyar hankali da nucuwa ba samar da sabani da rarrabuwa da tashin hankali ba.

Na uku:Kauna da soyayya wata babbar kyauta ce daga Allah madaukakin sarki da ya samar a tsakanin ma'aurata da kuma ke tallafa masu wajen gina rayuwar aure mai tsafta da karfo.

Na hudu:Kamar yadda kauna da soyayya ke kara dangon rayuwar ma'aurata haka a kullum rayuwa da zama tare ke bukatuwa  da kauna da son juna a tsakani.

*********************MUSIC***************

To madallah za mu saurari karatun aya ta 22 a cikin wannan sura ta Rum:

 

وَمِنْ آيَاتِهِ خَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلافُ أَلْسِنَتِكُمْ وَأَلْوَانِكُمْ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّلْعَالِمِينَ
 

 

22- Kuma halittar sammai da kassai da kuma sassabawar harsunanku da launukanku. Suna daga ayoyinsa. Hakika a game da wancan lallai akwai ayoyi ga ma'abuta sani.

Wannan aya tana bayani kan halittar mutum da kuma sauran halittu da ke rayuwa tare da shi a doran kasa da cikin kasa da sammai  da haka ke nuni bayan sanin karan kansa shi mutum yana bukatuwa da sanin sauran halittun da ke kewaye da shi a wannan duniya .Duk da tauraren dan adama masu yawan gaske da gine gine da kere keren na'urori barkatai na ci gaba da ganin kwakwab ,mutum har yanzu ya kasa gano zurfin halittar da ke sammai da wasu halittun ma kamar tauraro.Haka dubbai da sama da miliyoyin halittu iri iri a cikin karkashin kasa da ruwa mun kasa gano su. Haka lamarin yake dubbai ma'adunai da arzikin da ke karkashin kasa  kamar man fetur,gaz da Uranuim da zinariya da azurfa da tagulla da karfe da lu'u-lu'u mun kasa gano yawansu da kalolinsu haka sauran halittu kamar su kifi da kalolinsu.

Wannan ayar ta sake yin nuni da darajar da Allah ya bawa mutum inda y aba mu yarurruka masu yawa daban daban da kuma fuskoki d launin fata mabambanta.Shin da a ce dukan mutne launinsu daya ne kamarsu day ace tsayi da kibarsu daya ne suna kama da juna  to da ta yaya za mu gane wane ne wane ba wane ba? Shin hatta da ta yaya zai gano ma'aifinsa ko ma'aifiyarsa a tsakanin dubban mata da maza? Shin ta yaya mata mo namiji zai gane matasa ko mijinta ne ? Wannan na daya daga cikin hikimar Allah t sassabawar launinmu da kuma kamanninmu da harsunanamu da tsayi ko kibarmu  ko fahimtar juna da kuma jin dadin rayuwarmu ta zamantakewa da ba ta armashi .Misali idan da z aka shiga wani gari sai ka tarar motocin garin baki daya irin daya ne launi daya yaya z aka ji a ranka da rayuwarka.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Ilimin zahirin rayuwa na taimakawa mutum wajen sanin rayuwa ta dabi'a da ci gabansa kan sanin karfi da kudurar Mahalicci da kuma hikimarsa ta halittar halittunsa.

Na biyu:A mahangar masana sassabawar launin fatarmu da harsunanmu da kabilunmu na nuni da karfi da girman Mahaliccinmu amma su jahilai wannan sassabawar na kollonta a matsalin rauni da izgili da nuna fifiko a tsakanin mutane.

Na uku:Ko wane harshe a karan kansa yana da tushe da asali da daraja saboda babu wani da ke da hakkin muzguna wani yare ko kabila da kaskantar da wani yari don fifita wani yaren.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags