Oct 22, 2017 07:45 UTC

Suratur Rum, Aya ta 23-26 (Kashi na 734)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare a yau shirin namu na hannunka mai sanda za mu fara ne da sauraren karatun aya ta 23 da 24 a cikin suratun Rum:

 

وَمِنْ آيَاتِهِ مَنَامُكُم بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَابْتِغَاؤُكُم مِّن فَضْلِهِ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ
 

23-Kuma baccinku a dare da rana da neman falalarsa suna daga ayoyinsa.Hakika a game da wancan lallai akwai ayoyi ga masu ji na lura.

 

وَمِنْ آيَاتِهِ يُرِيكُمُ الْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنَزِّلُ مِنَ السَّمَاء مَاء فَيُحْيِي بِهِ الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
 

24-kuma nuna muku walkiya da yake yi don tsoratarwa da kwadaitarwa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama,sannan ya raya kasa da shi bayan bushewarta suna daga ayoyinsa.Hakika a game da wancan lallai akwai ayoyi ga mutane da suke hankalta.

A cikin shirin da ya gabata mun yi bayani ne kan ayoyin kur'ani a cikin suratul Rum da suka yi bayani da nuna mana matsayi da daukakar Allah da kuma kudurarsa a halittar mutum  da duniya baki daya da abin da ke cikinta to wadannan ayoyin da muka saurara suna bayani ne wa wasu ni'imomin da Allah yay i mana a rayuwa  don ta kara armashi da jin dadi da samin damar mu gode masa  inda wannan ayar ke cewa: tana yuyuwa wasu su yi zaton tsarin yin barci da aka samar mana wani abu ne mai sauki  amma idan muka lura da kyau shi barci da falkawa shin da dare ne ko da rana yana kumshe da hikima da tsari daga Mahalicci domin a duk lokacin da mutum ya gaji idan yayi barci ya tashi zai samu nucuwa ta gangar jiki da ta ruhu da samin karfin jiki da jin kwarjinin yin aiki da ci gaban rayuwa babu kasala ko mutuwar jiki.

Haka walkiya da tsawa daga sama da ke sanya mana tsoro wani lokaci wata alama ce ta sabbar ruwan sama da rayuwar dabbobi da mutum da tsirre da ita kanta kasar ke dogara .Idan wani yanki ya fuskanci jinkirin sabbar ruwan sama ,mazauna wannan yanki da sauran halittu masu rai za su kausa da jin kasa da fuskantar hatsarin ci gaba da rayuwa a wannan yanki. A yau domin isar da bututun man fetur ko na Gaz daga matatar zuwa wani gari ko yanki da kauyuka ana kasha biliyoyin dalolli da kuma kula da shi ba dare ko rana ga fargaba da matsaloli masu yawan gaske. Amma Allah cikin hikima da kudurarsa  da tsari na dabi'a mai inganci mai sauki amma a gurinsa .Ruwan tekuna da tabkuna ta hanayar iska  da kadawarta  da tafiyar da giza-gizai yana samar mana da ruwan sama daga wani yanki zuwa wani yanki domin raya kasa da shayarwa da kuma ciyar da mutanan da ke zaune a wannan yanki. To ya kamata mu yi tunani da nazari kan wadannan ni'imomi masu yawa  maras karewa da adadi da Allah ya halitta domin sanin karfin ikosa da zatinsa da kuma gode masa a kullum ba gajiyawa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu dauki darasi da ilimin abubuwa hudu kamar haka:

Na farko: Komin kankantar ni'ima a idonmu tana da girma da matsayi a gurin Allah don haka mu gode masa kan kowace irin ni'ima.

Na biyu: aiki da kokari wajen samar da abin da za a sa a bakin salati na halali  kuma addini yana son hakan da karfafa mana guiwa.

Na uku:tsawa da walkiya daga sama  da sabkar ruwan sama da fitar tsirre ba lamari ba ne haka kwacam bat sari  a'a yana tafiya ne cikin tsari daga Allah.

Na hudu:Shi sanin Mahalicci yana bukatar ilimi da tunani da tsinaye da nazari.

To yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 25 a cikin wannan sura ta Rum:

 

وَمِنْ آيَاتِهِ أَن تَقُومَ السَّمَاء وَالأَرْضُ بِأَمْرِهِ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمْ دَعْوَةً مِّنَ الأَرْضِ إِذَا أَنتُمْ تَخْرُجُونَ
 

25- Kuma tsayuwar sammai da kassai da umarninsa yana daga ayoyinsa .Sannan kuma yayin da Ya kira ku kira na tashi sai ga ku kuna fitowa daga cikin kasar.

A cikin ayoyin da suka gabata mun ji bayani kan halittun sammai da kassai to wannan ayar tana bayani ne kan ci gaba da wanzuwarsu da cewa; akwai manyan halittu a cikin sammai da har yanzu mun kasa gano su da killace su ,akwai biliyoyin tauraro da dangoginsu da wasu duniyoyi ba wannan duniyar da muke ciki ba , da tafiyar da rayuwarsu ba tare da wani yayi karo da wani ba ,wannan na nuni da cikekken tsari da karfin iko da hikimar wanda ya Halicce su.Idan da za a samu wani kuskure a tafiyar da rayuwarsu to da wannan matsala ta shafi sauran duniyoyin da ya hada da duniyar da muke ciki.Amma mai duka gwani masani mai hikima yana tafiyar da su baki daya cikin tsari da umarni. Wani abu da ya kamata mu sani a kwai lokaci na zuwa da Allah zai umarce wannan duniya da sauran duniyoyi da su daina aiki wannan rana it ace ranar tashin kiyama  inda za a tayyar da mu a wata duniyar ba wannan duniya ba wato lahira ke nan  domin fuskantar hisabi da sakamako mai kyau na gidan aljanna ko aksasin haka wato shiga wutar jahannama ,Allah ya kare mu duniya da lahira.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Wannan duniya da abubuwan da ke cikina da sauran duniyoyi an halicce su ne cikin hikima da tsari da umarnin Allah.

Na biyu:Allah da ya halicce mu da wannan duniya da abubuwan da ke cikinta Shi ne kuma yake tafiyar da lamarinmu.

Na uku:Sake tayar da mutum bayan mutuwa na nuni da ruhin mutun yana raye ba gangarsa ba a ke zama turba.

******************************MUSIC**************

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 26 a cikin wannan sura ta Rum:

 

وَلَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ كُلٌّ لَّهُ قَانِتُونَ

 

26-Kuma duk abubuwan da suke cikin sammai da kassai nasa ne.Dukanninsu masu biyayya ne gare Shi.

Wannan ayar ci gaban ayar da ta gabace ta ne da ke maida martini kan wasu mutane masu ra'ayi da mamakin rayuwarmu bayan mutuwa za a sake tayar da mu a wata duniyar inda wannan ayar ke cewa: kamar yadda Allah ne halicci mutum da iko kansa da kuma kan sauran halittun baki daya da mala'iku da aljannu.to yana da hakkin zartar da duk wani abu da ya ga dama komin kankantarsa da girmansa a idonmu kuma babu wani mai rai a doran kasa da ke da ikokon saba masa .Saboda babu wani da Allah y aba shi ikon saba masa ko taimaka masa wajen tafiyar da wannan duniya da sauran duniyoyi da halittun da ke cikinsu.Kuma kowa yana zartar da abin da Allah ya so da umurtarsa ne hatta zabin da mutum ke da shi Allah ne y aba mu balantana mala'iku da ba su da wani zabi sai abin da Allah ya umarce su da aikatawa.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Ba wai kawai duwatsu da tsirrai da dabbobi ba hatta sauran halittu kamar mutane,mala'iku da aljannu  bas u da ikon fita daga karkashin mulki da kudurar Allah.

Na biyu:Kamar yadda mutum a tsarin rayuwa ta ci da sha jikinsa ke girma da binkasa haka idan ya bi umarni da tsarin shari'ar Allah zai ci gaba da kai wag a kamala duniya da lahira.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags