Oct 22, 2017 07:52 UTC

Suratur Rum, Aya ta 27-29 (Kashi na 735)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah jama'a masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 27 a cikin wannan sura ta Rum:

 

وَهُوَ الَّذِي يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ وَهُوَ أَهْوَنُ عَلَيْهِ وَلَهُ الْمَثَلُ الأَعْلَى فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
 

27- Shi ne Wanda Yake farar halittu,sannan Ya mayar da su bayan mutuwa.Yin haka kuwa shi ya fi sauki a gare Shi a ganinmu,kuma Yana da sifa madaukakiya a cikin sammai da kassai watau Kalmar shahada,kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima.

A cikin shirye-shiryen da suka gabata a cikin wannan sura ta Rum Ku'ani yayi nuni da wasu ayoyi ne da ke ishara da kudurar Allah cikin halittunsa  da kuma wasu ayoyi da ke bayani kanilimi,kudura da hikima maras karewa na Mahalicci.To wannan ayar ci gaban ayoyin da ke Magana kan ranar tashin kiyama da cewa:Allah da ya halicci wannan duniya tun farko haka shi ne ke da iko da karfin sake tayar da halittun cikinta a ranar tashin kiyama. Mu sani a gurin Allah babu wani aiki wai shi mai wuya ko mai sauki duk daya ne a gurinsa .Mu mutane ne ke ganin wani aiki yana da wuya ko sauki kan waninsa ko sarkakiya. Amma a gurin Allah bah aka lamarin yake ba duk abin da ya gudurta sai y ace masa zama sai ya zama daidai yadda yake so.Idan a gurin mu mutane sake tayar da mutane yafi sauki kan halittarsu tun farko  to a gurin  Allah duk daya ne kuma yana da iko da kudurar zartar d abin da ya so fiye da fada da cikawa.

A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko:Siffofin Allah madaukakin sarki sun zarta tunani da bayanin fatar baki ta mutum kuma babu wani abu da za a iya kwatamtawa da Shi domin ya zarta duk wata halitta a wannan duniya da lahira da har za a bada kwatamce da Shi.

Na biyu :Hikimar Allah ta tabbata  da hukumcin cewa bayan wannan duniya akwai wata rayuwar bayan mutuwa da rayuwa a lahira.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun aya ta 28 a cikin wannan sura ta Rum:

 

ضَرَبَ لَكُم مَّثَلا مِنْ أَنفُسِكُمْ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُم مِّن شُرَكَاء فِي مَا رَزَقْنَاكُمْ فَأَنتُمْ فِيهِ سَوَاء تَخَافُونَهُمْ كَخِيفَتِكُمْ أَنفُسَكُمْ كَذَلِكَ نُفَصِّلُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

 

28- Ya buga muka misali daga kawunanku,shin kuna da wasu abokan tarayya daga bayinku da hannayenku suka mallaka game da abin da Muka arzuta ku da shi,ku da su ku zama daidai kuke game da wannan kuna kuma jin tsoron su kamar yanda kuke tsoron junanku? Kamar haka Muke rarraba ayoyin filla-filla ga mutanen da suke hankalta.

Mushrikai na dangantawa Allah abukkan tarayya daga cikin abubuwan da ya halitta amma kuma suna da karfi da iko da tasiri kamar Allah a lamurran zartar da wannan duniya.To don haka wannan ayar ta rusa wannan wawanci na Mushrikai da bada misali daya tilo kan sake raya mutane a lahira da cewa:Idan mu mutane mun mallaki bayu shin muna bas u yancin sarrafa dukiyarmu ? shin su tamkar mu ne da yin tarayya da mu a cikin wannan dukiya da sarrafa ta kamar mu babu wani bambanci? Ta yaya bayun da muka mallaka ba mu ganinsu daya suke da mu da bas u hakkin yin abin da suka ga dama kamar mu  amma halittun da Allah ya halitta  su zama daya da Shi da Ya halicce su da ba su hakkin zartarwa da yin tarayyar a cikin lamurran da suka kebantu da Allah .Ya kamata mu yi tunanin ta nutsu da sanin ya kamata.

Idan bayun da muka mallaka su tarayya da mu a dukiyarmu to halittun Allah ma suna tarayyar da Shi amma idan hakan  ba za ta yi yu ba  bawa yayi daidai da mai gidansa da hakkin sarrafawa sai da izininsa  to ta yaya za ku amince da halittun su sarrafa kamar Mahalicci Allah ba tare da izininsa ba .To mu sani duk wani lamari da ya kebanci Allah na Allah ne Shi kadai babu wani da ke da ikon zartar da wani abu sai da izininsa.

Daga cikin wannan ayar  za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:mutum adali shi ne babban alkalin kansa.Mu mutane hatta wani mai kama da mu idan yana aiki karkashin mu ba mu daukansa abokin tarayyarmu ta yaya kuma za mu hada haillittun Allah daidai da wanda ya halicce su da yin tarayya da Shi idan muka yi haka ba mu yi masa adalci ba kuma ba mu yi wa kanmu adalci ba.

Na biyu:Ayoyin kur'ani na bayani ne dai dai da hankali da tunanin mu mu mutane da kiran mu zuwa ga yin tunani na hankali.

**********************MUSIC********
To madallah daga karshe a cikin shirin nay au za mu saurari karatun aya ta 29 a cikin wannan sura ta Rum:

 

بَلِ اتَّبَعَ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَهْوَاءهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ فَمَن يَهْدِي مَنْ أَضَلَّ اللَّهُ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ
 

29- Ba haka ba ne, wadanda suka yi zalunci dai sun bi son ransu ne ba tare da wani ilimi ba,to wane ne zai shiryar da wanda Allah ya batar? Kuma bas u da wani maceci.

Wannan ci gaban ayar da ta gabace ta ne da ya bada misali da ya kamata mu yi tunani da nazari kansa kafin mu amince.To wannan ayar na cewa; wadanda ke danganta abokin tarayya ga Allah sun nisanta da duk wani tunani na hankali da hanya madaidaiciya  kuma suna fama da matsalar son rai da bin bukatunsu kawai.Domin abin da suke fada babu dalili na ilimi ko hankali a cikinsa domin suna son samarwa da danganta abokin tarayya ga Allah ta kowa ne hali. Mutane da suka maida ilimi da hankalin da Allah y aba su share guda suna aiki da son rai  ido rufe karshen aikinsu haka zai kasance cikin bat aba su taba samin shiriya ba. Saboda lazimin shiriya ya hada da aiki da hankali da tunani na gari wajen fahimtar hakikanin lamura da mutum ke isa gare su ta hanyar ilimi da fadakarwa.Amma duk wanda bay a son sanin gaskiya sai ya rungumi son rai da zucciya babu tunani da hankali da zama da abukai irinsa da suka yi hannun riga da hankali da tunani da ilimi na hakika.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko:duk wani wani abu na kaucewa hanya madaidaiciya ta tauhidi  wani nau'I ne na zalunci kan karan kansa da kuma koyarwa ta addinin musulunci.Shi wannan zalunci bas hi da bambanci kan karan kanka ko kan waninka haka wannan zaluncin ne ga Allah da kuma manzonsa .

Na biyu: A yau irin shirker da ake yi wa Allah  a sauran addinai kamar a addinin buda da Hindu  da suke bautawa abubuwa iri-iri da gumaka na mutane da dabbobi na nuni da jahilcin mutane a wannan karni na ci gaban ilimi amma kuma kash ba a yi aiki da ilimin ba da kuma hankali  da tunani kan wanda ya Halicci wannan duniya da abin da ke cikinta.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags