Oct 22, 2017 07:59 UTC

Suratur Rum, Aya ta 30-34 (Kashi na 736)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To Madallah za mu fara shirin na mu na yau tare da sauraren karatun aya ta 30 a cikin suratul Rum:

 

فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا فِطْرَةَ اللَّهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا لا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ اللَّهِ ذَلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لا يَعْلَمُونَ
 

30- Sannan kuma ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici, wanda shi ne, dabi'ar da Allah ya halicci mutane a kai, Ba wani canji ga addinin Allah.Wannan shi ne, addini mikakke, sai dai kuma yawaicin mutane ba su san haka ba.

A cikin shirye-shiryen da suka gabata, Kur'ani ya kawo ayoyin da suka yi bayani kan ilimi da kudurar Allah madaukakin sarki a lamarin da ya shafi halittar kassai da sammai da abubuwan da ke cikinsu. To wannan ayar da muka saurara na cewa: Gani da nazari kan abubuwa na dabi'a da tsari da ke tattare da kuma tafiyar da wannan duniya da kuma yin nazari a halittarmu mu mutane zai isar da mu ga Wanda ya Halicce mu. Dalili kuwa halitta mai kyau da tsari na tabbatar da kwarewar wanda yay i wannan halitta da karfinsa da iliminsa da hikimarsa da kuma daukakarsa.

Allah madaukakin sarki a cikin wannan ayar ya bukaci manzon Rahama,manzon musulunci da dukan ma'abuta imani da ba wai kawai ta fatar baka ba da kollon zahirin lamari a'a su nutsu  har zucci da ganin badinin lamarin  kollon na gaskiya da fahimta  ta hankali ta kowace hanya da yanayi da kaucewa son rai  da kuma yin dubi a cikin dukan addinai da Allah ya sabko mana za su fahimci gaskiya da kudurar Allan da ya Halicce mu da tafiyar da lamuranmu  cikin hikima da tsari.Amma kash yawancin mabiya addinai sun kaucewa hanya madaidaiciya da idan mutane suka bi ta za ta kais u ga shiriya da sa'ada duniya da lahira.Wannan ayar na cewa daya dayan addinin da ya tsaya da kafafunsa  kuma yana kan hanya madaidaiciya shi ne addinin musulunci.Addinin da ke tafiya tare da fidirar Allah  tun farkon halittar mutum har zuwa karshen tashin kiyama. Kuma duk da cancanjawar zamani da na rayuwar mutane  da guraren rayuwarsu bay a canja wa yana nan daram .Haka alkawalin da Allah yay i mana na isa ga kamala da sa'ada  matukar muka yi riko da addininsa yana nan ba ya canja wa. Amma yawancin mutane sun sha'afa da fahimtar wannan gaskiya sai bankaura suke yi sun kasa  fahimta da aiki da gaskiya.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Allah ya halicci mutum kuma ya nuna masa hanya madaidaiciya a ciki da wajensa a sarari da sammai da kuma fidirarsa.

Na Abubuwa da suka shafi fidira a fili suke karara sai dai wanda ya shagaltu da sha'afa kuma tushen addini lamari ne da yayi daidai da fidira amma yana bukatuwa da koyarwa ta gaskiya da shiriya da tsayin daka.

Na uku: Lamari da tsari na halittar mutum da kuma tsarin sharia daa Allah suna tafiya tare da juna  domin dukansu biyun daga tushe guda suka fito babu wani sabani a tsakaninsu.

Yanzu lokaci ne da za mu saurari karatun ayoyi na 31 da 32 a cikin wannan sura ta Rum:

 

مُنِيبِينَ إِلَيْهِ وَاتَّقُوهُ وَأَقِيمُوا الصَّلاةَ وَلا تَكُونُوا مِنَ الْمُشْرِكِينَ

 

31- Ku zama masu komawa zuwa gare Shi wato Allah kuma ku ji tsoronsa ku kuma tsai da salla kuma kada ku zamanto cikin mushrikai.

 

مِنَ الَّذِينَ فَرَّقُوا دِينَهُمْ وَكَانُوا شِيَعًا كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ
 

32- Irin wadanda suka rarraba addininsu suka kuma zamanto kungiya-kungiya kowacce kungiya tana mai farin cikinda abin da yake nata.

A cikin ayar da ta gabata mun yi bayani kan cewa duk addini lamari ne na fidira amma yana bukatar kar mutum ya gafala  da mantawa da koyarwar addini  saboda wannan ayar tana cewa; a duk lokacin da mutum ya gafala da kaucewa hanya ta gaskiya  to zai yi hannun riga da hanyar Allah  da kuma tauhidinsa don haka domin kare addinidole a bi umarninsa da dokokinsa kamar haka : na farko:kiyaye  tsaron Allah da hana kai aikata sabo. Na biyu dawwama kan hanyar da za ta danganta mu da Allah kamar yin sallah da ayyukan Alheri da gode masa da yin salati ga Manzonsa da iyalan gidansa . Idan muka bi wadannan lamurra biyu mutum zai kai ga bacci ta fuskar Iitikadi da ayyukan alheri da hana kansa ga aikata shirka da banna.

Ci gaban ayar na cewa tushen sabani da rarrabuwar kawuna a tsakanin mutane shi ne shirka da ayyukan dake da dangantaka da shirka domin da a ce dukan mutane sun rungumi tauhidi  da sun isa ga kamala da sa'ada  duniya da lahira  da hadin kai amma shirka ta haddasa sabani a tsakanin jama'a da kais u ga bata da tabewa duniya da lahira.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Fidira da addini abu guda ne domin tushensu guda ne idan mutum ya hada wadannan abubuwa biyu zai kai ga matsayin daukaka da kasancewa cikin ma'abuta alheri da karbar gaskiya da tsaron Allah da yin sallah da salatin manzon da iyalan gidansa.

Na biyu: Tauhidi yana haddasa hadin kai da fahimtar juna a tsakanin jama'a da zamantakewar mutane. Ita kuwa shirka na haddasa rarrabuwa da sabani a tsakanin mutane da zamantakewarsu.

Na uku: Rarrabuwar kawuna da sabani a tsakanin jama'a alama ce ta nisantar hanayr tauhidi da fadawa tarkon shirka.

**************************MUSIC*********

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 33 da 34 a cikin wannan sura ta Rum:

 

وَإِذَا مَسَّ النَّاسَ ضُرٌّ دَعَوْا رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَا أَذَاقَهُم مِّنْهُ رَحْمَةً إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ
 

33- Idan kuma wani matsi ya sami mutane sai su roki Ubangijinsu suna masu komawa gare shi,sanan kuma idan Ya dandana musu rahama daga gare Shi sai ka ga wata kungiyar daga cikinsu suna tarayya da Ubangijinsu.

 

لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ فَتَمَتَّعُوا فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ

 

34-Don su kafirce wa abin da Muka bas u.T ku ji dadi,kadan da sannu za ku sani.

Wadannan ayoyi ma kamar sauran ayoyin da suka gabace sun a bayani ne kan fidirar mutane ta sanin Mahalicci  inda wadannan ayoyi  suka yi nuni da wani misali na dabi'ar mutane a rayuwarsu da cewa; a duk lokaci da mutum ya fuskanci wata matsala  ko bala'a a rayuwa  da wani mutum ko wasu mutane suka kasa warware masa da taimaka masa har lokacin da guiwarsa ta yi sanyi babu gaba babu baya  sai ya mika wuya da rungumar Allah mai duka  da bukatar ya warware masa wannan matsala. A cikin wannan yanani ne mutum yake tunawa da wanda ya gafala da Shi . A wannan lokaci zai fahimci ya shafa'a da gafala da wanda bai kamata ya gafala da Shi ba  a lokaci guda ya bukaci Allah da ya taimaka masa . Amma a duk lokacin da lutifin Allah ya shafe shi  Allah ya warware masa wannan matsala da rahamarsa sai ya sake komawa halinsa na da na mantawa da gafala da Allah wanda ya halicce shi har yay a bijirewa umarninsa.Idan mutum ya ci gaba da wannan hali da dawwama kan wannan mummunan hali na kafircewa ni'imomin Allah  a wannan duniya to ba zai ga makoma mai kyau bat un a wannan duniya.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka;

Na farko:wasu gungu daga cikin mutane bas u tunawa da Allan da ya Halicce su zai sun shiga cikin matsala da tsanani a rayuwa kai k ace Allah kawai amfaninsa warware matsaloli ne idan bas u da wata matsala bas u tunawa da Allah.

Na biyu:Tsanani da matsaloli na tilastawa mutum mantawa da gafala sai yayi riko da fidirarsa ta neman mahalicce sa Allah madaukakin sarki.

Na uku: Rayuwa cikin wadata na sawa mutum ya manta da mahaliccinsa da gafala a rayuwa  ko neman taimakon Allah  dahakan ke kais hi ga ruhin kafirci na mantawa da ni'imomin da Allah yayi masa balantana ya gode masa.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags