Oct 22, 2017 08:15 UTC

Suratur Rum, Aya ta 39-42 (Kashi na 738)

Bismillahi rahamani Rahim, Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu, da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah jama'a masu saurare a yau za mu fara shirin da sauraren aya ta 39 a cikin  suratul Rum kamar haka:

 

وَمَا آتَيْتُم مِّن رِّبًا لِّيَرْبُوَ فِي أَمْوَالِ النَّاسِ فَلا يَرْبُو عِندَ اللَّهِ وَمَا آتَيْتُم مِّن زَكَاةٍ تُرِيدُونَ وَجْهَ اللَّهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْمُضْعِفُونَ
 

39-Kuma abin da kuka bayar na riba don ya karu a cikin dukiyoyin Allah. Abin kuwa da kuka bayar na zakka kuna masu neman yardarm Allah,to wadannan su ne masu ninninkuwar lada.

A cikin shirin da ya gabata mun kawo ayar da ke bayani kan ciyarwa da taimakawa mabukata amma tana bayani da kwatamta ciyarwa saboda neman yardarm Allah da kuma ciyarwar da aka yi babu ikhlasi a ciki da cewa: duk wani abin da z aka bawa wani bawan Allah idan don neman yardarm Allah ba neman birge wani Allah ba to mutum zai ga sakamakon wannan aiki nasa tabbas a gurin Allah linkin ba linkin amma idan kuma wannan kyata an yi ta ne ba don Allah ba  sai don neman birgewa da yabon mutane  ko kuma neman kara samin ribaya da yawan arziki to babu wani lada da za a samu domin tushen abin ba don Allah ne ba to me ya sa za a nemi ladan wannan aiki a gurin Allah wanda ba a yi ba don shi.

Kamar wanda zai bawa wani bas hi ne amma idan zai maido zai kara masa wata riba ko yay i don a yaba masa to bas hi da wani lada a gurin Allah domin burin aiki sa babu Allah ko neman yardarsa a ciki.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: abin mai muhimmanci a bada bashi niya da mai kyau ta neman yardar Allah ba yawan abin da za a bada ko samu ba.

Na biyu:daraja da ribar duk wani aiki niyar neman yardarm allah  idan kuwa babu wannan a cikinsa to bas hi da wata daraja.

Na uku:Duniya kasuwa ce  da kowa yake saye da sayarwa da neman riba  wasu suna ciki da sayarwa tare da Allah da samin ribarsu a wajensa a wannan duniya da kuma lahira .wasu kuwa na yin asara ne duniya da lahira.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 40 a cikin wannan sura ta Rum:

 

اللَّهُ الَّذِي خَلَقَكُمْ ثُمَّ رَزَقَكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ هَلْ مِن شُرَكَائِكُم مَّن يَفْعَلُ مِن ذَلِكُم مِّن شَيْءٍ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ
 

40- Allah Shi ne Wanda Ya halicce ku sannan Ya arzuta ku sannan Shi zai kasha ku sannan Ya raya ku.shin a cikin abokin tarayyarku akwai wanda zai iya aikata wani abu daga wadannan ? Tsarki ya tabbata a gare Shi,Ya kuma daukaka daga abin da suke Tarawa da Shi.

Wannan ayar na nuni da matsayi maras karewa na Allah a duk wani lamari da ya shafi halitta da cewa;Halittarmu  da razikin da wadatarmu da rayuwarmu da mutuwarmu da sake tayar da mu a wata rayuwar a ranar gobe kiyama duk suna hannun allah ne Shi kadai ba tare da wani abokin tarayya ba. Me yasa muke danganta wasu abubuwa ko wasu mutane a matsayin masu tarayya da Allah ne? Shi ta yaya za su yi yin wani abu dangane da lamari na rayuwa ? Idan masu shirka suka yi irin wannan tunani da dogaro a ranar lahira za su yi nadama domin kuwa abubuwan da suke bautawa babu wani abu da amfani da za su yi masu kuma a lokacin za su sani babu wata rawa da za su taka ko suka taka a lamarin rayuwarsu ko mutuwa da arziki da wadatarsu domin su kansu mabukata ne balantana su taimakawa waninsu.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:abin ya wuce da mai zuwa da arziki da wadata da rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah ne don haka mu kasance bayunsa ban a waninsa ba da hada shi da waninsa da bauta.

Na biyu;Dalili da dokokin lafiyar da wannan duniya da abubuwan da ke cikinta duk Allah ne ya samar  ba wai suna tarayya da shi ba ne kuma babu wani iko  face na Allah kuma komin girma da kankantar halitta Shi ne ya halicce ta.

*********************music********

To madallah masu saurare za mu saurari karatun ayoyi na 41 da 42 a cikin Rum:

 

ظَهَرَ الْفَسَادُ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِي النَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعْضَ الَّذِي عَمِلُوا لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
 

41- Barna ta bayyana a kan tudu da kuma cikin ruwa saboda abubuwan da hannayen mutane suka aikata don a dandana musu shashin abin da suka aikata ,ko watakila sa dawowa gaskiya.

 

قُلْ سِيرُوا فِي الأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن قَبْلُ كَانَ أَكْثَرُهُم مُّشْرِكِينَ

 

42- Kace da su: ku yi tafiya mana a bayan kasa sannan ku duba ku ga yadda karshen wadanda suke gabaninku ya zama,Yawaicinsu sun kasance mushrikai.

A yoyin da suka gabata suna bayani ne kan akidu masar kyau na mushrikai to amma wadannan ayoyin da muka saurara na bayanin cewa; dangantaka kai tsaye ayyuka da niyar mutane da ayyukan fasadi da banna a tsakanin mutane su ne tushe matsalolin da muke fuskanta a rayuwa da kuma uwa uba kafirci da yin shirka ga Allah. Da kuma mantawa da wanda ya halicce mu wanda kuma rayuwarmu da arzikinmu yake hannunsa.Duk wanda ba ya bin dokokin Allah zai fada tarkon sako da banna a tsakanin jama'a da kaucewa hanya madaidaiciya duniya da lahira kuma munanan ayyukan da muka aikata su za su zame mana karfen kafa a gobe kiyama.

Kan wannan dalili ne ma Kur'ani ke gayyatar musulmi da su yi nazari  da dubi a cikin rayuwar sauran al'ummomin da suka gabace mu  da yadda suka rayu da kuma yadda rayuwar ta kasance da karshenta hatta wasu da ke rayuwa a yau irin tasu ta banna da fasadi a tsakanin jama'a ya dace su sani da idon basira cewa Allah tun a wannan duniya ke nuna wa wasunmu sakamakon mummunan aikin da suka aikata. A rayuwar yau babu abin da ya fito  a fili karara kamar zalunci da danniya da banna a tsakanin jama'a da kuma a tsakanin kasashe mai karfi shi ke danniya mai rauni da zaluntarsa babu tausayi  da sanin ya kamata. Kamar yadda kur'ani ya shaida mana trushen duk wani sabo  da fasadi shi ne shirka kuma shi ke kai mutum ga hallaka.Shi kuwa Tauhidi shi ke kai mutum ga sa'ada da kwaciyar hankali ta hakika.

Daga cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:ayyukan maras kyau na mutane na tasiri a cikin tsarin zamantakewa da bata muhalli da tsarin rayuwa.

Na biyu:Muhalli da sarari da teku duk amana ne na Allah a gare mu mu mutane kuma Allah bai ba mu dama da yanci yin duk abin da muka ga dama da sub a dole mu kiyaye.

Na uku:mu fita mu kewaya da yin bulaguro da ziyarce-ziyarce domin daukan darasi a rayuwa wannan wani galgadi da fadakarwa ce daga addinin musulunci.

Na hudu:Idan yawancin mutane da ke rayuwa cikin wata al'umma suka kasance masu yawan sabo da fasadi da kaucewa hanya ta gaskiya za su fuskanci fushin Allah .idan ka tsunci kanka a wannan guri sai ka yi hijira da tsiratar da ranka.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags