Oct 22, 2017 08:29 UTC

Suratur Rum, Aya ta 43-46 (Kashi na 739)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau tare da sauraren karatun aya ta 43 a cikin wannan sura ta Rum:

 

فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ الْقَيِّمِ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ يَوْمٌ لّا مَرَدَّ لَهُ مِنَ اللَّهِ يَوْمَئِذٍ يَصَّدَّعُونَ

 

43- Sannan ka tsai da fuskarka ga Addini madaidaici tun kafin ranar nan da ba ta da makawa ta zo daga Allah ,a wannan ranar ne mutane za su rarrabu kowa ya kama gabansa.

Daya daga cikin abubuwan da addinin musulunci ya kebantu da  shi yadda yayi daidai da hankali da fidirar mutum  da kuma ba su sabawa suna tafiya kafada da kafada kan wannan dalili ne ma a cikin wannan ayar, musulunci addini ne da ya zarta duk wani addini ta fuskoki daban daban da dokoki managarta da ya hade duk wata maslaha da tsarin rayuwa mai inganci a daidaiku da zamantakewar jama'a. kuma tasiri da albarkar addini ta shafi dukan musulmi  ba tare da barin wani bangare ko shashe na rayuwar matukar muka yi aiki da shi . Shi addinin musulunci ba addini ba ne da mutum zai yi aiki da wani bangare ya bar wani bangare nasa  don haka mu yi aiki da dukan umarnin addini da amfanuwa da wannan damar da aka ba mu matukar mun tabbatar da cewa rayuwar wannan duniya gajera ce  sai mu yi kokarin amfanuwa da isa ga sa'ada ta karshe.

A ranar tashin kiya mutane za su kasance gungu-gungu bangaren mumunai ya banbanta da gurin kafirai da wadanda suka kaucewa hanya madaidaiciya kowa yana gurin da aka yi masa tanadi.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:dole mu bi addini da koyarwa ta addini da gaskiya ba aiki da wasu daga cikin dokokin addini ba a bar wasu ba.

Na biyu: bin koyarwar Addini na kai mu ga tsira da kubutar da mu daga fuskantar gurbacewar al'adu da zamantakewa.

Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 44 da 45 a cikin wannan sura ta Rum:

44-Wanda ya kafirta to zunubin kafircinsa yana kansa,wadanda kuwa suka yi aiki kyakkyawa,to kansu suke shimfida wa alhairi.

45- Don Allah Ya saka wa wadanda suka ba da gaskiya suka yi ayyuka nagari daga falalarsa. Hakika Shi Allah ba Ya son kafirai.

A cikin ayoyin da suka gabata kun ji cewa: a ranar kiyama za a kasa mutane kasha kasha ko in ce gungu-gungu.Sahun mumunai ya sha bamabn da da sahun kafirai to wadannan ayoyin da muka saurara na cewa;ita azaba da sakamako a ranar tashin kiya suna zuwa ne gwalgwadon aikin da mutum ya aikata a wannan duniya.kafirci ya azabtar da mutum da takura masa ne a wutar jahannama, yayin da shi kuwa imani  da aikin alheri na sanyayawa mutum ria da kwantar masa da hankali a cikin aljanna.. Wani abin lura  su kafirai ana azabtar da su ne daidai da mummunan ayyukan da suka aikata amma Su Muminai

bayan an saka masu da sakamakon ayyukan alheri da suka aikata  da kekkyawar niya  haka kuma za a kara masu da lutifin Allah da rahamarsa ta musamman da kuma falalar Allah. Amma shi kafiri an haramta masa wannan kuma ya kasa samin hakan a gurin shugabanninsa da kuma yake yiwa shirka.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Imani da kafircin mutane bay a cutar da Allah ko kara shi da komi sai dai cutarwa ko alheri na komawa a gare mu ne.

Na biyu: Duk azabar da kafirai za su fuskanta da fushin Allah karkashin adalcinsa ne su kuwa ma'abuta imani da ayyukan alheri karkashin falalarsa ne.

***************MUSIC*********************

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 46 a cikin wannan sura ta Rum:

46- Yana kuma daga ayoyinsa cewa yana aiko iska tana mai yin albishir da ruwa kuma don ya dandana muku rahamarsa,don kuma jiragen ruwa su rika gudana da umarninsa,kuma don ku nema daga falalarsa kuma don ko kwa gode.

Wannan ayar ta sake tabo bayanin Tauhidi da aka yi a farkon wannan sura  kan tsarin tafiyar da lamarin wannan duniya da rayuwa a cikinta  da cewa;idan  muka lura da sammai da kassai da sauran halittun Allah a wannan duniya kamar iska da ke kadawa  da sabkar ruwan sama za mu fahimci girma da karfi da kudurar Allah da kuma hikimarsa da fahimtar Shi kadai ne Mahalicci ba tare da abokin tarayya ba. Cikin tsari mai sauki a gurinsa yake tafiyar ahirin rayuwa  da sake tayar da abubuwa

kamar tsirre,dabbobi da tsintsaye da mu mutane da duk wani abu da yake so da muke bukatuwa da shi.Har mu samu damar yin noma da kiwo da samin abin da za mu ci mu sha mu yi sitira ta hanyar sabkar ruwan sama da kadawar iska hatta abubuwan da za mu yi jigilar abubuwan da muka noma ya samar mana su  cikin sauki a fadin duniya tun farkon wannan duniya da zuwa karshenta.

Amma kash yawancin mutane  bas u lura da wannan babbar ni'ima daga Allah madaukakin sarki da ya sanya a hannunmu balantana su yi tunanin gode masa .

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka;

Na farko:kadawar  iska ya samya tafiyar gajimare daga wannan yanki zuwa wancan  da samar da ruwan sama a gurin da kasa ta bushe a sake raya ta  da samar da fitar tsirre.

Na biyu:Hatta tafiya da zirga-zirgar jirgin ruwa a teku yana hannun Allah ne ba matukin jirgin ba saboda Allah ne ya samar da dokoki da tsarin tafiyar da dabi'a da yanayin da jirgin ruwa zai iya tafiya a kan ruwa da yin jigilar kaya da mutane na tsawon lokaci mai tsawo a kan teku ba tare da wata fargaba ko matsala da ikon Allah.

Na uku:kokari da tashi fadin neman halal addini musulunci a cikin kur'ani yay i umarni da hakan kuma duk abin da mutum ya samu ta hanayr halal ya godewa Allah da ya wadatar da shi da sanin ba karfi da dubararsa ba ne.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags