Oct 22, 2017 08:44 UTC

Suratur Rum, Aya ta 50-54 (Kashi na 741)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

 

*******************MUSIC****************

فَانظُرْ إِلَى آثَارِ رَحْمَتِ اللَّهِ كَيْفَ يُحْيِي الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا إِنَّ ذَلِكَ لَمُحْيِي الْمَوْتَى وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
 

50- Sannan ka yi duba zuwa ga guraban rahamar Allah yadda yake raya kasa bayan kekashewarta.Hakika wannan lallai Mai raya matattu ne,kuma Mai iko ne a kan komai.

 

وَلَئِنْ أَرْسَلْنَا رِيحًا فَرَأَوْهُ مُصْفَرًّا لَّظَلُّوا مِن بَعْدِهِ يَكْفُرُونَ
 

51- Wallahi in da za mu aiko da iska su gan ta fatsi-fatsi ba ta da ni'ima da sai su zarce suna kafircewa bayan zuwanta.

 

فَإِنَّكَ لا تُسْمِعُ الْمَوْتَى وَلا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاء إِذَا وَلَّوْا مُدْبِرِينَ

 

52- Sannan hakika kai b aka iya jiyar da matattu,kuma b aka iya jiyar da kurame kira lokacin da suka juya suna masu ba da baya.

 

وَمَا أَنتَ بِهَادِي الْعُمْيِ عَن ضَلالَتِهِمْ إِن تُسْمِعُ إِلاَّ مَن يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا فَهُم مُّسْلِمُونَ

 

53- Kuma kai ba mai iya shiryar da makafi watau batattu ba ne daga batansu,ba wadanda kake iya jiyarwa sai masu ba da gaskiya da ayoyinmu,suna Musulmi.

 

اللَّهُ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن ضَعْفٍ ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ ضَعْفٍ قُوَّةً ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ قُوَّةٍ ضَعْفًا وَشَيْبَةً يَخْلُقُ مَا يَشَاء وَهُوَ الْعَلِيمُ الْقَدِيرُ
 

54- Allah Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rauni,sannan kuma Ya sanya karfi bayan raunin,sannan kuma Ya sanya rauni da furfura bayan karfin,Yana halittar abin da Ya so .Shi ne kuwa masani Mai iko.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags