Oct 22, 2017 08:54 UTC

Suratur Rum, Aya ta 55-60 (Kashi na 742)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

 

وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يُقْسِمُ الْمُجْرِمُونَ مَا لَبِثُوا غَيْرَ سَاعَةٍ كَذَلِكَ كَانُوا يُؤْفَكُونَ

 

55- Kuma a ranar da alkiyama za ta tashi kafirai za su rantse kan bas u zauna ba a kaburburansu fiye da sa'a daya. Kamar haka suka kasance ana karkatar da su daga gaskiya.

 

وَقَالَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ وَالإِيمَانَ لَقَدْ لَبِثْتُمْ فِي كِتَابِ اللَّهِ إِلَى يَوْمِ الْبَعْثِ فَهَذَا يَوْمُ الْبَعْثِ وَلَكِنَّكُمْ كُنتُمْ لا تَعْلَمُونَ
 

56- Wadanda kuwa aka bai wa sani da imani sai suka ce : Hakika kun zauna ne a Littafin Allah har zuwa ranar tashi,sannan kuma wannan ce ranar tashin. Sai dai kuma ku kun kasance ba ku sani ba.

 

فَيَوْمَئِذٍ لّا يَنفَعُ الَّذِينَ ظَلَمُوا مَعْذِرَتُهُمْ وَلا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ
 

 

57- Sannan a wannan ranar wadanda suka yi kafirci hanzarinsu ba zai amfane sub a ,kuma ba za a nemi su kawo wani hanzari ba.

 

وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِي هَذَا الْقُرْآنِ مِن كُلِّ مَثَلٍ وَلَئِن جِئْتَهُم بِآيَةٍ لَيَقُولَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ أَنتُمْ إِلاَّ مُبْطِلُونَ
 

58- Kuma hakika Mun buga kowane irin misali ga mutane a cikin wannan Alkur'anin . Wallahi idan da wadanda suka kafirce sun ce: ai ku ba komai ba ne face masu barna.

 

كَذَلِكَ يَطْبَعُ اللَّهُ عَلَى قُلُوبِ الَّذِينَ لا يَعْلَمُونَ

 

59- Kamar haka Allah Yake sa yumki ga zukatan wadanda ba su sanin gaskiya.

 

فَاصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَلا يَسْتَخِفَّنَّكَ الَّذِينَ لا يُوقِنُونَ

 

60- Sai ka yi hakuri, hakika alkawarin Allah gaskiya ne, kada kuma wadanda ba sa gasgatawa su girgiza ka.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags