Oct 22, 2017 15:47 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 1-6 (Kashi na 743)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 7 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

وَإِذَا تُتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا وَلَّى مُسْتَكْبِرًا كَأَن لَّمْ يَسْمَعْهَا كَأَنَّ فِي أُذُنَيْهِ وَقْرًا فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
 

 

7-Idan kuma na karanta masa ayoyinmu  sai ya juya yana mai girman kai kamar bai ji su ba, kamar a ce akwai wani nauyi a cikin kunnuwansa. To kayi masa albishir da azaba mai radadi.

A karshen Ayar shirin da ya gabata an bayyana cewa wasu daga cikin mutane na watsa labaran karya maras fa'ida suna sanya mutane nashadi, domin hana su neman gaskiya, da kuma karbarta, wannan aya na cewa irin wadannan mutane ba a shirye suke su surari ayoyin Alkur'ani ba, ba rantana ba suyi tunanin ya dace su yi Imani, ko da yake tushen wannan lamari shi ne kin gaskiya da kuma girman kai, domin suna ganin kansu a matsayin wadanda suka fi ma'aiki da muminai daraja, kuma ba a shirye suke suka saurari abinda suke fad aba.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Girman kai na hana mutum karbar gaskiya, kuma yana jefa mutum cikin bata.

2-Sauraren magagganun bata da maras fa'ida, yana kawar da shirin mutum na saurare maganar gaskiya da kuma karbarta.

Yanzu kuma loakcin yayi da za mu saurari karantu ayoyi na 8 da ta 9 cikin wannan sura ta Lukman

 

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتُ النَّعِيمِ

 

8-Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi ayyuka nigari suna da (sakamako) aljannonin ni'ima.

 

خَالِدِينَ فِيهَا وَعْدَ اللَّهِ حَقًّا وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ

 

9-suna madawwama a cikinsu,alkawarin Allah kuma gaskiya ne,kuma shi mabuwayi ne Mai hikima.

A baya mun bayyana cewa wasu a maimakon fadar gaskiya, suna bin bayan karya da bata, irin wadannan mutane suna watsa kafirci ne, kuma a karshe su fada cikin azabar ubangiji. Amma a bangare guda akwai wasu da suka yi Imani da Allah da kuma ranar Alkiyama kuma suna aikata ayyuka na gari, wadannan mutane za su samu lada mai girma na ubangiji, wadanda suke karantun Alkur'ani cikin nutsuwa kuma suna sauraran shi, sun kasance masu tunani game da ayoyin ubangiji da kuma abinda suka fahimta daga cikin su sannan kuma suna Imani da shi, wadannan mutane a maimakon girman kai a gaban Ubangijin halittu, suna meka wuya ga Ubangiji kuma sun sauraren umarininsa sunma kuma Kankan da kai tare da bayinsa a gare shi.Allah madaukakin sarki ya yi alkawarin aljanarsa madawwamiya ga irin wadannan bayi, kuma babu shakka wannan alkwari zai cika, domin shi Allah mabuwayi ne mai hikima. Ba kasashe ba ne ba wajen cika alkawari, kuma bay a bayar da alkawarin a kan abinda bai dace ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe uku kamar haka:

1-Imani shi kadai, ko ayyukan alheri su kadai, ba za su yi sanadiyar sanya mutum ya samu aljanna ba,Imani da aikata ayyuka na alheri a tare suke bayar da sakamako mai kyau, kuma su kai mutum zuwa ga farin ciki na har abada.

2-Aljanna gida ne na ni'imomin Allah mababbanta, domin haka, gajiya, fargaba ko tsaro ba shi da wata ma'ana a cikin ta.

3-mu yarda da alkawari gami da kyautar ubangiji, kuma kadda mu kwatamta shi da alkawarin mutane, saboda mai yiyuwa mutum yayi maka alkwarin karya ko kuma ya kasa cika sa saboda shi ajizi ne.

Yanzu kuma loakcin yayi da za mu saurari karantu ayoyi na 10 da ta 11 cikin wannan sura ta Lukman.

 

خَلَقَ السَّمَاوَاتِ بِغَيْرِ عَمَدٍ تَرَوْنَهَا وَأَلْقَى فِي الأَرْضِ رَوَاسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَابَّةٍ وَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاء مَاء فَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ
 

 

10-Ya halicci sammai ba tare da wani jijjige da kuke ganin sa ba, ya kuma kafa manya-manyan duwatsu a cikin kasa don kada ta tangada da ku, ya kuma barbaza kowace irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama sannan Muka tsirar da kowane irin dangin tsiro mai kawatarwa.

 

هَذَا خَلْقُ اللَّهِ فَأَرُونِي مَاذَا خَلَقَ الَّذِينَ مِن دُونِهِ بَلِ الظَّالِمُونَ فِي ضَلالٍ مُّبِينٍ

 

11-Wannan (ita ce) hallitar Allah, sai ku nuna min abin da wadanda suke ba shi, ba suka halitta. A'a su dai kafirai suna cikin bata ne mabayyani.

Wadannan ayoyi sun bayyana misalai biyar na isharar kudirar ubangiji a halitta, na farko daidaituwar tsarin sammai da tauraru ba tare da wani kimshiki da ake gani ba, na biyu halittar Duwatsu masu girma da suka yi sanadiyar nutsiuwar kasa, na uku halittar dabbobi nau'I daban daban a cikin kasa, sama da ruwa, na hudu, saukar da ruwa daga sama, na biyar fitar da tsirai kala daban daban daga cikin kasa, ko wane daga cikin wadannan ababe biyar yana ishara game da kudirar Allah maras iyaka a wajen halitta, da babu wani mutun ko wani abu da ya taimaka masa a wadannan ayyuka.

Wadannan ayoyi sun yi ishara da kimshikan da ba a iya ganinsu ba, da sune suka yi sanadiyar tabbatuwar ababen dake cikin sama kamar su tauraru da sauransu da kuma kiyaye daidaiton dake tsakanin su, har ila yau cikin wadannan ayoyi an yi ishara dangane da Duwatsu ke takawa wajen hana kasa girgiza da kuma nutsuwarta, dukkanin wadannan ababe misalai ne na mu'ijizar ilimi na alkur'ani mai girma, abin ban sha'awa a nan shi ne an bayyana wadannan ababe ne a zamani da mutum bas hi da masaniya ko kadan daga wannan maudu'i.

Duk da irin wadannan mabayanan alamomin Ubangiji a halitta, abin bakin ciki, wasu daga cikin mutane cikin rashin sani da kuma rashin samun shiriya ta gaskiya, suna daukan wasu mutane ko wani abu a matsayin ubangiji, a tunanin su wadannan ababe su nada tasiri a raywarsu, suna cewa Allah madaukakin sarki ya bawa wadannan mutane ko wadannan ababe da suke bautawa wani bangare na tsarin rayuwa, kuma su ne suke taimaka masa a wani bangare na milkinsa.

Domin haka, ci gaban ayar ke cewa: wadanda kuke ganinsu akokanin tarayyar Allah, ku gwada mini me nene suka halitta? Ko kuma a halittar dabi'a me nene suka yi tarayya da Allah? Shi wai su nada karfin kera kuda ko sauro? a maimakon abinda ke cikin sammai ko tsirai.

Karshen wadannan ayoyi, wani nau'in tunani ne na yarda da zalintar kai, kuma mutum ya san cewa babu wani abu da zai iya halitta, duk abinda ke ciokin Duniya halittar ubangiji ne, a bar bautar wanin Allah.

Daga cikin wadannan ayoyi za miu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:

1-samuwar bilyoyin tauraru a cikin sama, ishara ce ta kudirar mahalicci, kuma dalili ne na mu'ijizar alkur'ani.

2-Ruwa, Kasa, Tsirai da dabi'a su nada kima a wajen Allah, mutum ya kamata ya kimanta mahalli saboda babbar amanar ubangiji ne, ya kuma kiyaye su ta hanya mafi kyau.

3-Daya daga cikin hanyoyin sanin Allah, kwatamta iko da kudurarsa da na waninsa.

4-wadanda suke bautar wanin Allah, sun shiga cikin zalinci, zalincin da zai kaisu ga bata.

*****************Musuc********************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

 

 

 

 

 

Tags