Oct 22, 2017 16:09 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 12-13 (Kashi na 745)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 12 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

وَلَقَدْ آتَيْنَا لُقْمَانَ الْحِكْمَةَ أَنِ اشْكُرْ لِلَّهِ وَمَن يَشْكُرْ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ
 

12-Hakika kuma Mun bai wa Lukmana hikima cewa:"ka yi godiya ga Allah. Kuma duk wanda yake godewa to yana godewa ne dan kansa, wanda kuwa ya kafirta to hakika Allah Mawadaci ne abin yabo (a sama da kasa).

Wannan aya da kuma wasu ayoyi da za su biyo bayanta suna magana a kan Lukmanu da kuma nasihohin da yayiwa dansa, bisa dalilai na Alkur'ani da hadisai, Lukumanu ba annabi ba ne, amma mutuman kirki ne wanda ya san yakamata, sai Allah madaukakin sarki ya sanar da shi hikima, hikima basira ce dake karkashin sanin ubangiji, tasirin sa kuma na bayyana ne a magana da mu'amalar mutum, kama daga kiyaye harshe, kula da ciki gami da sha'awa, rikin amana,tawadu'u ko Kankan da kai,nisanta daga aikata ayyuka marasa amfani  da makamantansu na daga cikin ababen dake b ayyana hikimar mutum, ko da yake hikima ba ta takaita ga Lukumanu kawai ba, bisa dalilai na hadisai ko wani mumini da ya gaskanta bakinsa da mu'amala cikin ikhlasi,Allah madaukakin sarki zai bashi wannan babbar ni'ima.

Duk da cewa nasihohin Lukuman, abu ne da Allah madaukakin sarki ke iya bayyana  su kai tsaye a cikin alkur'ani, to amma Allah ya bayyana wadannan nasihohi ne daga bakin Lukumanu zuwa ga dansa, domin yin hakan ya bayyana mana hikimar Lukumanu, kuma ya bayyana mana aikin da ya rataya a kan masu hikima shi ne wa'azi da shiryarwa.

Nasihihin Lukumanu zuwa ga dansa ta takaita ne zuwa ga umarni biyu, na farko yanayin magana da mu'amala a tsakanin iyalai da al'umma, na biyu bayyana ma'anar hikima da kuma hakimi na gaskiya wanda yake da wadannan siffofi guda biyu tare da kira ga al'umma da su dabi'antu da wadannan dabi'u.

A bayyane yake cimma irin matsayi tare da samun wannan babbar ni'ima na bukatar godiya ga Allah madaukakin sarki, godiya ta hakika tana nufin sanya go wata ni'ima a wurinta da kuma ribarta ke komawa wajen shi kansa mutum, wanda kuma hakan ke sanadin girma da daukakarsa, kamar yadda yake amfani da ni'imar Allah a wurin da bai dace ba kafirci ne, kai har ma idan mutum bai yi godewa Allah da bakin sa, domin godiyar baki tare da kafirci a aikace bas hi da wata riba, sai ma hakan na yin sanadin cutuwa, kuma cutuwar na komawa zuwa gas hi kansa Mutum ba wai Allah ba.

Daga wannan Aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-ko wani irin mutum,idan ya tsarkake kansa, ya kuma gyara bakinsa, tausayi da rahamar Ubangiji na iya shafarsa kuma ya cimma wannan matsayi na hikima, ko da kuwa bas hi da zirfin ilimi.

2-riba da hasara ayyukan mutum na komawa ne gare shi, har ila yau godiyar ni'imar ubangiji ko kafirce mata, tasirinsa na komawa ne ga Mutum, ba Allah ba.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karantun aya ta 13 cikin wannan sura ta Lukumanu.

 

وَإِذْ قَالَ لُقْمَانُ لِابْنِهِ وَهُوَ يَعِظُهُ يَا بُنَيَّ لا تُشْرِكْ بِاللَّهِ إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ

 

13- Kuma (ka tuna) lokacin da Lukumanu ya ce da dansa a yayin da yake yi masa wa'azi: "Ya kai dana, kada kayi shirka da Allah, hakika ita shirka zalinci ne mai girma.

Farkon nasiha da wa'azin Lukumanu zuwa ga dansa shi ne ya nisanci aikata shirka, ko shirka a akida ko kuma aikace. Bautar gumki, ko rana, ko wata da tauraru kai har  da dabbobi,a tsahon tarihi ya wanzu a tsakanin al'umma, da dama daga cikin mutane, a cikin jahilci da rashin sani suna tunanin cewa wadannan ababe da ba su da rai ko kuma wasu masu ran ma su nada tasiri a makomar rayuwarsu, domin haka suke ganin su a matsayin abin bauta suke kuma bauta musu.

Da dama daga cikin muminai sun yi Imani da Allah daya, to saidai a aikace mushrikai ne ne saboda suna yiwa wanin Allah sujada, saboda sun kasance suna bautawa kudi da iko, kuma domin su cimma fatnasu , a shirye suke su aikata ko wani irin sabo.

Lukumanu Hakimi ya san lahani da cutuwar shirka ko bautar wanin Allah, shi ya sanya ya fara wa'azinsa da gyaran dabi'u, ya bukaci dansa ya nisanta da duk wani nau'I na shirka, domin yana ganin sa a matsayin zunubi mai girma.

Abin ban sha'awa a nan shi ne a fakaice wannan aya na bayyani ne dangane da nauyin da ya rataya kan ma'aifa na koyar da 'ya'yansu kyakkyawar akida kuma su yi musu bayyani, ko da yake hanyar yin bayyanin ma na da mahimancin gaske, hanyar nasiha da wa'azi nada tasiri soasai a maimakon amfani da lafazin umarni da karfi, yanada kyau, ayi amfani da hanyar da za ta samu karbuwa daga wajen 'ya'ya, kamar amfani da lafazi na tausayi kamar su dana da sauransu.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-ko wani mutum yana bukatar nasiha da wa'azi, bisa dalilai na ayoyi da hadisai, wani lokaci Imam Ali (a.s) yana fadawa sahabansa cewa su yi masa nasiha da wa'azi domin a cikin akwai tasirin da babu shi a cikin sani.

2-Mu koyi hanoyin bayar da tarbiya ga kananen yara daga wajen manya da masu hikima, domin a wannan muna iya fadawa cikin kuskure.

3-Mu kiyaye gafala daga 'ya'yanmu, saboda yaro yana bukatar wa'azi da nasihar iyayensa, daya daga cikin mahiman hanyoyin bayar da tarbiya ga yara, shi ne ka ba shi matsayi, kuma ka yi mu'amala da shi cikin tausayi da soyayya.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

 

 

 

Tags