Oct 22, 2017 16:14 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 14-16 (Kashi na 746)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 14 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

وَوَصَّيْنَا الإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَى وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ
 

14-kuma Mun yi wa mutum wasiyya game da iyayensa: ma'aifiyarsa ta dauki cikinsa rauni a kan rauni, yayeshi kuwa a cikin shekaru biyu ne, saboda haka ka gode min da kuma iyayenka, makoma gare Ni take.

A cikin shirin da ya gabata, Lukumanu ya fara yi wa dansa wa'azi, wannan aya kuma da wacce ke gabanta wato aya ta 14 da ta 15, kamar yadda ake fada a yarar larabci Jumula mu'utarida, ma'ana wata magana magana ta shigo a tsakanin wani bayyani, yayin da Lukumanu ya fara yiwa dansa wa'azi da nasiha irin na iyaye  a kan ya nisanci shirka, sai wadannan ayoyi guda biyu suka shiga, inda Allah madaukakin sarki ya bayyana wa 'ya'ya kimar iyaye, sannan kuma ya bayyana rawar da suke takawa a wajen bayar da tarbiya.

Wannan Aya na cewa ma'aifi da ma'aifiya dukkanin su wasicin ubangiji ne, domin ta hanyarsu ne aka halicci 'ya'ya, kuma dukkaninsu sune suka sanya maniyyi aka samu yaro, ko da yake bayan sanya maniyyi, ma'aifiya ta dauki nauyin cikin har na tsahon watanni tara,kuma ta shayar da yaro har tsahon shekaru biyu, inda ma'aifiya take shayar da jariri abincin da yake ci daga jikinta tare kuma da soyayyar ma'aifiya ne jariri yake girma, domin haka a cikin gaban ayar Allah madaukakin sarki yayi ishara game da irin wahalar ma'aifiya ta sha, wajen daukan ciki, renonsa, har zuwa ga haifar da shi da kuma shayarwa na tsahon shekaru biyu wanda hakan ke yin sanadiyar raunanar jikinta. Domin haka, Allah ya yi ishara da cewa Yaro ya fi mayar da hankalinsa wajen ma'aifiyarsa fiye da ma'aifinsa. Cikin ko wani hali, ka godewa ni'imar Allah, kuma wajibi ne ka godewa samuwar ma'aifa da kuma irin wahalhalu da dawainiyar da ma'aifiya ta yi da kai.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe uku kamar haka:

1-Girmama ma'aifa hakkin su a kan ko wani mutum, domin haka iyaye ko da kuwa kafirai wajibi ne a kyautata musu, babu wani da hakki ya ki kirmama ma'aifansa saboda ba musulim ba ne.

2-A al'adar musulinci, ma'aifiya ta nada matsayi na musaman, saboda ta fi fuskantar wahalhalu game da rayuwar jariri har zuwa girmansa

3-a ko wani yanayi, hakkin ubangiji shi ne gaba a kan hakkin iyaye, kuma, tausayi iyaye kadda ya gafalar da mu game da Ubangiji mahalicin komai da komai.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karantun aya ta 15 cikin wannan sura ta Lukumanu

 

وَوَصَّيْنَا الإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَى وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ
 

 

15-Idan kuwa suka matsa maka kan ka yi tarayya da Ni game da abin da b aka hakikarsa, to kada ka bi su, kuma ka yi zaman duniya da su ta kyakkyawar hanya, ka kuma bi hanyar wanda ya kama zuwa gare Ni da biyayya. Sannan kuma zuwa gare Ni ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.

A cikin gaban ayar da ta gabata, wannan aya na jan hakali yara da su kasance masu kyakkyawar alaka tsakanin su da iyayensu, kuma bai kamata tausayin iyaye ya kawar da tunaninsa, ya kasance yana bin umarnin iyayensa ido rufe, idan iyaye sun kasance suna a kan mumunar akida, to bai kamata mutum yayi musu biyayya a kan hakan ba, ko da kuwa ransu zai bace su kore shi daga cikin gidansu.

Ci gaban ayar na cewa idan ma'aifan mutum suka kasance kafirai ko mushrikai, to ya zama wajibi yayi kyakkyawar mu'amala da su, Mutum bas hi da hakki ya yanke alakarsa da iyayensa don kafirai ne mu mushrikai, matukar suna raye, yayi kyakkyawar mu'amala da su, kuma bas hi da hakki cin mutunci gare su. Kasancewar irin wadannan ma'aifa, mayar da al'amuransu zuwa ga Allah shi ya fi dacewa,domin shi ne masanin komai kuma al'amuran kowa da kaomai na wajen sa.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:

1-biyayyar iyaye tana kaidi, biyan bukatun su ya nada kima a lokacin da bai yi karo da umarnin Ubangiji ba.

2-biyayya ga al'adar kasa ko al'umma, ta nada kima matukar ba ta ci karo da shari'a ko hankali ba, idan ba haka ba biyayya ido rufe ta rashin hanakali ga wadanda suka gabata ba ta da wani kima.

3-A mahangar musulinci babu laifi, rayuwa wuri guda tare da wadanda ba musulmi ba, matukar akidun su, da al'adunsu ba za su tasiri ga musulmi ba.

Yanzu kuma lokaci yayi na sauraren aya ta 16 a cikin wannan sura ta Lukmanu.

 

وَإِن جَاهَدَاكَ عَلَى أَن تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلا تُطِعْهُمَا وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا وَاتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
 

16-(Lukumanu ya ci gaba da cewa):Ya kai dana, hakika ita (mumunar dabi'a) idan ta kasance daidai da kwayar komayya, sannan kuma ta zamanto cikin katon dutse ko kuma cikin sammai ko cikin kassai, to Allah zai zo da ita.Hakika Allah mai tausasawa ne Masanin (komai).

Mafi yawan lokaci, idan mutum ya tashi lissafin ayyukansa na kwarai ne ko kuma akasin haka, abinda ya fi mayar da hankali kansa shi ne manya manyan ayyuka, sai ya gafala da kanana-kanana, alhali kuwa wadannan kananan idan suka taru, suna zama masu yawa, domin haka manyan ayyuka sun fi tasri game da kanana a wajen Mutum.

Wannan Aya ta sake komawa kan nasihohin Lukumanu ga dansa, ta bakin  Lukumanu Allah madaukakin sarki ya ishara kan binciken ayyukan Bayi,Lukumanu na cewa Ya Kai dana!aikinka karami ne ko babba, a bayyane yake ko a boye babu babbanci a wajen ubangiji, komin karamin aikin da ka aikata a boye, ba boyayye ba ne ga ilimin ubangiji, Allah madaukakin sarki zai zo da shi a katun ranar tashin kiyama, kuma bisa wannan za a yi maka hukunci.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:

1-janyo hanakalin yaro dangne kan ya fuskanci cewa akwai ranar hisabi, aikin iyaye ne.

2-Allah masanin ayyukan mutane ne, karami ko babba, imanin mutum da ranar alkiyama tare da yi masa hisabi zai kasance masa sanadin kyara ayyukana sa .

3-Ayyuka mutum bas a kushewa, za su kasance tare da shi har zuwa tashin alkiyama.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

 

 

 

 

Tags