Oct 22, 2017 16:46 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 29-34 (Kashi na 750)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 29 da na 30 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِي إِلَى أَجَلٍ مُّسَمًّى وَأَنَّ اللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
 

29-Yanzu ba ka gani cewa Allah yana shigar da dare cikin rana, Yana kuma shigar da rana cikin dare, ya kuma hore (muku) rana da wata, kowannensu yana tafiya zuwa ga lokaci iyakantacce, kuma hakika Allah masanin abin da kuke aikatawa ne.

 

ذَلِكَ بِأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ الْبَاطِلُ وَأَنَّ اللَّهَ هُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ
 

30-Wadancan (suna samuwa ne) saboda Allah Shi ne tabbatacce, lallai kuma abin da suke bauta wa ba shi ba karya ne, hakika kuma Shi Allah madaukaki ne mai girma.

A shirin da ya gabata mun ishara da fadin ilimi da kudurar ubangiji, da kuma hakan dalili ne na rashin iyaka da kuma rashin karshe na kudurarsa ga mutane, wadannan ayoyi kuwa suna ishara ne a  kan wasu misalai na daban game da kudurarsa ya kuma fadawa ma'aiki da muminai cewa gajarta ko tsahon dare da yini a cikin shekara na tare ne da zuwan kaka hudu wato bazara, rani, damuwa, da kuma hunturu, kuma wannan alama ce na jujjuyawar kasa ce daga Allah madaukakin sarki, a hakikanin gaske, cikin tsarin Ubangiji ne ake samun wannan canji na tsahon yini ko kuma kajartarsa, bisa ilimin da ya bawa bayi ana yi lissafa lokacin.

Ci gaban ayar na cewa ba wai kasa ce Allah ta'ala yake juyawa ba, har ma da rana da wata da hakan ke da tasiri sosai a rayuwar kasa da abin da ke rayuwa a cikin ta, an tsara abubuwa ne ta yadda za su samar da sharuna na rayuwar abin da ke cikin kasa, kama daga tsirai, dabbobi da mutane, wannan canji da kuma jujuyawar kasa, wata gami da rana zai ci gaba har lokacin da Allah madaukakin sarki ya bukata, a lokacin da ya kudiri tayar da kiyama duk wani tsarin Duniya sai rushe.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-Daga cikin hanyoyin sanin Ubangiji, karantu game da dabi'a, surri halittu, kuma Alku'ani mai girma game da wannan haske yayi tabbaci a kansa.

2-Tsarin Duniya da kuma tafiyar abinda ke cikin sammmai, na da kebebben lokaci, wannan duniya ta nada karshe, da hakan kuma na cikin ilimin Ubangiji.

3-Ubangiji shi kadai gaskiya kuma tabbacecce, duk wani abu koma bayansa mai karewa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na  31zuwa 32 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

أَلَمْ تَرَ أَنَّ الْفُلْكَ تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِنِعْمَتِ اللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنْ آيَاتِهِ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ
 

31-Ba ka gani cewa jiragen ruwa suna tafiya a cikin kogi da ni'imar Allah don ya nuna muku(wasu) daga ayoyinsa? Hakika a game da wadannan akwai ayoyi ga duk wanda yake mai hakuri mai godewa.

 

وَإِذَا غَشِيَهُم مَّوْجٌ كَالظُّلَلِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ فَمِنْهُم مُّقْتَصِدٌ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلاَّ كُلُّ خَتَّارٍ كَفُورٍ
 

32-Idan kuwa wasu rakuman ruwa kamar duwatsu suka kere su, sai su kira Allah suna masu tsarkake addini a gare shi, sannan kuma idan ya tserar da su zuwa gaci to akan sami shiryayye daga cikinsu.Ba kuwa mai yin jayayya da ayoyinmu sai duk wani mayaudari mai butulci.

A ci gaban ayoyin da suka gabata, wadannan ayoyi suna ishara ne da wasu alamomin na kudurar Allah guda biyu a doron kasa, tana mai cewa tafiyar jiragen ruwa a bisa ruwa da kuma bulaguron mutane da kuma safarar kayayyaki ta wannan hanya, na daga cikin dalilan da suke nuna kudurar Ubangiji, duk da irin ababen safarar da ake da shi a wannan Duniya kamar motoci, jirgin kasa da kuma jirgin ruwa, amma mafi yawan kayayyaki, ana safarar su ne ta hanyar ruwa, saboda ya horewa mutane hanyoyi masu fadi a bisa ruwa kyauta.

Teku na daga cikin manyan hanyoyin na sadarwa tsakanin yankuna daban daban na Kasa, kasashen daban daban nesa na kusa, hanyoyin teku na hada su. Domin tunatar da ni'imar teku ko kuma kogi, Alkur'ani mai tsarki ya Ambato daya daga cikin abubuwan da suka faruwa  cikin teku da kuma suke ishara game da sanin Allah madaukakin sarki, yana mai cewa: a yayin da teku yayi bori, kunfa na tashi jirgin ruwa na neman kifewa, a cikin irin wannan yanayi, fasinja za su yanke kauna daga duk wani mai ceto, a wannan lokaci ko bas a so za su fuskanci kudurin Ubangiji, cikin ikhlasi za su fara kiran ubangiji domin sun san cewa shi kadai ne mai karfin da zai iya tseratar da su daga hallaka.

Ko da yake mutanan da ba sa godiya, da zarar wannan hadari ya kushe, sun tsira daga hallaka , za su manta da wanda suka dinga kira ya tsiratar da su daga hallaka, har ma wasu su yi inkari da samuwarsa, a bangare guda kuma dama daga cikin mutane sun shiga cikin irin wannan yanayi, bayan sun fuskanci ubangiji, ya kuma ya tseratar da su daga hallaka, sun kasance a kan hanyar Ubangiji kuma sun gyara imaninsu.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-kadda mu dauki ko wata irin halitta da cewa abu mai sauki ne, Kogi, teku da abubuwan dake cikinsu, ayoyi ne na Ubangiji, kuma na daga cikin hanyoyin sanin Ubangiji.

2-Mutum a tsarin fitirarsa, masanin ubangiji ne, to saidai wasu abubuwa ne suke yi sanadiyar rufewar wannan fitira.

3-Imanin wasu gungun mutane tabacecce ne, amma imanin wasu gungun mutane yana canzawa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na  33zuwa 34 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ وَاخْشَوْا يَوْمًا لّا يَجْزِي وَالِدٌ عَن وَلَدِهِ وَلا مَوْلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِ شَيْئًا إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ فَلا تَغُرَّنَّكُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَلا يَغُرَّنَّكُم بِاللَّهِ الْغَرُورُ
 

33-Ya Ku Mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, kuma ku ji tsoron ranar da ma'aifi ba zai amfana wa dansa komai ba, kuma dan shi ma ba zai amfana wa ma'aifinsa komai ba, Hakika alkawarin Allah gaskiya ne, to kada rayuwar duniya ta rude ku, kuma kada shaidan ya rude ku game da Allah.

 

إِنَّ اللَّهَ عِندَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ الْغَيْثَ وَيَعْلَمُ مَا فِي الأَرْحَامِ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ مَّاذَا تَكْسِبُ غَدًا وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ بِأَيِّ أَرْضٍ تَمُوتُ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ
 

34-Hakika Allah a wurinsa (kadai) sanin ranar alkiyama yake, kuma (shi) Yake saukar da ruwa (shi) kuma yake sane da abin da yake cikin ma'aifu, ba kuwa wani mutum da yake sane da abin da zai yi gobe, ba kuma wani mutum da yake sane da kasar da zai mutu. Ba shakka Allah shi ne Masanin sarari da boye.

Wadannan ayoyi su ne karshen ayoyi na cikin suratu Lukuman, suna nasiha ce ga dukkanin mutane game da kiyaye tsoron Allah a cikin rayuwa dangane da dalilin wannan bayyani kuwa suna cewa sabanin duniya da wani gungu na cikin gida ko iyalai zai iya  taimako na magance matsalolin da wani daga cikin iyalan gidan ya fuskanta, a ranar kiyama babu wani da zai iya daukan nauyin dan'uwansa, kuma babu wanda zai iya taimakon wani, domin haka kadda mun yi fariya da alakar dake tsakanin iyalai, kuma kadda mu yi zamanin ba tare da ayyuka na alheri ba za mu shiga cikin tausayi da rahamar ubangiji, hakika Allah madaukakin sarki ya san dukkanin abinda yake a boye kuma bai sanar da mutum wannan ilimi ba, kama daga lokacin tashin alkiyama, lokacin da ko wani mutum zai mutu, da yanayin ko wani jariri a cikin ma'aifar ma'aifiyarsa, abin tuni a nan shi ne ba kwai sanin mace ko namiji shi ne sanin Allah ga jariri a cikin ma'aifar ma'aifiyarsa ba kaiwa, a'a yanayin tunaninsa, shin za a haife shi da rai ko A'a, yaya zai fito Duniya, yaya rayuwarsa za ta kasance idan har ya rayu, da abubuwan da dama da har yanzu dan Adam bai samu wannan ilimi ba, da kuma Ubangiji ne kawai masani game da hakan,amma duk da hakan kada mutum yayi tunanin cewa Allah madaukakin sarki bai san abinda yake aikatawa a boye ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-Abotaka ko dangantaka ba ta amfanarwa a ranar kiyama, a yayin da  da da ma'aifinsa ba za su iya taimakon junarsu ba, to nauyin da ya rataya kan kowa a bayyane yake.

2-tashin Alkiyama gaskiya ne, duk da cewa ba mu san lokacin ba, kamar yadda yake mutuwa a kan ko wani mutum za ta wakana, to amma babu wanda ya san lokaci da kuma wurin da zai mutu, Allah ne kadai ya san wannan.

3-Gidan Duniya, gida ne na mantuwa da gafala, ya kamata mutum kada ya manta da ranar tashin Alkiyama.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

 

 

 

 

Tags