Oct 22, 2017 16:57 UTC

Suratus Sajdah, Aya ta 1-6 (Kashi na 751)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 1 zuwa na 3 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

الم

1-ALIF LAM MIM.Allah ne ya san abin da yake nufi da wannan.

 

 
تَنزِيلُ الْكِتَابِ لَا رَيْبَ فِيهِ مِن رَّبِّ الْعَالَمِينَ 
 

2-Saukar da Alkur'anin da babu kokwanto a cikinsa daga Ubangijin talikai ne.

 

أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُۚ بَلْ هُوَ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّا أَتَاهُم مِّن نَّذِيرٍ مِّن قَبْلِكَ لَعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ
 

3-ko kuwa suna cewa (Annabi Muhammadu kirkirar sa ya yi? A'a,Shi dai (Alkur'ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake don ka gargadi mutanen da wani mai gargadi bai zo musu gabaninka ba, don su shiriya.

Surar Sajadati, na daga cikin surori 29 na cikin alkur'ani da suke farawa da irin wadannan harufa, kamar surar Bakara da ta fara da ALIF LAM MIM.wannan sura mai ta fara da wannan harufa.ayar dake biyar bayanta na nuni da cewa wadannan harufa suna alaka da saukar alkur'ani, kuma tana bayyana girman littafin da aka tsara da wadannan harufa, da babu wani dan adam da  zai iya kawo makamancinsa.

Littafin da aka samar daga gaskiya, kuma bayan gaskiya babu wani abu a cikinsa, ko da yake masu adawa da munkirai ba a shirye suke su amince da shi ba, inda suke zarki ma'aikin Allah (s.a.w.a) da cewa shi ne ya kirkiro sa, sannan kuma yake danganta shi da Allah madaukakin sarki. A yayin da shi kuma manufarsa shi ne gargadi da tsoratar da mutane game da munanan ayyukan da suke yi domin su ji tsoro su daina don kada su hadu da mumunan sakamako, ya kuma shiryar da su zuwa hanya ta gaskiya.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-Duk da cewa Munkirai na kokarin sanya tababa da kokwanto a cikin gaskiyar alkur'ani, to amma game da gaskiyar alkur'ani babu wani rudu da kokwanto, saboda shi daga mahalicin Duniya ne.

2-Alkur'ani littafi ne na shari'a, tushen wannan littafi shi ne sanya tsari a rayuwa.

3-tsoratarwa da kuma gargadi domin nisantar da mutane game da kaucewa hanya da tabewa, na daga cikin manufar tayar da Annabawa da ma'aika.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 4 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

اللَّـهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ مَا لَكُم مِّن دُونِهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا شَفِيعٍ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
 

4-Allah ne wanda ya halicci sammai da kassai da abin da yake tsakaninsu cikin gwargwadon kwana shida sannan ya daidaita bisa Al'arshi, ba ku da wani majibincin al'amari ko mai ceto bayansa.Yanzu me ya sa ba kwa wa'azantuwa?

Ayoyin da suka gabata, sun yi ishara ne game saukar alkur'ani mai girma daga bangaren Allah madaukakin sarki, ita kuma wannan aya tana ishara ne game da halittar halittu daga bangarensa, kamar yadda a saukar da Alkur'ani Ubangiji bas hi da kishiya, dukkanin ayoyin cikin wannan littafi (wato alkur'ani) daga shi ne, haka zalika a wajen halitta ba shi da kishiya, dukkanin halittu na cikin sammai da kassai shi ya halicce su, kuma a kan tsarinsa suke tafiya.

Kamar yadda ayoyi alkur'ani cikin shekaru 23 aka saukar da su  sannu-sannu ga Ma'aiki(s.a.w.a), haka zalika, an halicci duniya sannu sannu cikin zamanuka guda shida, ko da yake mai yiyuwa ko wani zamani daga cikinsu ya dauki lokaci mai tsaho.

Abin bakin ciki, da dama daga cikin mutane, bas a lura da cewa Allah madaukin sarki shi ne kadai ya halicci komai, kuma shi ne kadai abin bauta, sai su koma bayan wata halitta ta daban suna ganin ta a matsayin shugaba ko kuma wacce za ta cece su,alhari kuwa bayan waliyan Allah da Allah madaukakin sarki ya basu ikon ceto babu wani abu ko wani mutum da zai iya ceton mutum.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

1-tsarin al'umuran halittu, yana wajen wanda ya halicce su, ma'ana wanda ya halici mutum bai bar shi yayi abinda ya ga dam aba, ko kuma ya bar al'amuransa ga wasu halittu na daban.

2-Mutum yana bukatar tunatarwa da kuma tunatar da shi game da ni'imomin Ubangiji, idan ba hakan ba zai fada cikin gafala da mantuwa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 5 da na 6 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

يُدَبِّرُ الْأَمْرَ مِنَ السَّمَاءِ إِلَى الْأَرْضِ ثُمَّ يَعْرُجُ إِلَيْهِ فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ أَلْفَ سَنَةٍ مِّمَّا تَعُدُّونَ 
 

5-Yanzu shirya al'amari daga sama zuwa kasa sannan (al'amarin) ya hau zuwa gare shi a cikin ranar da gwargwadon (tsawonta) yake shekara dubu ne daga abin da kuke kirgawa.

 

ذَٰلِكَ عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ

 

6-Wannan (Shi ne) Masanin boye da sarari, Mabuwayi Mai rahama.

A ci gaban ayoyin da suka gabata da suke bayyani a kan kula da tsarin halittu daga Allah madaukakin sarki, wadannan ayoyi sun kara tabbaci a game da hakan, suna cewa dukkanin halittu daga sammai zuwa kassai na karkashin kulawarsa ne, kuma bayan babu wani da yake kula da kuma tsara al'amura halittu a Duniya face shi, ba wai kawai al'amuran wannan duniya ba yake kula da su ba, saidai dukkanin ayyukanku da mu'amalarku har zuwa tashin alkiyama suna komawa ne zuwa gare shi, babu wani abu da ta fita daga ilimi da kuma kudurarsa.

Abinda ake nufi rana a wajen dan adam kamar shekaru dubu ne, ranar alkiyama ce, a wannan rana, za a gurfana a gaban kotun Ubangiji, shi kuma Ubangiji bisa iliminsa maras iyaka, da yake da masaniyar ko wani irin aiki da aka yi a boye ko a bayyane, kuma bisa buwayarsa da rahamarsa zai hukunta bayinsa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-mahalicci, hakimi, mai kula da tsarin rayuwa guda ne, kuma tauhidi na gaskiya shi ne, mayar da dukkanin al'amura zuwa  ga Ubangiji ne, kamar yadda yake halittu, dukkanin abubuwa daga gare shi, kuma zuwa gare shi suke komawa, haka zalika kula da tsarin al'amura daga gare shi ne kuma suna komawa zuwa gare shi.

2-kula da tsarin al'amuran Duniya, da dokokin hukuncin Duniya, na karkashin ilimin maras iyaka na Ubangiji ne.

3-Ilimin Ubangiji game da dukkanin al'amura guda ne.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags