hakin da ya wajaba kan Mu Game Da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) 10
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau, Mine ne Hakki na takwas daga cikin hakkokin da suka wajabta kanmu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a)? Hakika a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan wasu hakkoki guda bakwai da suka wajaba kanmu dangane da Ma'aiki(s.a.w.a) kamar haka, hakkin da'a da biyayya, hakin komawa gare shi domin yin hukunci garesu a yayin wani bullar sabani, hakin soyyaya, hakin yi masa salati, hakin girmamawa kamar yadda Allah madaukakin sarki ya girmama shi, hakin mubaya'a da kuma meka wuya gare shi ga dukkanin umarninsa da kuma hakkin ziyartar shi daga nesa ko daga kusa,Hakin bayar da Khumusi da kuma hakin Uba na Addini,bayan hakan Mine ne Hakki na goma daga cikin hakkokin da suka wajabta kanmu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a)? kafin amsa wannan tambaya, sai a dakace mu da wannan.
**************************Musuc*****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,domin samun tambayar da muka bijiro da ita za mu fara da hasken shiriya na farko wato Alkur'ani mai girma inda Allah tabaraka wa ta'ala ke cewa:(Wannan fa shi ne abin da Allah Yake yin albishir da shi ga bayinsa Wadanda suka b aba da gaskiya suka kuma yi ayyuka na gari.Ka ce: "Ba na tambayar ku wani lada a kan sa (isar da sako) sai dai soyayya ta zumunta (ga zuriyata) Duk wanda ya aikata wani aiki kyakkyawa za Mu kara masa kyakkyawan sakamako a kansa, Hakika Allah mai gafar ne Mai godiya)Suratu Shura Aya ta 23, idan muka yi nazari da wannan Aya mai girma, za mu amfana da fadar Allah madaukakin sarki na cewa (soyayya ta zumunta (ga zuriyata) hakki ne na Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma an umarce shi da ya neme shi a gare shi a wajen Mutane a matsayin lada na girman wahalhalun da a fuskanta wajen isar da sakon Ubangijinsa da kuma shiryar da Bayi zuwa hanyar cimma koramun Aljanna. Wannan gaskiya kuma ta kebanta ne kawai ga Shugaban Ma'aika (s.a.w.a) a tsakanin dukkanin Annabawan Allah tsarkaka,Hakika cikin Suratu Shu'ara an maimata wannan gaskiya, misali fadar Allah madaukakin sarki bisa harshen Annabawan sa masu girma Nuhu, Hudu, Salihu, Ludu da Shu'aibu amincin Allah ya tabbata a gare su, dukkanin su sun ce:(Ba kuma na tambaye ku wani lada a kansa (isar da Manzanci) ladana yana wajen ubangijitalikai kawai) a maimata wannan Aya har so biyar a cikin Suratu Shu'ara bisa bakunan Annabawan da muka Ambato a baya.kuma a bangaren Ma'aikin Allah (s.a.w.a) wannan Ladan da ya bukata, a hakikanin gaskiya albarkarsa na komawa ne ga wannan ya cika wannan gaskiya, kamar yadda Allah tabaraka wa ta'ala yayi ishara cikin Suratu Saba'I (Ka ce:"Abin da na tambaye kun a wani lada to naku ne, ladansa bai zamanto ba sai wajen Allah kawai, kuma Shi Mai tsinkayar komai ne) suratu Saba'I Aya ta 47, haka zalika fadar Allah tabaraka wa ta'ala:(Ka ce (da su): "Ba na tambayar ku wani lada a kansa (gargadin) sai dai ga wanda ya so ya riki hanya tagari zuwa ga ubangijinsa) sutaru furakan Aya ta 57 a kan haka ya bayyana cewa cika wannan Hakki daga cikin hakkokin Annabin Rahama (a.s) hanya ce ta samun kusanci ga Allah madaukakin sarki kuma shi kyakkyawa ne da Allah madaukakin sarki yake yin kari ga aiyuka kyakkyawa na wanda ya cika wannan hakki, ya kuma gafarta masa gami da gode masa a kan hakan , kuma shi Allah madaukakin sarki shi ke mafi alherin masu godiya, godiyarsa kuma za ta kasance ta hanyar sanya Bawa cikin koramun Aljanna kamar yadda yake a bayyane idan muka yi nazari a cikin Ayoyin da suka gabata.
********************************Musuc*****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Huasa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, bayan bayyanin da muka yi a baya, tambayar da za ta biyo baya ita ce Su waye Makusantan Masoyinmu Mustapha (s.a.w.a) da aka wajabta mana ciki wannan hakki na Soyayya ko mawadda a gare Su? Wannan tambaya, Annabin Rahama (s.a.w.a) da kansa ne ya amsa mana ita cikin hadisai da dama da aka ruwaito a bangarori guda biyu wata Shi'a da Sunna, daga cikin su wacce Shekh Suyidi ya ruwaito cikin Tafsirinsa Durarul-Mansur daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: (Ba na tambayar ku wani lada a kan sa (isar da sako) sai dai soyayya ta zumunta (ga zuriyata) ku kiyaye Ni a Iyalan gida Na, kuma ku cika wannan hakki na mawadda a gare su), har ila yau cikin tafsirin Durul-Mansur, Shekh Suyudi ya ruwaito Hadisi daga Ibn Abas yace a yayin da wannan Aya ta sauka sai aka ce ya Ma'aikin Allah su waye makusantanka wadannan da aka wajabta soyayar su? Sai Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: Su ne Ali da Fatima da 'ya'yan Su) idan muka koma hadisan da aka ruwaito a hanyoyi na bangaren Ahlul-bait (a.s), a cikin Littafin Almahasin, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) dangane da tafsirin Ayar da ta gabata sai ya ce:(Ita wato Soyayyar Wallahi farrilla ce da Allah ya wajabta ta ga Bayinsa ga Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da kuma iyalan gidansa tsarkaka (a.s)), a cikin Littafin Usulul-Kafi, har ila yau an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) dangane da tafsirin Ayar da ta gabata yace Sune A'imma wato Shugabanin Shiriya 12 daga cikin iyalan gidan Anabta Tsarkaka, a cikin Littafin Uyunil-Akhbar, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu imam Aliyu bn Musa Arridha (a.s), cikin wani dogon hadisi da aka ruwaito dangane da tambayoyin da ya fuskanta a fadar Ma'amun inda maliman fadar suka tambaye shi dangane da babbancin Itira da Umma, da kuma tafsirin zaben iyalan gidan Anabta tsarkaka a cikin Alkur'ani mai girma sai ya fassar ma'anar Istifa a zahiri ba badini ba da cewa Ayoyi 12 sannan ya Ambato Ayar Mawadda wato soyayyar Ahlil-bait(a.s) har lokacin da ya ce wannan ta kebanta ne ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka har zuwa ranar Alkiyama, kuma ta kebanta ga iyalan gidansa sabanin wasunsu, kuma Allah bai wajabta soyayyar sub a sai da ya san cewa Hakika su har abada ba za su ridda daga Addini ba, ba kuma za su karkata zuwa ga bat aba, duk wanda ya bar ta wato wajibcin soyayyar su, bai kuma dauke ta da hannu biyu ba, ya kuma yi kiyayya ga Ahlul-bait Rasul (s.a.w.a) , ga Ma'aiki (s.a.w.a) yay i kiyayya da shi domin ya bar farilla daga cikin farillar Allah madaukakin sarki) da wannan masu saurare zai bayyana cewa cika hakin Siyayya ga makusantar Anabin Rahama (s.a.w.a) yana tabbatuwa ne ta hanyar Soyayyar Ahlin gidansa Ma'asumai (a.s) wato soyayya ta gaskiya ta hanyar da'a da biyayya tare da yi musu biyu da kuma gabatar da su a kan Ahli da kiai. har ila yau cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi daga Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce:(Ranar Alkiyama Ni mai ceton bangarori 4 ne daga cikin Al'umma ta ko da kuwa sun zo da zunuban Mutanan Duniya, na farko Mutuman da ya taimaki zuriya ta, na biyu Mutuman da ya sadaukar da abinda ke da shi ga iyalan gida Na yayin gunci, na uku Mutuman da ya so zuriyata da Baki da kuma Zuciya, sai kuma Na hudu,Mutuman da yay i kokari wajen bukatun zuriya ta idan an kore su ko kuma suna gudun hijra). Har ila yau cikin Littafin Uyunul Akhbar an ruwaito Hadisi daga Imam Ridha (a.s) ya ce :(kallon zuriya ta Ibada ce) sai wanda ya ruwaito hadisin ya tambaye shi kallo zuwa Shugabani daga cikin su ko kuma dukkanin Zuriyar Annabi muhamad (s.a.w.a)? sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa kallo zuwa ga dukkanin Zuriyar Annabin Rahama(s.a.w.a) Ibada ce matukar dai ba su kaucewa hanyar su ba, ba su kuma tsudu da sabo ba).
Masu saurare, takaicecciyar amsar da za mu fahimta a nan shi ne hakki na 10 daga hakkokin Annabin Rahama (s.a.w.a) da suka wajaba kan Al'umma shi ne hakkin Mawadda da Soyayya ga iyalan gidansa tsarkaka ma'asumai, kuma cika wannan hakki na tabbatuwa ne ta hanyar binsu, yi musu da'a da biyayya da kuma ziyartar su cikin mawadda da soyayya,kamar kuma yadda hakan ke tabbatuwa ga dukkanin zuriyar Ma'aiki (s.a.w.a) ta hanyar son su, girmama su, taimakon su tare da sanya fara'a da farin ciki a cikin zukatan su da makamantan hakan, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon cika wannan hakki da ya rataya kanmu domin albarkar riko da tafarkin Annabin Rahama (s.a.w.a) da kuma na iyalan gidansa tsarkaka.
*********************Musuc*************************************
Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.