Tushen Aikin Imamnci
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata, mun yi bayyani dangane da abinda ake nufi da Imamanci, da kuma babbanci tsakaninsa da Anabta, Hakika Aya ta 124 cikin suratu-bakara ta amsa tambayar tare da bayyana mana hakikanin ma'anar Imami da cewa ba matsayi ba ne da Anabta, domin haka Allah madaukakin sarki yayiwa madadiyansa Annabi Ibrahimu (a.s) alkawarin sanya shi Imami a karshen rayuwarsa kafin ya rike shi Bawa, Annabi, Ma'aiki da Madadayi, domin haka, ita imama, wa'adin Ubangiji ne da Allah madaukakin sarki ya ke zaben wanda yake so wanda kuma bai taba zalinci ba, domin haka tambayar mu ta yau, mine ne tushen aikin Imami?kafin shiga cikin shirin sai a dakace mu da wannan.
*************************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,shirin nayau zai fara da hasken shiriya na farko wato Alkur'ani mai tsarki, inda za mu ga cewa wasu daga cikin ayoyi sun bayyana ma'anar Imamanci da Shiriya , ba wai Shiriya ta gaba daya ba, wato kebarcecciyar shiriya wacce ke kasancewa da umarnin Allah madaukakin sarki, a cikin suratu anbiya'I, Allah madaukakin sarki ya ce:(Muka kuma bas hi Is'haka da kuma Yakubu kari (watau jika) kowannensu kuma Mun sanya shi salihi*muka kuma sanya su shuwagabanni masu shiryarwa zuwa ga addininmu, muka kuma yiwo wahayi zuwa gare su na aikata alheri da tsai da salla da ba da zakka, sun kuwa zamanto masu bauta masa ne) suratu Anbiya'I aya ta 72 da ta 73, domin haka tushen manufar tayar da imami daga Allah madaukakin sarki shi ne shiriya da umarnin Allah madaukakin sarki? To amma anan tambayar da za ta biyu baya ita ce me ake nufi da shiriya da umarnin Allah ? Alkur'ani mai girma ya amsa mana wannan tambaya, inda ya bayyana cewa abinda ake nufu da Umarnin Allah shi ne Iradarsa Takwuniya, wacce babu abinda zai hanata tabbatuwa kamar yadda wadannan ayoyi suke ishara da hakan, Allah madaukakin sarki ya ce:(Umarninsa kawai idan Ya yi nufin wani abu sai ya ce da shi:Ka samu, sai ya samu*To tsarki ya tabbata ga wanda milkin kowane irin abu yake a hannunsa, kuma wurinsa ne kawai za a komar da ku) suratu Yasin Aya ta 82 da kuma ta 83.da wannan Ayoyi masu albarka ya bayyana cewa babbanci Imamanci da kuma shiriya ta gaba daya gami da shiriya kabencecciya, domin Karin bayyani masu mausarare, sai a biyu bayan mun saurari wannan.
**************************musuc********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na karamin sani kukkumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jamhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,idan muka yi nazari game da wasu ayoyi na alkur'ani za mu fahimci cewa hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya tayar da Annabawa masu albishirin da gargadi, kuma babbar aikin su shine shiryar da Mutane, watau abinda ake nufi a nan shi ne bayyanawa mutane hanyar gaskiya da kuma bayyana musu hukunce-hukuncen addinin, ma'ana su masu da'awa ne zuwa ga iradar Allah ta shara'a, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ba mu taba aiko wani manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa don ya bayyana musu (komai), sannan Allah yana batar da wanda ya so yana kuma shiryar da wanda ya so. Shi ne kuwa Mabuwayi,Gwani) suratu ibrahimu Aya ta 4. Amma Imamanci ko shugabanci ba aikinsa ba ne kawai isar da sako na shara'ar Ubangiji kadai, sai dai baya ga isar da sako, aiki imami shi ne kama hannu mutane ya kuma taimaka musu wajen isar da su zuwa gaskiya da kuma ishara takwiniya ta Ubangiji, wannan shi ne abinda Alkur'ani mai girma ya kira da umarni daga sama.Allama tabataba'I cikin Tafsirinsa Almizan mujalladi na farko , yayin da yake bayyani kan fadar Allah madaukakin sarki da yake Magana da Annabi Ibrahimu (a.s) (Ni na sanya ka shugaba a kan Mutane) ya ce Imami ko shugaba shi ne mai shiryarwa, yana shiryarwa da umarni daga sama, Imamanci ko shugabanci a badini kamar wulaya yake ma'ana taimako ga Mutane cikin ayyukansu da kuma shiryar da su,wato abinda shiriyar shugabanci ga mutane yake nufi shi ne isar da su zuwa abinda ake bukata da umarnin Allah madaukakin sarki wanda kuma hakan sha'ani ne na Annabi da Mautane da kuma ko wani mumini da yake shiryarwa zuwa ga hanyar Allah madaukakin sarki ta hanyar nasiha da wa'azi.
Masu saurare, babbanci tsananin ma'anoni guda biyu da suka gabata, nassosi da dama sun yi ishara dangane da hakan, Allah tabarka wa ta'ala ya fadawa Annabinsa mai girma (s.a.w.a) cewa:(…Hakika kai mai gargadi ne kawai, kowadanne Mutane kuwa suna da mai shiryarwa) suratu ra'adi aya ta 7, hakika cikin tafsirin majma'ul-bayyan an ruwaito hadisi daga Ibn Abas na cewa yayin da wannan aya ta sauka, Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Ni mai gargadi ne, Ali kuma mai shiryarwa ne bayana, Ya Kai Ali daga gareka ne masu shiryiwa za su shiryu).a cikin littafin Kamalu-Din da Littafin Basa'iru-darajat, an ruwaito hadisi daga Imam Muhamad Bakir (a.s) yayin da yake tafsirin ayar da ta gabata ya ce:( mai gargadi ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, Ali kuma shi ne mai shiryarwa, kuma ko wani zamani akwai Shugaba daga cikinmu yana shiryar da su zuwa ga abinda Ma'aiki (s.a.w.a) ya zo da shi).
Har ila yau, cikin wani hadisi na daban da aka ruwaito cikin litattan Algaiba na shekh Nu'umani, da Basa'iru-darajat na shekh safar da sauraransu cikin tafsirin ayar da ta gabata, Imam Muhamad Bakir (a.s)ya bayyana cewa:(Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne mai gargadi, kuma Ali (a.s) shi ne mai shiryarwa, Na rantse ba ta gushe da mu ba wato wannan Aya, kuma ba za ta gushe daga cikinmu ba har zuwa ranar Alkiyama), Da wannan masu saurare zai bayyana cewa babbanci dake tsakanin Anabta da imamanci ko shugabanci, shi ne anabta ta kawo karshe da shugaban Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a yayin da shi kuma imamanci ko shugabanci zai ci gaba har zuwa tashin alkiyama, kamar yadda yake kowace al'umma ta nada mai shiryarwa.
Takaicecciyar amsar da za mu fahimta cikin wannan shiri, shi ne imamanci ko shugabanci matsayi ne na ubangiji wanda aikinsa shi ne shiryarwa da iradar Allah, ma'ana taimakon halittu da kuma rike hannayansu da kuma isar da su zuwa ga gaskiya da umarnin Allah madaukakin sarki, da kuma hakan zai ci gaba har zuwa tashin alkiyama.
*********************Musuc*************************************
Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.