Samuwar Imami Cikin Ko Wani Zamani
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,shin yardadden abu ne ga bangarori biyu wato sunna da Shi'a game da dalilin wajibcin samuwar Imami ko shugaba daga Allah madaukakin sarko cikin ko wani zamani?a shirin da ya gabata mun gabatar da wannan tambaya? Inda muka samu dalili daga cikin Alkur'ani mai girma dake bayyana cewa Allah madaukakin sarki ya sanya cikin ko wani zamani Imam iko Shugaba mai shiryarwa da umarnin Allah ta'ala , to yaya dalilin yake a cikin Sunar annabi ingantatta wato cikin sahihan Hadisai? kafin amsar wannan tambaya sai a dakace mu da wannan.
*************************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hakika sahihan hadisai masu inganci daga bangarori biyu wato shi'a da sunna, sun shiryar da mu kan cewa bisa rahamar Allah ga bayinsa, lallai shi bai bar wani lokaci a a doron kasa ba da babu hujjarsa ba wanda yake shiryar da bayinsa daga lokacin Annabi Adamu har zuwa ranar tashin alkiyama, hakika malimam bincike sun fitar da hadisai da dama da suka tabbatar da ingansu da suke bayyani dangane da wannan gaskiya, sannan sun rubuta litattafai a kan hakan kamar su Ihkakul-Haq, da mausu'atu Akbatul-anwar da mausu'atul-Qadir da sauransu. A cikin wannan shiri za mu takaita a kan hadisan da aka ruwaito a bangaren litattafan Sunna, kamar su litattafan Buhari, Muslim, musnad Ahmad bn Hanbal da sauransu, inda a cikin su aka ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:( ba zai kushe wannan al'amari cikin Kuraishawa matukar dai abu biyu sun yi saura a cikin mutane) abinda ake nufi da wannan al'amari cikin wannan hadisi shi ne Imamanci ko shuganci daga Allah madaukakin sarki kamar yadda aka ishara da hakan a aya ta 59 cikin suratu Nisa'I inda madaukakin sarki ke cewa:(Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku bi Allah ku kuma bi manzo, da kuma majibinta al'amuranku) abinda ake nufi da al'amari cikin wannan aya shi ne Imama ko shugabanci domin Allah madaukakin ya sanya yi musu da'a a matsayin yiwa Allah da ma'aikin sa sa'a, wanda hakan ke tabbatar da Ismarsu kuma su nadaddu ne daga Allah madaukakin sarki. Kuma baya ga hakan wannan hadisin ya kafa hujja a kan cewa babu wani lokaci da zai kasance ba tare da shugaba daga cikin kuraishawa yana shiryarwa zuwa ga Allah da umarninsa bayan ma'aikin Allah (s.a.w.a) har zuwa ranar alkiyama.kuma wannan dalili da muka bayyana za mu same kamar yadda maliman hadisai kamar buhari da ya Ambato cikin littafin tarihinsa, da kuma Ahmad cikin Musnadinsa, Ibn Haban cikin sahihinsa, Ibn Abi Shaibatu da Tayalisi, abu ya'ali, tabrasi, Baraz da sauransu dukkaninsu sun ruwaito wannan hadisi daga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda ya mutu ba tare da imami ba yayi mutuwar jahilci) Ibn Haban cikin sahihinsa yayi ta'aliki game da wannan hadisi yana mai cewa Abu Hatim ya ce: fadar ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya mutu mutuwar jahilci, shi ne duk wanda ya mutu ba tare da yayi imanin cewa ba ya nada Imami ko shugaba da yake kiran mutane zuwa da'a ko biyayyar Allah, har sai ya kasance karfafar musulinci da shi a wajen aukuwar wani abu, da kuma tabbacin cewa babu wani kamar shi kuma mai irin soffofinsa daga cikin zuriyar ma'aikin Allah (s.a.w.a), to ya mutu mutuwar jahilci.
*************************Musuc******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, a ci gaban shirin za mu koma bangaren hadisan da aka ruwaito daga hanyoyin ahlul-bait (a.s), su nada yawa sosai, allama majlisi cikin littafinsa mai suna mausu'atu bihar juzu'I na 23 ya tattara wani adadi daga cikin su inda ya bashi suna Al-Idtirar lil hujja) ((الإضطرار للحجة) cikin littafin imama, ba ri mu karanto wasu daga cikin su, hakika cikin littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( a yayin da anabtar annabi adamu ta kawo karshe, sai Allah madaukakin sarki yayi masa wahayi zuwa gare shi: Ya kai Adamu hakika anbtarka ta zo karshe, ka duba abinda ke wajenka na ilimi, imani da kuma gadon anabta, da kuma suna mai girma ka sanya shi ga na bayanka daga cikin zuriyarka (watau danka) Hibatullah, domin nib a zan kasa ba tare da wani masani da zai sanar da da'a da biyayyata gami da addini na ba, kuma ya kasance tsira ga wanda yayi masa da'a da biyayya).
Ya zo cikin hadisin Kudusi a cikin littafin Ilalul shara'I'I daga shugabanmu Imam ja'afaru sadik (a.s) ya ce:( hakika mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauka wajen Annabi Muhamadu (s.a.w.a) yana bashi labari daga Ubangijinsa madaukain sarki, ya ce masa: Ya Muhamadu hakika ni ba zan doron kasa ba face a cikinsa akwai masani ko malami da zai sanar da mutane da'a da kuma yadda za a ayi min biyayya da kuma shiriya ta, ya kuma kasance tsira tsakanin lokacin da wani annabi ya kushe zuwa tayar da wani annabi na daban, kuma har ba zan kasance na bar Iblisi ya batar da mutane ba, da kuma a doron kasa babu hujjar da zai kira mutane zuwa ga shiriya zuwa ga hanya ta, kuma masani ga al'amari na ba, hakika na tabbatar ga ko wata alumma mai shiryarwa wanda ta hanyarsa zan shiryar da masu rabo, kuma ya kasance hujja a kan tabbabu). Kuma a cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu imam muhamad Bakir (a.s) ya ce yayin da wannan aya ta sauka (Ranar da za mu kirawo ko wanne (jinsin) mutane da shugabaninsu) suratu isra'I aya ta 71sai musulmai su ce Ya ma'aikin Allah shin ba kai ba ne shugaban mutane gaba daya? Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Ni ma'aikin Allah ne zuwa ga mutane baki daya, saidai sai kasance bayana shugabani a kan mutane daga iyalan gidana za su tashi cikin mutane, za a karyata su, kuma al'ummar kafirai da bata gami da mabiyansu za ta zalince su, duk wanda ya bi su ya kuma gaskanta su shi daga ni ne kuma yana tare da ni, zai kuma hadu da ni, ku saurara! Duk wanda ya zalince su ya kuma karyata su, bay a daga ni, kuma ba zai kasance a tare da nib a kuma ni na nisanta da shi).
A cikin Littafin Aliyu bn Ibrahim Qummy yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito hadisi daga imam sadik (a.s) ya ce:(mai gargadi ma'aikin Allah (s.a.w.a), mai shiryarwa kuma shine shugaban muminai Aliyu bn Abi talib (a.s), bayansa kuma shugabanin shiriya (a.s) kuma wannan shi ne fadar Allah madaukakin sarki: (kowadanne mutane kuwa suna da mai shiryawa) suratu Ra'ad karshen aya ta 7, sannan kuma Imam (a.s) ya ce: cikin ko wani zamani akwai Imami mai shiryawa bayanane, kuma wannan ayar da ta gabata ta mayar da martani ga masu inkarin cewa cikin ko wani lokaci da ko wani zamani akwai imami ko shugaba, domin shi Allah ta'ala ya dauki alkawarin cewa ba zai bar ba kasa ba tare da hujjarsa ba, kamar yadda Shugaban muminai (a.s) ya fada: ba za a bar doron kasa ba tare da wani shugaba ba daga hujjojin Allah ta'ala, ko ya kasashe bayanenne wanda ya shahara, ko kuma wanda yake a boye, domin kada hujar Allah ta rushe da kuma hujjojinsa bayinanna).
Masu saurare, takaicecciyar amsar da za su fahimta cikin wannan shiri, shi ne ingantattun hadisai daga bangaren Shi'a da sunna sun kafa dalili na samuwar imami ko shugaba zababbe daga Allah madaukakin sarki domin shiryar da halittu da umarninsa madaukakin sarki cikin ko wani zamani daga lokacin Annabi Adamu (a.s) har zuwa ranar Alkiyama, yanzu kuma tambayar da za ta bijoro ita ce wasu siffofi ne ga wannan imami ko shugaba ko kuma sharudan da ya kamata su cika a gare shi? Sai a biyu mu a maku nag aba domin jin amsar wannan tambaya.
*********************Musuc*************************************
Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.