Dalilin Bukutuwar Imami Cikin Ko Wani Zamani
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau minene dalilin bukatuwa zuwa ga samuwar Imami ko Shugaba zababbe daga Allah tabaraka wa ta'ala cikin ko wani zamani? Hakika a shirye-shiryen da suka gabata mun fahimci cewa wasu daga ayoyin Alkur'ani mai girma sun bayyana cewa ko wata al'umma tanada mai shiryarwa, kuma Allah ta'ala ba zai bar kasar b aba tare da hujjarsa ba daga cikin iyalan gidan anabta tsarkaka, to minene dalilin bukatuwar hakan? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
************************Musuc**********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, domin samun amsar tambayar da muka bijoro da ita, da farko za mu fara da riwayar da Shekh Saduk ya ruwaito cikin littafinsa Ilalu shara'I'I daga salihin bawan nan Jabir Alju'ufi, ya ce:Na tambayi Imam Muhamad Bakir (a.s):a wani dalili ake bukatuwa da Annabi da Imami ko Shugaba? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa domin ci gaba da zaman kasa cikin aminci, kuma da wannan Allah madaukakin sarki yake dauke azaba ga mutanan kasa idan ya kasance a cikinsu akwai Annabi ko Shugaba.Allah madaukakin sarki ya ce:(Allah kuwa bai zamanto mai yi musu azaba ba alhali kai kana cikinsu) suratu Anfali Aya ta 33 sannan ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce tauraru amince ne ga abinda ke cikin sammai, iyalan gidana kuma aminci ga ahlin dake cikin kasa, idan tauraru suka gushe, abinda ahlin dake cikin sama suke ki zai zo musu, haka zalika idan iyalan gidana suka kutse abinda ahlin dake cikin kasa suke ki zai zo musu), kamar yadda za kuyi mulahaza masu saurare, shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya kafa hujja da Alkur'ani mai girma da kuma hadisin Annabin Rahama (s.a.w.a) wajen bayyana bukatuwar samuwar Annabi ko Imami a doron kasa, kasancewarsa Imami ko shugaban gaskiya zababbe daga Allah madaukakin sarki wajibi ne na ci gaban kasa cikin aminci da kuma rashin saukar azaba ga halittu sanadiyar fasadi da zubar da jinni.
Da wannan masu saurare, zai bayyana cewa kasancewar Annabi ko Imami cikin ko wani zamani, lutufi da tausayi ne na Allah madaukakin sarki ga bayinsa, domin samuwar Ma'asumi amincin Allah ya tabbata a gareshi yana karewa halittu azabar Ubangiji saboda albarkar shiryarwarsa ga wadanda suke a shirye na karbar shiriyar da kuma kama hannayansu zuwa ga neman gafarar ubangiji kamar yadda aya ta 33 cikin suratu Anfali wacce Imam Muhamad Bakir (a.s) ya kafa hujja da ita ta fadakar da mu, a cikin wannan aya mai girma Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa dafa'I na azabar Ubangiji ga halittu na kasancewa ne bisa samuwar Annabin Rahama Muhamad Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a cikinsu, kuma da kasancewarsu suna neman gafarar Ubangiji, domin jin Karin bayyani sai a kasance da mu bayan sauraren wannan.
**************************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na karamin sani Kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sahsen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,ci gaban shirin zai nazari game da wannan Aya mai girma ta cikin suratu Anfali da mafi gaskiyar masu fada ke cewa: (Allah kuwa bai zamanto mai yi musu azaba ba alhali kai kana cikinsu kuma Allah ba za ya yi musu azaba ba alhali suna neman gafara) suratu Anfali Aya ta 33.ba boyayyan abu ba ne a gare ku masu saurare cewa hakikanin istigfari shi ne komawa ga Allah madaukakin sarki da kuma yi masa da'a da biyayyarsa, da kuma kaucewa sabonsa, tabbatuwar wannan Tuba da da'a na kasancewa ta hanyar komawa gareshi da kuma biyayyarsa da ta ma'aikin sa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, domin haka wajibi ne ya kasance samuwar ma'asumi cikin ko wani zamani kuma ya kasance yi masa biyayya kamar yiwa Allah da ma'aikinsa ne biyayya.
Kuma wannan shi ne abinda Imam Muhamad Bakir (a.s) ya fadakar da mu a karshen hadisin da ya gabata, a yayin da yake ta'aliki ko sharhi game da hadisin da ya ruwaito daga kakansa Mustapha Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka da cewa abinda ake nufi da shuwagabani na iyalan gidansa tsarkaka su ne shuwaganin shiriya da Allah madaukakin sarki ya daidaita yi musu da'a da biyayya da da'ar Ubangiji sannan ya ce:(Ya Ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku bi Allah ku kuma bi Manzo, da kuma majibinta al'amuranku) sannan Imam (a.s) ya ce: su ne kuma ma'asumai tsarkakakku wadanda bas a aikata zunubi , kuma bas a sabo, kuma su tabbatatu ne wadanda su keda muwafaka, ta hanyar su ne Allah yake arzuta bayinsa, kuma ta hanyar su Allah yake zaunar da garinsa, kuma ta hanyarsu ne yake saukar da digon ruwa daga Sama, kuma ta hanyar su ne ake fitar da albarkatun kasa, kuma ta hanyar ake yiwa masu sabo jinkiri kuma ba a gaggauta saukar da ukuba gami da azaba a gare su, bas a rabuwa da kariyar Allah, kuma bas a rabuwa da Alkur'ani shi ma ba ya rabuwa da su, amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya)
Kamar yadda kuka yi mulahaza masu saurare, Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) yayi ishara kan kafa hujjar da yayi a baya na cewa samuwar Imami ma'asumi cikin ko wani zamani shi ne sanadi na dauke azaba daga mutane ko da kuwa shi Imami min bai karbi wannan matsayi a zahiri ba, domin duk da hakan shi ne khalifan Allah a doron Kasa da hujjarsa ke cika ga bayinsa, ya kuma kasance samuwarsa sanadi ne na saukar albarkar Ubangiji da kuma wanzuwar arziki a tsakanin Bayi da kuma dukkanin abinda suke bukata na ci gaba da rayuwarsu a doron kasa, kuma ya basu lokaci har da masu sabo na tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki domin ya rubuta musu rabauta a shafin ayyukansu, kuma wannan Tuba ta kasance ta hanyar komawa zuwa ga khalifan Allah a doron kasa wanda shiriyar Ubangiji ba ta rabuwa da shi cikin ko wani hali da yanayi, ya kuma kasance da wannan mai kudura na isar ga wanda ya bukaci tuba zuwa Allah madaukakin sarki.
Bisa abinda ya bayyana a baya za mu samu amsar tambayarmu ta cikin wannan shiri wato dalilin bukatuwar Imami ko shugaba cikin ko wani zamani, wannan sanadi shi ne cikin lutufi da tausayin Ubangiji ya sanya khalifansa a doron kasa da zai kasance shiriya daga wajen Allah kuma ya kasance ma'asumi mai alaka kai tsaye da Tabaraka wa ta'ala, ya kuma mayar da duk mai neman komawa zuwa ga Allah da kuma rabauta zuwa gare shi domin tsira daga bata da kuma azabar Ubangiji, gami da rabauta da Ajanna da kuma yardarm Allah, da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya mu daga cikin wadanda Shugabanin shiriya za su kama hanunmu zuwa ga yardar Ubangiji.
**************************Musuc******************************
Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.