Nov 23, 2017 12:18 UTC
  • Siffofin Imami 02

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Hakika Shari'ar da Manzo (s.a.w.a) ya zo da ita, ita ce karshen Shari'ar Ubangiji a doron kasa, kuma hakika manzon Allah ya tabbatar da hakan, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya dau alkawarin kare Littafin mai girma wato Alkur'ani mai tsarki, to bayan haka, minene bukatar samuwar Shugaba ko imami ma'asumi cikin ko wani zamani bayan fakuwar Manzon Allah (s.a.w.a)? kafin amsa wannan tambaya sai a dakacemu da wannan.

***************************Musuc*****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, hakika cikin nassosi da dama an bayyana fuskoki da dama a game da wannan bukata, a cikin wannan shiri za mu ambato fuska guda da Alkur'ani mai tsarki ya ambato cikin mafi balagar bayyani, cikin suratu Nisa'I aya ta 59 Allah madaukakin  sarki ya ce:(Ya ku wadanda kuka bada gaskiya, ku bi Allah kuma ku bi manzo, da kuma mjibintan al'muranku, sannan idan kuka yi sabani game da wani abu, to sai ku mai da shi zuwa ga Allah (watau Alkur'ani) da Manzonsa(lokacin da yake da rai, ko kuma sunarsa bayan fakuwarsa) idan kun kasance kun ba da gaskiya da Allah da ranar lahira,(Yin) wancan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawar makoma) suratu Nisa'I aya ta 59, masu saurare kafin muyi bayyani game da dalilin wannan aya na tabbatar da bukatuwar ko wani shugaba ko imami ma'asumi cikin ko wani lokaci bayan fakuwar Ma'aiki (s.a.w.a) bari mu karanto wannan aya dake a matsayin cikar hujja ko dalili na ayar da ta gabata, Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan kuma wani labari ya zo musu na aminci (cin nasara), ko na tsoro(rashin nasara), sai su watsa shi, (don su raunana zukatan muminai). Da dai  za su komar da shi(watau labarin) zuwa ga Manzo ko kuma majibinta al'amura daga cikinsu, lallai da wadanda suke tace shi (labarin) daga cikinsu sun gane shi (labarin da ya kamata su wasta). Da ba don falalar Allah ba a gare ku, da kuma rahamarsa, da ba shakka kun bi shaidan(kan abinda yake kawata muku na miyagun abubuwa) in ban da 'yan kadan daga cikinku) suratu Nisa'I aya ta 83,hakika maliman tafsiri da dama sun wallafa litattafai da dama da suka bayyani kan irin bincike da suka yi game da dalilin