Feb 04, 2016 07:21 UTC
  • Afirka: Harin Burkina Faso

Jama’a masu saurare Assalamu barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako

shirin da kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana  awasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, a wannan makon ma za mu duba wasu daga cikin batutuwa da suka dauki hankula a Burkina, Najeriya, Nijar, Saliyo da sauransu, gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali.
Da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin.
…………………………..
To bari mu fara daga kasar Burkina Faso kan sha’anin tsaro, inda  a cikin wannan mako ne aka kaddamar da wani hari a kan wani katafaren otel a cikin birnin Wagadu, inda ‘yan kasashen ketare suke safka, wanda hakan hakan yay i sanadiyyar mutuwar mutane akalla 21 tare da jikattar wasu, baya ga yin garkuwa da wasu mutanen na daban, wadanda daga bisani aka samu nasarar kubutar da su. Kungiyar Alkaida a yankin Magrib dai it ace ta dauki alhakin kai wannan hari.
………………………………..
To daga Burkina Faso kuma bari mu nufi Saliyo kan batun lafiya, inda rahotanni suka ce cutar Ebola ta sake bulla a kasar, bayan da hukumar lafiya ta duuniya WHO ta sanar da  kawo karshen ta a yammacin nahiyar Afirka baki daya.
Bayan sanar da sake bullar cutar a kasar ta Saliyo dai mahukunta musamman bangaren kiwon lafiya a kasar sun sanar da killace mutane 109 da ake kyautata zaton sun yi mu'amula da matar data mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Gwamnatin Saliyo ta bukaci al’ummar kasar su kwantar da hankalin su bayan ta sanar da killace mutanen saboda mu’amala da matar mai shekaru 22 da ta mutu sa'o'i kadan bayan da hukumar WHO ta sanar da murkushe cutar a yammacin Afirka.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matar ta mutu ne a garin Magburaka dake kusa da iyakar kasar Guinea, inda 'yan uwanta suka mata jana’iza ba tare da sanar da hukumomin lafiya ba.
hukumomin wannan kasa dai sun ce har yanzu akwai wasu mutane 3 da ake nema ruwa a jallo.
Music………………………….
To a can tarayyar Najeriya kuwa batun badakalar nan ta kasafin kudi da kuma canjin da aka samu a cikin wasu takardu da aka gabatarwa majalisar dattijai, yana dagta cikin abubuwan da har yanzu ake ci gaba da Magana a kansu
…………………………..
To a bangare guda kuma batun watanda da kudaden sayen makamai da ake zargin ofishin tsohon mai baiwa tsohon shugaban Naijeriya shawara kan harkokin tsaro Sambo dasuki, da kuma ci gaba da bayyanar mutanen da suka karbi tagomashi daga cikin kudaden, na daga cikin abin da har yanzu yake ci gaba da daukar hankula.
Jam’iyyar SDP dai wadda ta yi kawance da jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin ta fito ta wanke kanta dangane da zargin da ake yi kan wasu miliyoyin kudade da suka shiga hannun jam’iyyar, da ake danganta su da batun watandar kudaden sayen makaman, yayi da jam’iyyar ta ce kudaden ta amsa tsakanin da PDP ne kuma batun siyasa ne ba batun sayen makamai ba.
…………………..
To a jamhuriyar kuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar karatowar lokacin gudanar da zabukan kasar, har yanzu wasu suna korafi karafi dangane da batun yawan ‘yan talara, duk kuwa da cewa tun an riga an sanar da amincewa da mutane 15 da za su kara da juna a yayingudanar da zabukan, yayin da kuma wasu ke ganin hakan dama ga masu domin su darje su zami wanda suke ganin sun gamsu da manufofinsa.
…………………………….
 
Kwamitin tsaro na MDD ya fitar da sanarwa cewa nan bada jimawa ba zai yi kokarin bude wata tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan adawa a kasar Burundi.
Wannan dai na a matsayin bangare na wani sabon shiga tsakani da MDD zata yi a wannan kasa da ta tsunduma cikin rikicin siyasa tun bayan da shugaba Pierre Nkurinziza ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da ya lashe a karo na uku.
A gobe Alhamis ake sa ran jakadun kasashe 15 mambobin kwamitin tsaron mdd zasu soma wata ziyarar kwanaki biyu a birnin Bujumbura babban birnin kasar ta Burundi.
Da yake bayani ga manema labarai danganeda halin da kasar Burundi ke ciki, wakilin  MDD ya ce : ''Matsalar da ake fuskanta ita ce, babu wani tsari na siyasa domin fitar da Burundi daga  rikicin da ta fada a ciki, amma duk da hakan suna tsammani hada bangarorin biyu a teburin tattaunawa.
…………………………………………
To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai Allah ya kai mu mako nag aba za  aji mu dauke da wani jigon kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah