Dec 06, 2017 09:07 UTC

Suratus Sajdah, Aya ta 7-9 (Kashi na 752)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 7 da na 8 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

الَّذِي أَحْسَنَ كُلَّ شَيْءٍ خَلَقَهُ وَبَدَأَ خَلْقَ الْإِنسَانِ مِن طِينٍ

7-Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi, kuma ya fara halittar mutum daga tabo.

 

ثُمَّ جَعَلَ نَسْلَهُ مِن سُلَالَةٍ مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ

8-Sannan ya sanya zuriyarsa daga tataccen ruwa raunana.

A shirin da ya gabata, ayoyin alkur'ani sun yi bayyani game da halittar sammai da kassai da kuma kula da al'amuransu daga Ubangiji madaukakin sarki masani mai hikima, wadannan ayoyi kuwa sun yi tabbaci ne game da abubuwa guda biyu, na farko: duk abinda Ubangiji ya halitta, dabbobi, Mutum da abubuwa, dukkaninsu ya halicce su ne kyawawa, babu wani ragi ko nakasi a halittar ubangiji, na biyu kuwa daga cikin halittun Ubangiji, an ambato mutum,ambatowa ta musaman, saboda shi mutum, an halicce sa ne daga ruwa da tabo, sauran zuriyarsa kuma daga hanyar haifuwa da kuma matakan girma da yake bi a cikin ma'aifar Uwa da sauransu.

Abinda tuni a nan shi ne duk da cewa a zahiri, ruwan dake fita daga jikin mutum ba shi da wata kima, to amma game da gini da kwayoyin rayuwar dan adam, abu dake matsanancin ban mamaki, wannan kuma na daga cikin alamomi dake nuna girman  ilimi da kudiran mahalicci.

Wannan aya na cewa da iradar ubangiji, ya halicci Adamu daga ruwa da tabo kai tsaye, a wannan bangare kuma ya sanya babbanci tsakaninsa da zuriyarsa, saboda shi kansa Adamu daga tabo aka halicce sa, su kuma zuriyarsa daga maniyi, alhali kuma bisa nazarin juyin halitta, halittar Adamu ma ta kasance daga Uwa da Uba, da kuma ta hanyar ruwan maniyinsu. Ba aya ta 7 cikin wannan sura kadai ce ta yi bayyani game da halittar dan adam, ayoyi da dama sun yi tabbaci game da wannan lamari na cewa Adamu ba shi da Uwa da Uba,misali aya ta 59 cikin suratu Ali-Imrana ta bayyana cewa:(Hakika misalign Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne, ya halicce shi ne daga turbaya, sannan ya ce da Shi ka kasance, sai kuwa ya kasance)

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Tsarin samuwar Duniya, tsari ne kyakkyawa, saboda bisa ilimi,hikima da kudura maras iyaka ta ubangiji aka halicce shi, kuma babu wani dalili na ragi ko nakasi a cikinsa.

2-fusahar Allah ne ya samar da abu mai kima daga digon ruwa da tabo, saboda ya halicci Mutum daga turbaya.

3-Ganin cewa an halicci mutum daga digon ruwa, tabo da tataccen ruwa raunana, to bai kamata ya yi dagawa, girman kai tare da ganin kansa ya fi wani.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 5 da na 6 a cikin wannan sura ta sajadati:

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 9 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

ثُمَّ سَوَّاهُ وَنَفَخَ فِيهِ مِن رُّوحِهِ وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ

9-Sannan Ya daidaita shi, Ya kuma busa masa daga ransa, kuma ya sanya muku ji da gani da tunani. Kadan ne kwarai kuke godewa.

Wannan aya tana ishara ne game da matakan halittar Adamu da zuriyarsa, inda take cewa:Allah madaukakin sarki ya daidaita sashen jikin mutum, kuma ya bashi kyautar jiki, sannan kuma ya bashi ruhi, wato rai, ya kuma babbanta mutum da sauran halittu masu rai, Adamu da farko bayan ya kasance tabo, an daidaita shi zuwa mutum sannan bisa so da iradar Ubangiji ya bashi rai, kuma aka bashi rayuwa ta musaman, zuriyarsa ma har zuwa yau na cikin gaba da habbaka, a yayin da aka sanya ruwan maniyi a ma'aifa, a cikin watanni 9 jariri na rayuwa ta musaman a cikin mahaifar ma'aifiyarsa.

Abinda ya kamata mu lura a nan shi ne, abinda ake nufi da ruhi cikin wannan aya shi ne, rayuwa ta musaman da Allah madaukakin sarki ya horewa mutum da ita , ya kuma babbanta shi da sauran halittu masu rai, bai wai ana nufin wani abu daga Allah ya kwarara zuwa jikin mutum, saboda hakan ba abu ba ne mai yiyuwa. Sauran halittu masu rai suma su nada idanu da kunnuwa, to amma ruhu ko kuma rai na musaman da Ubangiji ya horewa mutum shi ya sanya yake idraki ko gano wasu ababe da dauran halittu masu rai bas a iya ganowa.saboda Ubangiji bayan jida gani da ya horewa mutum ya bashi hankali da karfi idraki ko ganuwa da fahimtar abubuwa, wanda da taimakon wadannan ababe ne yake yin nazari game da jinsa da kuma ganinsa kuma yake gano hukuncin halittu, a bayyane yake cewa, mutum na gano nau'in abubuwa ne ta hanyar ilimi kamar na kimiya, ilimin sanin mahalli da sauransu, domin haka ta hanyar ilimi ne mutum ke ci gaba, a yayin da babu wani canji na rayuwar sauran halittu masu rai, a matsayin misali, zumuwar yau da zumuwar shekaru dubu da suka gabata, babu wani canji a tare, sakar da wucan zumar ke yi shekaru dubu da suka gabata, it ace sakar da zumar yau ke yi kuma ruwan zuma iri daya suke bayarwa.

Wannan aya na ishara ne game da mahiman ababe na sani, wato, gani, ji da kuma hankali, wasu daga cikin sun a zahiri ne wasu kuma na badini ne, sani na gwaji da tajruba na samuwa ne ta hanyar gani da ji, sanin kafa dalili na samuwa ta hanyar hankali.

Shakka babu wannan babbar ni'ima ce ta Ubangiji da ta caccanci godiya, amma abin bakin ciki, mafi yawan mutane na mance mahaliccinsu, bas a godewa ni'imar da ya basu,wadanda kuma suke godewa mahaliccinsu, wannan godiya ce daga kyautatawarsa da kuma irin ni'imar da ya horewa mutane maras iyaka.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-daga cikin alamomin tsarkaka da karamcin nau'in mutum, fusamsa ruhun Ubangiji, da kuma bashi rayuwa ta musaman daga Allah madaukakin sarki.

2- abu na farko ga godiyar Allah, shi ne kyakkyawan sanin kai da kuma Ubanigiji,duk wanda bai san kansa ba to ba zai san Allah ba, idan kuma mutum bai san Allah ba, to ba zai yi godiya a gare shi ba.

3-Mutum wani samuwa ne mai bangare biyu, bangaren zahiri (wato gangar jiki) da kuma bangare badini (ruhi) da kuma ya fi kima da rayuwa, mutuman da yake da karamci da falala yana amfani da bangaren jikinsa domin yiwa bangaren ruhinsa hidima, wanda kuma bas hi da wata kira da karamcin yana watsi da bangaren ruhinsa yana biyawa bangaren jikinsa bukatunsa domin jin dadinsa.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags