Afirka: Rikicin Zaria
Jama’a masu saurare Assalamu barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako
Jama’a masu saurare Assalamu barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako, shirin da kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana awasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, a wannan makon ma za mu duba wasu daga cikin batutuwa a Najeriya, Kamaru, Libya, J. Nijar da sauransu, gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali.
Da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin.
MMusic…………………………..
To bari mu fara daga Najeriya, a cikin wannan mako ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada Yusuf Olaolu Ali a matsayin lauyan Hukumar Bincike a kan Rikicin Zaria, wanda ya afkua cikin watan Dimsamba, inda sojojin Najeriya suka zargi wasu daga cikin mabiya sheikh Ibrahim Zakzaki jagoran harkar muslunci ta mabiya mazhabar shi’a a Najeriya da tare wa babban hafsan hafsoshin sojin kasar hanya a lokacin da yake wucewa, ta ksa da cibiyar da suke gudanar da taruka ta Hussainiya, wanda sakamakon hakan sojojin suka kashe dukkanin mutanen da ke wurin tare da rusa ginin baki daya, da kuma kai hari kan gidan sheikh Ibrahim Zakzaki tare da kashe daruruwan mutane da suka samu a gidansa da suka hada har da ‘ya’yansa uku, tare da kama shi da mai dakinsa bayan da sojojin suka harbe su da harsasan bindiga, kamar dai yadda mamaba a kwamitin majalisar addinin muslunci ta kasa da ya ziyarce shi a inda ake tsare da sheikh Zakzaki din ya tabbatar da hakan.
………………………………..
To bari mu sake komawa Najeriya, inda a ranar Litinin da ta gabata ce aka bude wani babban taro kan dimokradiyya, da kuma ganin an samo hanyoyi na tabbatar da girkuwarta yadda ya kamata a Najeriya da ma sauran kasashen Afirka baki daya, wanda ya samu halartar dukkanin jahohin kasar, da ma wakilai daga kasashe daban-daban na Afirka.
…………………………………
A Nijar kuwa wasu daga cikin ‘yan adawa na zargin jam’iyya mai mulki da fara gudanar da wasu ayyuka a yanzu da sunan gwamnati, domin neman kuri’ar jama’a, kamar yadda Musa Alhussaini na jam’iyyar adawa ta Afirka Lumana daga jahar Agadez ya bayyanawa sashen Hausa, amma a nasu bangaren PNDS tarayya mai mulki sun kore wannan zargi.
………………………..
Kotun tsarin mulki a jamhuriyar tsakiyar Afirka ta soke sakamakon zaben majalisar dokokin da aka gudanar a watan da ya wuce, bias wasu kura-kurai da ta ce a tafka alokacin zaben.
Sai dai kotun ta tabbatar cewa, tsofaffin Firai ministan kasar biyu: Anicet Dologuele da Faustin Touadera, su ne za su yi takara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, wanda za a yi a makon gobe.
……………………………
A can Libya kuwa, majalisar dokokin kasar da kasashen duniya suka amince da ita ta yi watsi da gwamnatin hadin kan kasa mai ministoci 32 da zasu wakilci illahirin jihohin kasar.
Cikin 'yan majalisa 104 da majalissar ta birnin Tobruk ta kunsa 89 sun yi watsi da gwamnatin da aka kafa mako guda da ya gabata
Wannan matakin dai zai maida hannun agogo baya a yunkurin samar da zaman lafiya a wannan kasa data kasa tsayuwa bias dugaduginta tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Gaddafi a shekara ta 2011, inda yanzu haka take fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda da suke isa kasar daga koina cikin fadin duniya, inda yanzu haka ‘yan ta’adda ISIS suke hankoron kwace iko da yankunan gabashin kasar da ke da arzikin danyen man fetur da iskar gas.
…………………………………………
To jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai Allah ya kai mu mako na gaba za aji mu dauke da wani jigon kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah