Dalilin Samuwar Imami Na 2
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,shirin na yau zai ci gaba da bayyani a game da siffofin Shugaban gaskiya da nassosi da dama suka bayyana cewa Allah madaukakin sarki ya dauki alkawari ba zai bar doran kasa ba cikin ko wani zamani ba tare da hujjarsa ba a kan bayinsa kuma da zai kasance sanadi na tsiransu. Hakika a shirye shiryen da suka gabata, mun kawo muku ayoyi guda biyar da suke bayyani game da wadannan siffofi da sharudan da ya kamata suka kasance ga Imami ko Shugaban gaskiya kamar haka: na farko ya kasance ma'asumi ga Allah, wanda kuma bai taba yin shirka ba, kuma bai taya yin sabo ba, na biyu ya kasance mai shiryarwa zuwa ga Allah, kuma wadattace game da shiriyar halittun Allah, na uku kuma ya kasance daga cikin masu tabbaci da sakankancewa da Allah madaukakin sarki yake kwada musu mala'ikunsa su kuma kasance daga cikin inuwar al'arshin ubangiji, na hudu ya dabi'antu da mafi daukakar hakuri wajen gudanar da ayyukan shugabanci, sai kuma na biyar ya kasance mai shiryarwa da umarnin Allah, mai taimakawa bayi wajen cimma iradar Allah takwiniya bayan wadannan siffofi, shin akwai wasu siffofi na daban da ya kamata su kasance ga Imami ko shugaban gaskiya? Amma kafin shiga cikin shirin sai a dakace mu da wannan.
***********************Musuc**********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, abin fahimta daga cikin nassosi da dama shi ne daga cikin sharudan Imami ko shugaban gaskiya da Allah madaukakin sarki ya zabe shi shugaba ga mutane, shi ne ya kasance mai gabatar su wajen gudanar da ayyukan alheri da bautar Allah, domin ya kasance abin koyi kyakkyawa a garesu su yi koyi da shi a kan hakan, dangane da wannan sharadi, Allah madaukakin sarki ya ce:(Muka kuma sanya su shuwagabanni masu shiryarwa zuwa ga addininmu, muka kuma yiwo wahayi zuwa gare su na aikata alheri da tsai da salla da ba da zakka, sun kuwa zamanto masu bauta masa ne) suratu Anbiya'I Aya ta 73, idan muka yi nazari game da wannan aya mai albarka za mu fahimci cewa duk wanda Allah madaukakin sarki ya sanya shi imami ko shugaban gaskiya zai kasance tabbatacce da tabbacin ubangiji, ko kuma kamar yadda ake Ambato cikin addu'o'I da taufiki na biyayya, don hakan zai kasance mai gabata a duk wani aiki na alheri, ba ya kiran mutane ga wani abu na da'ar ubangiji, face ya gabace su wajen aikata shi, kamar yadda shahararrun hadisan da aka ruwaito daga shugaban muminai (a.s) suka yi ishara da hakan.kuma wannan siffa wajibi ce da hukuncin makamin Imamanci, domin shi Imami ko shugaban gaskiya shi ne igiyar da take hada tsakanin sama da kasa, kuma shi abin koyi ne da duk wanda yake bukatar sa'ada da kamala yake koyi da shi,Hujjar Allah ba za ta kasance cikakka a kan bayi ba, matukar dai Imami bai gabaci halittu zuwa ga da'ar Allah madaukakin sarki a zamaninsa ba.
Allama tabataba'I cikin Tafsirinsa Al-mizan yayi bayyani karkashin wannan Aya ta cikin suratu Anbiya'I yana mai cewa:Imami shi ne tsani tsakanin mutane da ubangijinsu wajen bayar da alhairan ubangiji na boye kamar yadda Annabi shine tsani tsakanin mutane da ubangijinsu wajen daukan alhairai na zahiri kamar hukunce hukuncen shari'a da suke sauka ta hanyar wahayi a kan Annabi shi kuma ya bayyanawa Al'umma, Imami ko shugaban gaskiya kuma dalili ne mai shiryar da zuciya zuwa matsayinta, kamar yadda Annabi yake shiryar da mutane zuwa akidun gaskiya da kyawawen ayyuka.sannan rahamar Allah ta tabbata a gare shi ya ce dangane da wahayi na aikata alheri na shugabanni a cikin wannan aya: kuma fadar sa madaukakin sarki( sun kuwa zamanto masu bauta masa ne) zahirin wannan aya na kafa dalili da cewa su shuwagabanin shiriya (a.s) sun kasance kafin wannan masu bautar Allah sannan wahayi ya tabbatar da su, kuma ibadar su ga Allah ta kasance ta hanyar ayyukan da Allah madaukakin ya shar'anta musu ta hanyar wahayi kafin hakan, kuma wannan wahayi ya kumshi aikata alheri, bisa wahayi na ilhami ba wahayi na shari'a ba.sannan Allama ya takaita bayaninsa da cewa: abinda aka cimma a cikin wannan nassi shi ne hakika su, sun kasance wadanda aka tabbatar da su daga wajen Allah madaukakin sarki, wadanda aka karfafa da karfin ubangiji, dake kiransu zuwa aikata ayyukan alheri da kuma tsai da salla da bayar da zakka).
***************************Musuc********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai Ambato hadisai da suka tabbatar da wannan ma'ana, daga cikin su hadisin aka ruwaito daga Imam Ridha (a.s) cikin littafin Uyunul-Akhbar yana mai cewa:(Hakika Allah madaukakin sarki ya tabbartar da mu da ruhi daga wajensa mukaddasi mai tsarki da ba milki ba, wannan ruhi bai kasance ga wani ba daga cikin wadanda suka gabata face ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma ita ce tare da shuwagabanin shiriya daga cikin mu ta karfafa su kuma ta sanya su samu nasara), masu saurare wannan ruhi na ubangiji da aka tabbatar da shi ga shugaban A'imomi da Annabawa Muhamadu Dan Abdullahi (s.a.w.a) da kuma shugabanin gaskiya daga cikin zuriyarsa tsarkaka, shi ne mai daukaka na hanyoyin tabbacin Ubangiji, wannan tabbaci na gudana ne tare da sauren shuwagabani da Annabawa gwalgwadon matsayinsu da martabarsu amincin Allah ya tabbata gare su baki daya. Har ila yau masu saurare cikin wata aya ta daban Allah madaukakin sarki na cewa:(Sannan Muka gadar da Littafin ga wadanda Muka zaba cikin bayinmu, sannan daga cikinsu akwai mai cutar kansa, akwai kuma masu tsakaitawa a cikinsu, akwai kuma wanda ya tsere a aikata alheri da yardar Allah,wannan kuwa shi ne falala mai girma) suratu Fadiri aya ta 32. A bayyane yake masu saurare, wannan aya mai girma na bayyana cewa wanda yayi fintin kyau wajen aikata alheri shi ne sama ga waninsa daga cikin bangarorin da Allah ya zaba wajen gadar musu da Littafi, wannan gabata ko tserayya na kasancewa ne da izinin Allah. Wato ta hanyar tabbacinsa madaukakin sarki, kamar yadda aka fahimta a ayar da ta gabata cikin suratu anbiya'I, Hakika mailman hadisi sun ruwaito ingatattun hadisai da suke bayyani game da dalili wannan aya mai girma wacce take kafa dalili na gabacin Imami ko shugaban gaskiya a kan aikata ayyukan alheri, daga cikin wacce aka ruwaito cikin littafin Kafi na sikatul-islam kulaini daga Shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya ce:(wanda yayi tsere ko kuma ya gabaci kowa a aikata alheri shi ne Imami, mai tsagaitawa kuma shi ne masanin Imami ko shugaban gaskiya na zamaninsa, wanda ya zalinci kansa kuma shi ne wanda bai san imami ba).
Masu saurare siffa ta shida, daga cikin siffofin Imami ko shugaban gaskiya wanda saninsa da kuma yi masa biyayya ke tseratar da mutum daga mutuwar jahilci ita ce ya kasance ya tserewa mutane da aikata dukkanin alheri da yardar Allah, da kuma tabbatar da shi gami da karfafa sa, da wannan kuma zai kasance shugaba da dukkanin halittu za su yi masa biyayya.
**************************Musuc******************************
Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.