Jan 25, 2018 17:03 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau menene al'umma ke bukata na fitar muku da kokonto ko zabi game da wajibcin samuwar Imami ma'asumi? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

*************************Musuc****************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, shirin na yau zai yi bayyani game da wata riyawa dake bayyani na daya daga cikin fuskokin bukatuwa zuwa ga samuwar Imami ko shugaba zababbe daga Allah madaukakin sarki cikin ko wani zamani, kuma wannan bukatar mutane zuwa ga abinda zai kawar musu da kokonto da zabi a gare su, a cikin wannan riwaya an bayyana dalilan da suke rubuce a cikin littafin Ibrahim da musa amincin Allah ya tabbata a gare su kamar yadda aka ishara a cikin suratul- a'ala. Riwaya ta biyu da littatafai masu inganci da dama kamar Littafin Rijal na Kashi, littafin kamaludin da ilalu shara'I'I wal amaly na shekh saduk, da littafin Al'ihtijaj na tabrasi da sauransu suka ruwaito daga yunus bn ya'akub ya ce:(na kasance a wajen babban Abdallah Imam Sadik (a.s) tare da wasu jama'a daga cikin sahabansa daga cikin su akwai Hamran bn a'ayun,da mu'umin Attaq, da hisham bn salem,da tayyad da sauransu, kuma ya kasance a cikin su akwai hisham bn hakam shi kuma matashi ne, sai Abu Abdallah imam sadik (a.s) ya ce:shin ba zaka bani labarin yadda kayi da Umar bn abid kuma yaya ka tambaye shi? Sai Hisham ya ce fansar kaina kareku ya dan ma'aikin Allah hakika ni ina jin kunyarku kuma kada kada harshena yayi aiki a gabanka. Sai Imam sadik (a.s) ya hisham idan an umarceku da wani abu ku aikata shi, sai Hisham ya amsa umarnin shugabansa Sadik(a.s) ya fada masa da sahabansa wannan munazara. Masu saurare ruwaito muku wannan munazara bari muyi ishara game da ko wanene Hisham bn Hakam, shi ya kasance daga cikin zababbun sahaban Imam Sadik da Imam Kazem (a.s), kuma yana cikin zababbu na masu fasahar Magana, masu kare Imamanci da gabatar da hujjoji  ga makiya. Shi kuma Umaru bn Abid na daga cikin batatun malimai na zamanin Khalifa Abbasi abi ja'afar  dawaniki, ya kasance kuma yana haifar da makiya ga Imam Sadik (a.s), yana kuma zuhurin zuhudu ko dabi'ar gudun duniya sannan yana kira zuwa ga ayi biyyaya da hukamar bani Abbas yana kuma yakar shugabancin iyalan gidan Annabi Muhamadu (s.a.w.a). bayan wannan takaiceccen bayyani game da kowannarsu bari mu Ambato muku wannan kissa.

Hisham ya cewa Imam(a.s) na samu labarin abinda Umaru bn Abid ke yi da zuma zamansa a cikin masallacin basara, abin yayui girma a gare ni, yadda yake yakar imamancin iyalan gidan anabta tsarkaka yana kuma kare bani Abas.Hisham ya ce hakan ya sanya na fita daga garin kufa na isa kuma birnin Kufa a ranar juma'a, sai na isa masallacin garin na Basara, ina dauke da wani zobe babba, shi kuma yana dauke da sai na ce Ya kai malam ni bako ne, shin za kayi mini izini in gabatar da tambayoyina?shi kuma yana dauke da wani bakin gyalle da ya kasance alama ce na Bani Abas yana sanye da shi sannan kuma ya yafa wani gyalle irinsa na daban Su kuma mutane suna yi masa tambayoyi, sai na shiga cikin mutane na zauna a kan kafafuwana, sannan na ce allah shi gabata malam, ni bako ne shin za ka yi mini izini in gabatar da tambaya ta a game da wata mas'ala? Sai Umar bn abid ya ce Na'am, I tambayarka… sai na ce masa shin ka nada idanu? Sai y ace haba yaro wata irin tambaya ce wannan? Idan ka kasance kana ganin abu menene ya sanya kake tambaya a kansa? Sai Hisham ya  ce na ce wannan ita ce tambayata. Sai ya ce ya kai wannan yaro I tambayarka ko da kuma tambayar wawaye ce… na'am inada idanu.sai n ace me kake gani da su? Sai ya ce mutane da kuma launuka, sai na ce masa shin kanada Hanci ? sai ya ce na'am sai na ce me kake da shi? Sai ya ce ina jin kamshi ko wari da shi. Kafin ci da wannan munazara bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.

*************************Musuc*************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, masu saurare haka, Hisham bn hakam yardar Allah ta tabbata a gare shi ya ci gaba da tambayar Umaru bn Abid game da dukkanin gabobin jikinsa da kuka ayyukan da suke yi har zuwa inda ya tambaye shi a game da zuciya.Hisham ya ce shi ka nada zuciya? Shi kuma ya ce na'am, ya ce me kake yi da ita sai ya ce ina babbance dukkanin abinda suka shigo min daga wannan gabobi na jikina, sai Hisham ya ce shin daga cikin wannan gabobi ba akwai wadatuwa daga zuciya ba? Ma'ana wadannan gabobina ba za su wadatu daga zuciyarka ba? Sai ya ce a'a. sai na ce ta yaya hakan zai kasance alhali ita lafiyarta kalau? Sai Umar bn sa'ad ya kai wannan yaro idan daya daga cikin gabobi sun kokwanto game da wani abu, na shinshinawa ne, ko gani ne, ko kuma na dandano ne, ko kuma na tabawa ne suna mayar da shi zuwa ga zuciya domin ta tabbatar da shi sannan ta kawar da shakku ko kokwanto.

Masu saurare daga aka zo kan wannan gaba, tare kuma da tabbacin Umaru bn abid game da bukatuwar gabobi zuwa ga zuciya a matsayin shugabansu, sai hisham bn hakam ya fara bayyana dalilin bukatuwar dan'adam na shugaba saboda kansa ma'ana domin gyara yakini da tabbacinsa da kuma kore kokwanto, ya zo a karshen riwayar cewa Hisham ya ce domin hakan hakika Allah ya tayar da zuciya ne (ma'ana  ya halarci) saboda kokwanton gabobi? Sai Umaru bn Abid ya ce Na'am, sai ya ce:Ya Aba Marwan Hakika Allah ta'ala ya Ambato hakan, bai bar  gabobi ba har saida ya sanya musu shugaba da zai gyara musu tabbbacinsu ya kuma kore musu shakku da kokwanto a cikin su, shin ta yaya za a bar halittu gaba daya cikin zabinsu, kokwantonsu, da sabaninsu, ba ya tayar musu da shugaba wanda zai magance musu shakunku da sabaninsu? Sai Umaru bn Abid yayi shuru bai ce komai ba, sannan Hisham bn hakam ya sake yi masa wannan tambaya a majalisinsa amma ya kasa cewa komai har sai da ya tashi. Wannan ya ruwaito hadisin ya ce sai Abu Abdallah Imam Sadik (a.s) yayi dariya sannan ya ce Ya Hisham wanene ya koyar da kai wannan? Hisham ya ce Ya Dan ma'aikin Allah  hakan kawai ya kwarara a harshena, sai Imam (a.s) ya ce Ya Hisham wannan wallahi shi ne yake rubuce cikin littafin Ibrahima da Musa amincin Allah ya tabbata a gare su.

Masu saurare da wannan ya bayyana hujar daga daga cikin fuskokin bukatuwar dan'adam zuwa ga shugaba ma'asumi zababbe daga Allah madaukakin sarki cikin ko wani zamani, domin kawar da shakku, da sabani gami da jayayyar da ta biyo bayan babbancin ra'ayi kai har ma da karatun litattafai,  ba za a yi tunanin cewa dakile ko wani irin shakku ba tare da shugaba ma'asumi ba zai samar da nutsuwa a cikin zukuta kasancewarsa yana Magana ne daga Allah madaukakin sarki kuma hukuncinsa na a matsayin hukuncin Allah tabaraka wa ta'ala.

**************************Musuc******************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.