Jan 25, 2018 17:18 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau minene dalilin da ya sanya Alkur'ani mai girma bai Ambato sunayen shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsarkaka kamar yadda ya Ambato shugabar su Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ba? Kuma menene dalilin da ya sanya aka wakilta wannan babban al'amari ga ma'aiki (s.a.w.a)? , amma  kafin hakan sai a dakacemu da wannan.

************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, hakika wannan tambaya an bijoro da ita tun cikin karni na biyu bayan hijrar ma'aiki (s.a.w.a) daga Makka zuwa Madina, kuma shugabanin shiriya amincin Allah ya tabbata a gare su sun bayar da wannan amsa ta irin amsarar alkur'ani mai girma dake a matsayin kololuwar balaga, an ruwaito hadisi daga Sikatul-Islam kulaini rahamar Allah ta tabbata a gare shi a cikin littafinsa mai suna Usulul-kafi daga Abi Basir yardar Allah ta tabbata a gare shi ya ce: na tambayi babban abdallahi Imam Sadik (a.s) game da fadar Allah madaukakin sarki:( ku bi Allah ku kuma bi Manzo, da kuma majibinta al'amuranku) suratu Nisa'I aya ta 59, sai Imam (a.s) ya ce ta sauka ga Aliyu bn abi talib da hasan da husaini amincin Allah ya tabbata a gare su, sai na ce da shi , hakika mutane na cewa menene ya sanya ba ambaci sunan Ali da iyalan gidansa a cikin Littafin Allah madaukakin sarki ba?sai Imam (a.s) ya ce ka fada musu cewa hakika ma'aikin Allah (s.a.w.a) an saukar masa da salla (ma'ana ayoyi dake bayar da umarnin a tsaida salla) amma ba a Ambato cewa ayi raka'a uku ko hudu ba, har saida ya kasance ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne ya fassarawa al'umma yadda za su yi sallar kuma raka'a nawa ne a ko wata sallar .sannan imam (a.s) ya kara da cewa kuma an saukar a gare shi (s.a.w.a) ayoyin zakka, amma ba a Ambato cewa ba cikin wani dirhami arba'in har saida ya kasance ma'aikin Allah tsira da amincin Allah a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya fassara, haka kuma aka saukar da ayar Hajji a gare shi, ba a Ambato cewa ku yi dawafi so bakwai ba, har saida ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya fassara musu hakan.

Masu saurare, bayan da Imam sadik (a.s) ya Ambato wadannan misalai daga mahiman rukunonin musulinci da aka saukar da ayoyinsu cikin  Alkur'ani mai girma kuma aka wajabtawa mutane ba tare da fayyace adadinsu da kuma yadda za a yisu ba, sannan kuma ya wakilta wannan zuwa ga Annabinsa Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka bayan wannan  sai ya zo da al'adar Alkur'ani cikin al'amarin shugabanin shiriya da kuma majibintar al'amuran musulmi yana mai cewa sai wannan aya ta sauka:( ku bi Allah ku kuma bi Manzo, da kuma majibinta al'amuranku) wannan aya ta sauka a kan Ali da hasan da husain sannan dangane da Imam Ali (a.s) ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce (duk wanda na kasance majibicin al'amarinsa to majibicin al'amarinsa ne, sannan ya ce na yi muku wasici da Littafin Allah da kuma iyalan gidana, hakika ni na tambayi Allah na kada ya raba tsakaninsu har sai sun tarar da ni a bakin tabki, kuma Allah ya bani wannan, sannan ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce ba za su koyar da sub a domin su sune mafi sani da ku, sannan ya ce : Hakika ba za su fitar da ku daga kofar shiriya har abada ba, kuma ba za su shigar da ku cikin kofar bata har abada ba.

Don haka masu saurare, Hakika Annabi Muhamadu (s.a.w.a) ya bayyana misdakin ayar da'ar majibinta al'amura da mafi balagar bayyani domin cikar hujja a kan bayi wajen wajibcin yin biyayya a gare su, kuma ya katse hanyar masu da'awar wannan matsayi cikin hadisai da dama da musulmai suka ruwaito ta hanyoyi daban daban, wannan Kenan, na biyu kuma hakika Alkur'ani mai girma kansa ya gaskanta wadannan hadisai a cikin wasu ayoyi na daban, kamar yadda ya zo cikin wannan hadisi, shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(da ma'aikin Allah (s.a.w.a) yayi shuru bai bayyana al'amarin iyalan gidansa tsarkaka ba, da iyalan wane da wane sun yi da'awar wannan matsayi. Saidai kuma Allah madaukakin sarki ya saukar da aya cikin littafinsa domin ya gaskanta Annabinsa (s.a.w.a) fadar madaukakin sarki:(Abin da Allah yake so kawai shi ne ya kawar muku da duk wata kazanta, ya ku iyalan gidan Annabi, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa) suratu ahzabi aya ta 33,yayin da wannan aya ta sauka a gidan Umu salma sai ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya sanya Ali, Hasan, da Husaini da Fatima amincin Allah ya tabbata a gare su karkashin mayafi, sannan ya ce Ya Ubangijina ko wani annabi yanada iyalai da ma'auni, wadannan kuma su ne iyalan gida na da ma'auni na, sai Umu salma ta ce Shin ni ba na daga cikin iyalanka? Sai Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce da ita Hakika ke kina zuwa ga alheri, saidai kuma wadannan su ne iyalan gidana da ma'aunina).

**************************Musuc************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kada a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhororiyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, masu saurare, idan muka nazari a game da ababen da muka Ambato a sama za mu samu cewa hakika Alkur'ani mai girma ya Ambato shugabanin shiriya na iyalan gidan anabta tsarkaka da mafi balaga na ambaton sunayensu, hakan kuwa na wakana ne ta hanyar Ambato siffofinsu da kuma kasancewar ma'asumai da Allah ta'ala ya kawar musu da duk wata kazanta, , ya kuma tsarkake ku tsarkakewa, a cikin wannan hakika akwai tunatarwar ubangiji mai tausayi  zuwa ga hakikanin al'amarinsa madaukakin sarki na yin biyayya ko da'a ga iyalan gidan anabta tsarkaka, ba wai kawai don kasancewarsu  iyalan gidan masoyinshi Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ba, saidai don kasancewarsu ahli na Isma da tsarki (ma'ana wadanda aka basu kariya na aikata sabo) kuma sahiban mafi martaba da koluluwar Imani ga Allah madaukakin sarki., hakika a karshen wannan hadisi Imam sadik (a.s) yayi ta'aliki a game da ma'anar kazanta cikin ayar da ta gabata yana mai cewa ma'anar kazanta a wannan aya shi ne kokonto, wallahi ba ma kokonto a game da Ubangijinmu har abada.

Imam Sadik (a.s) ya ci gaba da hadisin yana ishara da cikar hujja ta hanyar sakon alkur'ani da kuma hadisin ma'aiki (s.a.w.a) domin bayyana yanayin khalifofon annabi (s.a.w.a) yana mai cewa:(a yayin da Allah ya dauki ran annabinsa (s.a.w.a), ya kasance Ali shi ne mafi cancantar wannan matsayi a tsakanin mutane saboda yawan hujjojin da ma'aiki (s.a.w.a) ya fada kansa da kuma yadda ya dauki hanuwansa mai albarka ya fada wa mutane, a yayin da karshen khilafancin Imam Ali (a.s) ba zai iya ba kuma ba zai yi ba, ya sanya dansa Muhamd bn Ali ko Abas bn Ali ba ko kuma daya daga cikin 'ya'yansa kan wannan matsayi, da Hasan da husaini sun ce hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya saukar a garemu kamar yadda ya saukar gare ka, yayi umarnin da yi mana da'a, kamar yadda yayi umarni da yi maka da'a, kuma hakika ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya isar da wannan sako zuwa ga mutane game da wulayarmu kamar yadda isar da naka wulayar, ya kuma kawar mana da kazanta kamar yadda ya kawar da naka, bayan khalifancin Imam Ali (a.s), ya kasance Imam Hasan (a.s) shi ne mafi caccanta da wannan matsayi).

Takaicecciyar amsar tambayar mu shi ne daya daga cikin mafi mahimancin sirrin rashin Ambato sunayen iyalan gidan anabta a cikin alkur'ani mai girma shi ne kamar yadda ke gudana a sunar alkur'ani na Ambato gundarin abu, ya bar ma'aiki (s.a.w.a) ya bayyanawa al'ummarsa kamar yadda ya kasance ga salla, zakka da hajji, na biyu kuma shi ne abinda Alkur'ani ke so shi ne tunatarwa zuwa ga sirri na al'amarin ubangiji ta hanyar biyayya ga iyalan gidan anabta tsarkaka, amincin Allah ya tabbata a gare su, saboda kasancewarsu ahlin Isamar ubangiji, kuma mafi cancantar mutane wajen isar da umarnin ubangiji, da khalifancin ma'aikin Allah (s.a.w.a), da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yi musu da'a da biyayya kamar yadda ya bukata don albarkar alkur'ani mai tsarki.

**************************Musuc******************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.