Ranar Yaki Da Babban Tari
A yau shirin zai muyi waiwaye ne akan ranar yaki da cutar tarin huka ta duniya, wace MDD ta ware domin kara fadakar da jama'a kan illolin wannan cutar da nufin kawar da ita a doron duniya. Taken ranar ta bana dai shi ne '’Kawar da Tarin Fuka a Rayuwata'’.
To madallah, ranar 24 ga watan Maris ita ce ranar da MDD ta ware a kowa ce shekara domin kara himma wajen yaki da cutar tarin huka, kuma a zagayowar irin wannan ranar akan fadakar da al’umma kan illolin wannan lallar cuta domin kawar da ita a doron duniya.
Taken ranar ta bana dai shi ne 'Kawar da Tarin Fuka a Rayuwata’’
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kimanin kashi daya cikin uku na al'ummar duniya na dauke da kwayar cutar da ke haddasa ta.
Wani batu da ke tasowa a baya-bayan nan dai shi ne irin alakar da ke akwai tsakanin tarin na huka da kuma cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.
Masana sun ce dalilin da ya san tarin ke yawan kashe masu cutar kanjamau shi ne cewa ba su da kariya a jikinsu da za ta yaki tarin huka.
Cutar Tarin Fuka (TB, wato tuberculosis) ta dade tana addabar bil-Adama. An san wannan ciwo tun kafin a sami magungunan kashe kwayoyin cuta (wato antibiotics).
Babban abin da yafi yada cutar shi ne iska wanda idan mai daukeda ciwan yayi tari ko atishawa, zai iya yada shi ga wani ko wasu.
Ciwon yana haddasa tari, fitar da majina da jini da matsananciyar rama; wanda sananin wannan ciwo, miliyoyin mutane ne suke rasa rayukansu.
shirin a yau ya tattauna da Dr Attahir Sallah na sashen kula da masu fama da babban tari a babbar asibitin Maradi dake jamhuriya Nijar, a cikin shirin kuma mun tattauna da wasu masu fama da cutar.