Apr 27, 2016 11:27 UTC

Jama’a masu saurare Assalamu alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka, shirin da kan duba wasu daga cikin lamurra da suka wakana a cikin wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, a yardar Allah shirin zai leka kasashen Najeriya, Nijar, Masar, Gabon Kenya da sauransu, gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin.

To bari mu fara daga tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan mako ne kungiyar kare hakkokin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta fitar da wani bayani, wanda  acikinsa ta bayyana cewa sojojin Najeriya sun tafka ta’asa kan mabiya mazhabar shi’a a Zaria, ta hanyar  yin kisan gila a kansu tare da bizne daruruwan gawawwakin wadanda suka kashe  a cikin wani katafaren kabari a wani wuri a gefen birnin Kaduna, inda kungiyar ta ce wannan abin da aka yi ya sabawa kowadanne irin dokoki na duniya,kuma ta ce za ta ci gaba da bin kadun lamarin tare da harhada bayanai kan hakikanin abin ya faru, wanda nan ba da jimawa za ta fitar da cikakken rahotonta kan dukkanin abin da ya faru a Zaria.
Kan wannan batu jam’iyyar Labour a Naeriya ta fito ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da kisan gillar da aka yi a Zaria, tare bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a gane xewa mulkin demokradiyya ake yi ban a sojoji ko da gurguzu ba, kamar dai yadda shuagaban jam’iyyar Alh. Abdulkadir Abdulsalam ya sheda ma naema labarai a birnin Abuja.
Mosahebeh (1)…………………………….
Shi ma a nasa bangaren Dr. Bawa Abdullahi Wase, wanda masani ne kan harkokin tsaro a mataki na kasa da asa, kuma masani kan lamrra da suka danganci manyan laifuka da shari’a, ya bayyana ma sashen Hausa mahangarsa kan wannan rahoto na Amnesty dangane da kisan gillar Zaria.
Mosahebeh (2)…………………………..
To za mu sake komawa tarayyar Najeriya daga bisani, amma yanzu bari mu leka makwabciyarta J. Nijar, a cikin wannan makon ne wasu daga cikin kungiyoyin farar hula suka shirya gudanar da wani gangami a birnin Yamai domin nuna damuwarsu kan wasu abubuwa da suke korafi a kansu ga gwamnati, amma jami'an tsaro sun hana su gudanar da wannan gangami da zanga-zanga.
Musa Changarai , yana daga cikin wadanda suka shirya gangamin, ya yi wa sashen Hausa Karin bayani kan batun.
Mosahebeh (3)………………………
To a bangare guda kuma a J. Ta Nijar, jami'an tsaron kasar sun sanar da kama wasu mutane fiye da 100 da suke da nufin fita daga kasar ba bisa ka'ida ba zuwa kasar Algeriya, daga cikin mutanen kuwa da mata da kanan yara ne suka fi yawa, wadanda mafi yawansu sun fito ne daga yankin Kantche na jahar Damagaram.
A lokutan baya ne jami'an tsaron na Jamhuriyar Nijar suka sanar da mutuwar wasu daga cikin mutanen da suke tafiya zuwa kasar Algeriya ba bisa kaida ba domin yin bara, wanda hakan yasa daga bisani hukumomin J. Nijar suka sanar da cewa sun cimma yarjejeniya tare da mahukuntan Algeriya, domin dawo da wasu daga cikin 'yan kasar da suke can Algeriya suna zaune ba bisa kaida ba.
Music…………………………. 
A can kasar Masar kuwa jami'an tsaro da suka hada da sojoji sun dauki matakan hana gudanar da zanga-zangar da al'ummar kasar ke yi, domin nuna rashin amincewarsu da mika tsibiran kasar guda biyu kyauta ga kasar Saudiyya, ba tare da maincewar al'ummar kasar ba, inda kasar ta Saudiyya a nata bangaren ta yi alkawalin saka hannyaen jari a kasar ta Masar domin taimaka mata ta fuskar tattalin arziki.
Wasu daga cikin lauyoyin kasar ta Masar sun fitar da wasu bayanai da ke tabbatar da cewa wadannan tsibirai na Siran da Sanafir mallakin kasar Masar ne a tsawon tarihi, domin kore duk wani shakku kan mallakar wadannan tsibirai ga kasar.
Wannan mataki dai ya jawo cece kuce ta fuskar siyasa a kasar ta Masar, inda Sisi y adage kan matsayinsa na kyautar da wadannan tsirai ga Saudiyya, yayin da 'yan siyasa da kungiyoyin lauyoyi da al'ummar kasa suka dage a kan cewa ba za su taba  amincewa da hakan ba.
Music………………………
A can kasar Kenya ma jam'iyyun adawa ne suka gudanar da nasu gangamin, inda su kuma suk ebukatar a rusa hukumar zaben kasar, a wani mataki da suke ganin shi ne yafi dacewa da sauye-sauyen da suke fatan ganin an yi domin tabbatar da cewa an yi zabe na gaskiya a shekara mai zuwa.
Jam'iyyun adawar wadanda suka gudanar da gangami a birnin Nairobi sun ce ba a yi m usu adalci a zaben shekara ta 2013 ba, kuma a wanann karon ba za su amince da hakan, domin kuwa har jami'an hukumar da suke zargi da tafka magudi su ne kan shugabancin hukumar, a hakan suke yi kira da a sallame su kuma a maye gurbinsu da wasu da za su kamanta adalci.
Music………………………..
Bari mu sake komawa Najeriya, inda a cikin wannan makon ne shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari, ya bayar da umarni ga ma'aikatar ayyukan gona ta kasar da ta fitar da abinci kimanin ton 10,000 da ke ajiye a rumbunan ajiye abinci na gwamnati, domin sayar da ga mutane, da nufin rage radadin talaucin da ya addabi al'ummar najeriya a halin yanzu, duk kuwa da cewa ba a san yanayin farashin da gwamnati za ta sayar da abincin ba.
Alh. Abubakar Ali masani kan harkokin tattalin arzikia Najeriya, ya yi sashen Hausa Karin bayani kan yadda yake kallon wannan batu.
Mosahebeh (4)………………………..
A Gabon kuwa 'Yan hamayyar siyasa ne a kasar suka kira yi shugaba Ali Bongo da ya yi murabs daga kan mukaminsa.
Jam'iyyun adawar siyasa da kuma na wasu kungiyoyin fararen hula na kasar ta Gbanon sun yi kira da a hana Ali Bongo sake tsayawa takarar shugabancin kasar sannan kuma sun bukace shi da ya yi murabus ba tare da wani bata lokaci ba.
Sai dai kakakin gwamnatin kasar ta Gbano Alain-Claude Bille By Nze ya yi watsi da kiran na 'yan adawa, yana mai cewa; Matakin nasu yana nuni da cewa basu da wani shiri na aiki a kasa a yayin zabe.
"Yan adawar dai suna zargin cewa; Ali Bongo ba dan asalin kasar ba ne,s aboda haka ba shi da hakkin rike mukamin shugabancin kasar.

Music…………………………..
A Uganda kuwa Wani Sojan Kasar ne ya yi harbi kan mai uwa da wabi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Wani babban Jami'in 'yan sanda a garin Kanango mai suna; Ford Ananga, yana cewa; Sojan mai suna Moris Kiyatoko ya bude wuta akan abokan aikinsa 'yan sanda a cikin bariki, sanann kuma ya fita zuwa cikibiyar kasuwanci ta garin inda acan ma ya yi harbi kan mai uwa da wani.
Majiyar 'yan sandan ta tabbatar da mutuwar fararen hula biyar da kuma jikkata wasu sojojin.
Tuni dai aka kame sojan domin gudanar da bincike akan musabbabin harbin nashi.
Music……………………..
Jama'a masu saurare lokacin da muke da shi ya kawo jiki a nan zamu dakata sai Allah ya kai mu mako na gaba  za a ji mu dauke da wani shirin, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum wa rahmatullah.





Tags