Apr 27, 2016 14:27 UTC

A cikin shirin na yau zamu yi waiwaye ne akan ranar duniya ta shayar da jarirai da nonon uwa, wace MDD ta ware a wani yunkuri na zaburar da iyaye muhimmancin shayar da yara da nonon uwa.

Masana sha’anin kiwan lafiya dai na cewa shayar da yara da nonon uwa zalla a watanni shida na farko yana da matukar anfani ga lafiyar jarirai da samar da abinci masu gina jiki da kuma kariya daga cututuka masu illa ga kananan yara.

A hannu daya kuma masanan na cewa yana da muhimmanci ga jarirai da kuma mahaifiyar kanta saboda yana kare mahaifiyar a kan samun juna biyu da wuri, sannan kuma yaro zai sami lafiya sosai saboda yana kareshi daga cututuka kamar su gudawa, da kuma wadansu dabam dabam.


Tags