May 03, 2016 14:05 UTC

A Shirin na yau, zamu tabo batun cutar zazabin cizon sauro ko maleriya, wace hukumar lafiya ta duniya ke cewa har yanzu fa da sauran rina–a-kaba a yunkurin kawar da ita musamen a kasashe masu tasowa.

Wani kiyatsi na MDD ya nuna cewa mutane 338,000 ne ke mutuwa duk shekara sanadiyyar kamuwa da cutar a duniya, yayin da wasu miliyan 414 ke kamuwa da cutar, kuma kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a nahiyar Afirka suke. 

A rahoto data fitar a bana hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane da dama ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar a duniya muddin dai ba' a dauki wani mataki ba.

To domin tattauna wannan batun a yau muna tare da Dr Bukar Gremat kwararen likita a tarraya Najeriya, kuma kuma yayi muna bayani kan muhimmancin keba ranar yaki da cutar wace ke gudana ko wace 25 ga watan Afrilu.

 hukumar lafiya ta bayyana kasashen Algeria da Botswana da Cape Verde da Comoros da Afrika ta Kudu da kuma Swaziland a matsayin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen fada da wannan cuta, tare da hasashen kawo karshenta a shekara ta 2020.

Sauran kasashen duniya da ake sa ran za su kawo karshen cutar nan da shekara ta 2020 sun hada da China da Malaysia da Koriya ta Kudu da kuma wasu kasashe takwas da ke yankin Lantin Amurka.

Sanarwar da hukumar lafiyar ta fitar a farkon watan Afrilu ta ce, nahiyar turai da yankin tsakiyar Asiya duk sun kawo karshen cutar ta zazzabin cizon sauro a cikin shekara ta 2015, amam ta gagara a kasashe da dama na Afirka.

A cikin bayani da likita ya yi, ya dauko misalai da kasashen turai suka dauka wajen kawar da wannan cutar, ko Dr ko matakan da kasashen Afirka suke dauka basu yin tasiri ne wajen kawar da cutar ?

Kimanin mutane miliyan 214 ne suka kamu da wannan cutar a bara, inda kusan dubu 450 daga cikin su suka rasa rayukansu kamar yadda hukumar WHO ta ce.