May 03, 2016 14:38 UTC

A kasahen Chadi da Nijar zamu duba batun tsawaita dokar ta baci a wasu sasan kasashen, akwai ma wasu tarin labaren da suka fi daukan hankali cikin wannan mako a Nahiyar ta Afirka.

Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka, barkan mu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a mako,

shirin sashin hausa na muryar jamhuriya musulinci ta Iran da kan yin dubi kan muhimman lamurra da suka wakana a wasu kasashen nahiyar a cikin mako.
 
Idan dai za’a kasance damu a cikin shirin na yau zamu leka a tarayya Najeriya kan batun yerjejeniyar tsaro da kasar ta cimma da Faransa, zamu kuma duba wani taro da wasu shugabannin kasashe da kuma kungiyoyin kare gandun daji suka yi kan kawo karshen cinikin hauren giwa, zamu kuma leka kasahen Chadi da Nijar kan batun tsawaita dokar ta baci a wasu sasan kasashen, akwai ma wasu tarin labaren da suka fi daukan hankali cikin wannan mako a Nahiyar.
Da fatan dai za'a kasance damu a cikin shirin tare da ni Hassan barka.
……………………………….
To madallah, bari mu dauko shirin kan batun yerjejeniyar tsaro da kasashen najeriya da faransa suka cimma a wannan mako.
Bangarorin biyu sun cimma wannan yerjejeniyar ce a yayin ziyara da ministan harkokin wajen faransa Jean Yves le Drian ya kai a Abuja fadar mulkin kasar,
Daga cen din ga rahoto da wakilin mu Muhammad Sani Abubakar ya hada mana.
……………………..01………………
To har yanzu muna kan batun tsaro a cikin makon nan ne gwamnatibn kasar Chadi ta tsawaita dokar ta-baci na tsawon watanni shida domin dakile hare haren kungiyar Boko haram musamman a yankin tabkin Chadi.
Majalisar dokin kasar ce ta amince da gagarumin rinjaye da matakin tsawaita dokar da aka kafa tun ran 9 ga watan Nuwamba bara…………..
To a cen jamhuriya Nijar batun yayi kama da hakan inda hukumomin kasar suka tsawaita dokar ta da watanni uku a jihar diffa mai fuskantar barazana kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin ta dau wannan matakin ne a yayin taron majalisar ministocin ta na baya bayan nan
to domin jin ko yaya mazauna yankin suka ji da wannan doka, daga nan birnin Tehran na tuntubi Mal. Usman Almustafa wani mazaunin birnin na Diffa, ga kuma abunda ya shaida min
……………………….. 02…………………
To yanzu sai kasar Africa ta Kudu inda wata Kotu a kasar, ta ce Shugaba Jacob Zuma zai fuskanci zargin laifukan cin hanci da rashawa har guda 800 wadanda aka jingine tun a shekara ta 2009.
Zargin wanda ya shafi miliyoyin kudade wajen sayen makamai, mai shigar da kara ya jingine su ne domin baiwa shugaba Jacob Zuma damar tsayawa takarar shugabancin kasar a wancan lokaci, saidai a yanzu alkalin kotu dake Pretoria, Aubrey Ledwaba ya bayyana cewa sun jingine karar a wancan lokaci amma yanzu ya dace a sake duba batun…………………………
To daga Afirka ta kudu bari mun kasar Kenya, inda shugaban kasar Uhuru Kenyatta, ya bukaci kasashen duniya da su kawo karshen cinikin hauren giwa da ake yi daga Afirka zuwa yankin Asiya, wanda hakan ke barazana ga makomar giwaye a duniya.
Uhuru Kenyatta wanda ke jawabi a wani taron shugabannin kasashe da kuma kungiyoyin kare gandun daji, ya ce " matukar dai muka rasa giwayen da muke da su a Afrika, to hakan na a matsayin rasa abinda muka gada ne.
Kan wannan batun ne kuma na tuntubi Laftana Mahadi na ma'aikatar gandun Daji ta garin Dakoro dake a jihar Maradi jamhuriya Nijar, da farko kum ya bayyana muna matsayin da giwa take da shi.
…………………………… 03……………………….
To a Equatorial Guinea kuma hukumar Zaben kasar ce ta bayyana shugaba Teodoro Obiang Nguema a matasyin wanda ya lashe zaben kasar da kashi 93 na kuri’un da aka kada.
Sakamakon ya nuna cewar abokan takarar sa Bona-ventura Monsuy Asumu da Avelino Mocache sun samu kashi daya da rabi kowannen su.
Wannan nasara zata baiwa shugaban da ya fi dadewa a karagar mulki a Nahiyar Afrika damar kara wasu shekaru kan 36 da yayi yanzu haka.
………………………………
To yanzu sai kamaru inda a wannan mako ne hukumar kuda da muhali ta MDD ta gudanar da wani taro a birnin Yaoude kan yadda za'a zabura da kasashen Afirka wajen tsarin gine-gine na zamani ta yadda za'a samu walwale a tsakanin jama'a
Daga birnin na Yaoude ga rahoto da wakilin mu Wada Alhaji ya aiko muna
………………………….04………………….
To yanzu bari mu sake kowama Najeriya kan zanga-zanga da wasu matasan kasar sukayi a harabar majalisar datijan kasar, suna masu korafi kan batun sayan motocin alfarma ga 'yan majalisar ….
To ko yayi zafi ? ga abunda wasu daga cikin matasan ke cewa
…………………………
To Saidai da yake maida martani kan zanga-zanga, Sanata Mahamadu Ali Ndume shugaban masu rinjaye a majalisar datijan, cewa yayi …..
………………………..
To yanzu sai Burundi inda gwmanatin kasar ta ce, ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiyar kasar ba sai an shaida ma ta wadanda za su halarci taron.
Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar, Willy Nyamitwe ya ce dole sai an basu damar amincewa da wadanda zasu halarci taron a lokacin gudanar da shi da kuma inda za a yi taron.
Tsohon shugaban kasar Tanzania Benjamin Mkapa da ke jagorancin shirya taron ya ce, za a gudanar da tattaunar ne tsakanin ranakun 2 zuwa 6 ga watan Mayu a birnin Arusha.
……………………….
To bari mu karkare shirin daga Jamhuriya Nijar inda a cikin makon ne gungun wasu kungiyoyin fara hula suka bukaci al'umma kasar da kowa ya zauna gida, a wani mataki na kalubalantar salon mulkin kasar .
kafin hakan dai kungiyoyin sun so gudanar da zanga-zanga a Yamai babban birnin kasar saidai mahukuntan kasar suka haramta masu yin hakan, lamarin da yaya suka bullo da wannan salo na bukatar kowa ya zauna a gida.
Mal……… na daya daga cikin jagoran gamayar kungiyoyin, kuma daga nan birnin Tehran Awwal Kunya ya tuntube shi ga kuma abunda yake cewa…
…………………….05…………………
To jama'a masu saurare ganin lokacin da muke da shi ya kawo jiki, a nan cilas zan ja birki a shirin na yau, sai kuma mako na gaba idan Allah ya kai.
Yanzu amadadin dukkan wadanda suka taimaka shirin ya kamala musamman Mohd Amin Ibrahim, daya hada muna sautin shirin, ni Hassan barka dana shirya na kuma gabatar ke yi muku fatan Alkhairi, daga nan birnin Tehran…..

Tags