May 21, 2016 03:13 UTC
  • Siffofin Sanin Allah ta hanyar ilhami ko fitira

tambayarmu ta yau ita ce wasu siffofi ne sanin Allah ta hanyar ilhami ko kuma fitarar Dan Adam yake banta da su


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan hanyoyin sanin Allah madaukakin sarki, domin nasossi da dama sun bayyana mana hanyoyi da dama, daga cikin a kwai hanyar dabi’ar Dan Adam wato dabi’ar da Allah madaukakin sarki ya halicce shi, ko kuma na ta hanyar ilhami ,tambayarmu ta yau ita ce wasu siffofi ne sanin Allah ta hanyar ilhami ko kuma fitarar Dan Adam yake banta da su? Kafin amsa wannan tamabaya bari mu saurari tanayin da aka yi mana a kan faifai


*************************Musuc*********************


Masu saurare, daga cikin mahiman siffofin da wannan sani yake banta da su shine Dan Adan zai ji a cikin wujidinsa lutfi da tausayin da Allah  madaukakin sarki yayi masa na cewa lallai shine mahalicinsa sannan ya gode masa madaukakin sarki, wannan shine abinda shugabanmu, shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yake ishara da shi a cikin daya daga cikin khudubobinsa da aka ruwaito cikin littafin Nahjul Balaga inda yake cewa:(godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yiwa bayinsa ilhami na gode masa , kuma ya halicce su bisa sanin cewa shine ya halicci halittu) a wani hadisi na daban kuma shugaban muwahidai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya rarrabe mana sifoffin da wani sani na fitra ko kuma wanda Allah madaukakin ya halarci Dan Adam da shi yake banta da su,daga cikinsu shine sani na ilhami ya kan sanya mutune ya so Allah ya kuma gode masa, a cikin Littafin Attauhid na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) shi kuma daga ma’aifinsa Imam Zainul Abidin (a.s) shi kuma daga kakansa Imam Husain (a.s) ya ce wani Mutune ya tashi tsaye wajen Imam Ali (a.s) ya ce masa ya shugaban mumunai ta yaya ka san mahalicinka?sai Imam Ali (a.s) ya amsa masa da cewa yayin da na yunkura na yi azama tare da himmatuwa  wajen aikata wani abu , sai hakan bai yuyu ba,a lokacin na fahimci cewa a kwai mai tsara mani da kuma tsarawa kowa da kowa abubuwa kuma wannan shine Allah madaukakin sarki ), da wannan masu saurare, Mutune zai ji cewa tsarin Allah madaukakin sarki da kuma kada’insa ya sabawa so da kuma abinda Bawa ya baiwa mahimanci, sai Mutune ya bukaci wani abu a wajen ubangiji, Allah madaukakin sarki ya canza masa da abinda ya fi zama maslaha a gareshi da kuma abinda zai kiyaye shi, ya kuma kare shi da abinda yake maras kwau a gareshi saboda shi Dan Adam bai san karshen al’amaru ba ,kuma wannan shi jawabin amsar da ta gabata, a ci gaban hadisin, mutuman nan ya sake tambayar Imam Ali(a.s) ya ce Ya Amiru mumunin a kan mine ya sanya ga godewa ni’imominsa? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa wani bala’I ya tunkare ni, sai ya kawar min da shi sannan ya jarrabe da wani abu, sai na fahimci cewa lallai yayi ni’ima a gare ni, sai na gode masa, bayan haka sai matambayi ya koma kan tasirin soyayyar Allah madaukakin sarki a cikin wujudin bayinsa sannan ya ce Ya Shugaban mumunai minene ya sanya kake son haduwa da shi ?wato Ubangiji, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa a yayin da naga ya zaba mani addinin Mala’ikansa, ma’aikansa da Annabawansa tsarkaka, sai na fahimci cewa wanda ya karrama ni da wannan, ba zai mantani ba, don haka na bukaci haduwa da shi).masu saurare, wannan hadisi mai albarka yayi ishara kan yadda Imam Ali(a.s) yake shiryar da mu wajen yin tunani mai kyau game da irin karamcin da Allah madaukakin sarki yayi mana, ko wani dan Adam yayi tunani a kan kan sa domin ta hanyar tunani mai kyau ne mutune yake fahimtar kansa sannan ya kai zuwa ga martabar dan Adamtaka har ya kai ga samu tabbaci da yakini , kuma wannan shine koyarwar musulinci da shugabanin musulmi .


**************************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa , a ci gaban shirin ka wani hadisi da yake ishara ga hadisin da ya gabat wanda maluman Ahlusunna da dama suka ruwiato a cikin sharhin Littafin Ihkakul Haq zuji’I na tara wanda yake hikayar wani saurari daga cikin hadiman shugaban masu Kadaita Allah Aliyu bn Abi talib (a.s), a cikin wannan littafi an ruwaito hadisi daga Abu Na’im da Ibn bishkuwal daga sufyanu Sauri ya ce: yayin da nake aikin Hajji wani matashi ya shigo waje na, ba ya dauke kafarsa yaa kuma dorata a kasa face yayiwa Annabi Muhamad da iyalan gidansa tsarkaka salati ba, ya na cewa اللهم صل علی محمد وآل محمد،, sai nace masa cikin sani kake fadar wannan ? sai ya ce Na’am sannan ya ce da ni wanene kai sai nace masa nine Sufyanu Sauri, sai yace da ni shin kasan Allah? Sai na ce masa Na’am, yace min ta wata hanya kan san Allah madaukakin sarki? sai na fara bayyana masa tasiri da halitun Allah madaukakin sarki, sai wannan matashin ya amsa masa da kalman Amirun mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) kan sanin wujudi ko kuma na fitra da ilhami da kuma irin siffofin da suka kebenta da su, sai Sufyanu sauri ya ce na san Allah ta hanyar cewa shi ne Mai shigar da dare a cikin Rana, Mai kuma shigar da rana a cikin Dare kuma shine Mai suranta Da a cikin Ma’aifa, sai Matashin nan yace da ni Ya Sufyan hakika ba ka san Allah hakikanin sani ba, sai Sufyan ya tambayeshi kai ta yaya kasan shi? Sai yace da ni  yayin da na yunkura na yi azama tare himmatuwa  wajen aikata wani abu , sai hakan bai yuyu ba, a lokacin na fahimci cewa a kwai mai tsara mani da kuma tsarawa kowa da kowa abubuwa kuma wannan shine Allah madaukakin sarki , sai sufyan ya ci gaba da tambayarsa kan salatin da yake yiwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sai wannan samari ya ce na kasance ina aikin hajji tare da ma’aifiyata, ta bukace ni in shigar da ita cikin dakin Allah  sai na shigar da Ita,ina tsaya a kanta tana fama da ciwon ciki ga kuma fuskarta tayi baki,na kasance a wannan lokaci cikin damuwa da bacin rai, sai na daga hannuwana sama na ce ya ubangiji haka ka ke yiwa wanda ya ziyarci dadinka, sai na ga wani abu kamar gajimare yay aye, sai wani mutune sanya da fararen tufafi  ya shigo cikin Dakin Allah, ya shafi kanta sai fuskarta ta yi fari sannan ciwon da take fama da shi na ciki ya kawar ma’ana ta samu lafiya daga cutar da take fama da ita,sai ya juwa zai futa, sai na rige rigarsa sannan na tambayesa, na ce wanene kai da kayi sanadiyar  yaye mana damuwar da muke fama da ita? Sai yace da ni nine Annabinka Muhamad, sai na ce ya Ma’aikin Allah ka yi masi wasici da wani abu,sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce da ni idan ka daga kafarka kadda ka ajiyeta face kayiwa Annabi da iyalan gidansa salati ba, اللهم صل علی محمد وآل محمد،


Masu saurare, mahiman sifofin da suka kebantu da sanin Allah na ilhami ko fitra shine wannan sani shike sanya soyayya  mai karfi tsakanin Bawa da mahalicinsa, bawa ya fahimci irin karamcin da Allah madaukakin sarki ya yi masa kuma ya gode masa a kan hakan, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon gode masa don darajar shugaban halittu da iyalan gidansa tsarkaka.


***********************Musuc***********************


Masu saurare a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala , ni da na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu