May 21, 2016 03:17 UTC
  • Babbancin Sanin Allah ta Fitra Da Halittu

Tambayar mu ta yau minene ke banbanta saninsa madaukakin sarki daga wannan hanya da kuma saninsa daga wani sashen halittunsa


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, tambayarmu ta yau ita ce wasu mahiman siffofi ne suka kebanta ga sanin Allah madaukakin sarki wacce Mutune zai cimmawa ta hanyar sanin kai, a shirin da ya gabata mun bayyana daya daga cikin mahiman hanyoyi na sanin Allah madaukakin sarki ubangijinmu,mai tsarawa mana rayuwa,shine mai arzutawa,kuma shine mai rayawa da sauren soffofinsa kyawawa, Tambayar mu ta yau minene ke banbanta saninsa madaukakin sarki daga wannan hanya da kuma saninsa daga wani sashen halittunsa?kafin shiga cikin shirin gadan-gadan bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.


**************************Musuc***************************


Masu saurare, idan muka kan ayoyi alkur’ani masu albarka za mu fahimci cewa Allah madaukakin sarki ya karrama bani-adama bayan ya haliccesa cikin kyakkyawar halitta,sannan ya sanya shi khalifansa a doron kasa kuma shugaban halittunsa, a cikin Suratu Isra’I Aya ta 70, Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa(Hakika Mun girmama ‘ya’yan Adam, Muka kuma dauke su(kan ababen hawa) na sarari da na ruwa muka kuma Arzuta su daga tsarkakan (abubuwa) kuma fifita su a kan wasu da yawa daga abin da muka halita nesa ba kusa ba) har ila yau a cikin wannan sura mai albarka Aya ta 61da kuma ta 62,Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da Mala’iku:”ku  yi sujada ga Adam, sai suka yi sujjadar in ban da Iblis da ya ce “Yanzu na yi sujjada ga wand aka halitta daga Tabo* Ya ce: “ka gane fa, wannan da ka fifita shi a kaina, wallahi idan ka jinkira min har zuwa ranar Alkiyama to lallai zan batar da su da zuriyar sa, saidai kadan (daga cikinsu)) a cikin suratu Daha  Aya ta 41,Allah madaukakin sarki ya ce Annabi Musa (a.s):(kuma na zabe ka don kaina),a cikin suratu Tini Aya ta 4 Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika mun halici mutun cikin kyakkyawan darin (halitta)) a cikin Suratu Sad Aya ta 26, Allah madaukakin sarki ya bayyana ceewa:(Ya Dawuda, Hakika Mun sanya ka kalifa a cikin kasa,sai ka yi hukunci a tsakanin mutane da gaskiya…)


Masu saurare, abin fahimta a wadannan Ayoyi da ma makamantansu, shine Allah madaukakin sarki ya halicci mutune a kan mafi kamalar surar halittu , kuma ya martaba shi da mafi girman martaba, sannan ya umarci mala’iku suyi masa sujjada, ya kasance halifan Allah madaukakin sarki a doron kasa, mai iko wajen gudanar da hukunci a tsakanin Mutane da gaskiya,mafi girmar kauta da kuma mafi kamala da Allah madaukakin sarki ya horewa mutune bisa sauren halittu ita ce hankali, domin haka duk wanda ya fahimci girman Allah da kuma siffofinsa masu madaukaka,shi zai fi saukin cimma sanin Allah daga sauren halittu, Allama faidu kashani, ya nakalto wasu shahararun Abyat  a cikin Tafsirinsa mai suna Tafsiru Safi , a farkon tafsirin Suratu Bakarat daga shugaban mumunai Ali bn Abi Talib (a.s) da suke bayyani kan kishin dan Adam ya ce warakarka a cikinka alhali b aka shu’urin hakan, kuma warakarka na gareka amma b aka gani , kuma kaine Littafi bayananai wanda da harufansa ka ke bayyana, shin kuma kana tunanin kai karamin  laifi ne, alhali daga kaine babbar Duniya ta bayyana.a cikin Tafsirin Safi, sheikh faidu kashani ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya ce:(halitar Mutune ita ce babbar Hujjar Allah a kan bayinsa kuma shine Littafin da Allah madaukakin sarki ya rubuta shi da hanunsa) kuma wannan hadisi shine hakim Sabzawari ya nakalto a cikin juzi’I na farko na sharhin Adu’ar jaushunar Kabir wanda aka fi sani da sharhin Asma’ul husna.


***************************Musuc****************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin, babban malamin hadisin nan ibn Abi jamhur Al’ihsani ya nakalto cikekken hadisin daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:( halitar Mutune ita ce babbar Hujjar Allah a kan bayinsa kuma shine Littafin da Allah madaukakin sarki ya rubuta shi da hanunsa, kuma ita ce ginin da Allah madaukakin sarki ya gina da hikimarsa, kuma ita ce dukkanin surar talikai,kuma ita ce takaiceccen lauhil mahfuz, kuma ita ce abin ganin duk wanda ba ya nan,kuma ita ce hujar ko wani mai jayayya,kuma madaidaiciyar hanya ga duk wani alheri)


Masu saurare, abin fahimta a wannan hadisi na shugaban iyalan gidan ma’aikin Allah, za mu fahimci cewa hakika Allah madaukakin sarki ya sanya asarin karfi da kuma kuzari na dukkanin mahlukai cikin fitirar dan Adam a takaice, domin haka ne sanin mutune na wannan karfi da kuzari zai budewa mutune sanin kansa da mahalicinsa madaukakin sarki wanda ya busa ruhunsa mai tsarki a cikin mutune ya kuma zama Mutune kamar yadda Alkur’ani mai tsarki ya saraha.


Da wannan za mu fahimci cewa kebabbun sifoffin da suka siffanta na sanin Allah madaukakin sarki ta hanyar sanin kai, ita ce mafi girma ,daraja da kuma martaba na wujdanin sanin Allah madaukakin sarki ga Dan Adam, domin haka ne sanin Allah madaukakin sarki ta hanyar waliyansa da kuma zababbu makusanta ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ita ce mafi girma da kamala na sanin Allah madaukakain sarki.domin su amincin Allah ya tabbata a garesu sune cikekkiyar kamala taMutune wanda shine khalifar Allah a doron kasa, kuma wannan shine karfi da kuzarin da Allah madaukakin sarki ya tabbatar a halittar mutune , da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya mu fahimci hakikanin sanin kai domin sanin Allah madaukakin sarki.


****************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.