Sanin Allah ta hanyar Tunani
Tambayarmu ta yau ita ce ta yaya za mu san Allah madaukakin sarki ta hanyar tunani ga abinda ke tsakaninmu na halittu?
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, tambayarmu ta yau ita ce ta yaya za mu san Allah madaukakin sarki ta hanyar tunani ga abinda ke tsakaninmu na halittu? Ma’anar hakan shine Ayoyi da kuma hadisai da dama sun umarcemu da yin tunani ga halitun Allah madaukakin sarki a matsayin hanyar Sanin Allah, ta yaya hakan zai tabattu a garemu?kafin amsa wannan tambaya ga wannan.
***********************Musuc*****************************
Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba , zai fara da Littafin Allah mai girma, a cikin suratu Bakara Aya ta 164, Allah madaukakin sarki ya ce:(hakika a cikin halittar sammai da kassai da sassabawar dare da rana da jiragen da suke yawo a teku(suna tafe)da abin da yake amfanar mutane da kuma abin da Allah ya saukar daga Sama na Ruwa, ya raya kasa da shi bayan mutuwarta, ya kuma baza dukkanin dabbobi a cikin ta,da sarrafa iskoki da gizagizan da aka hore (sun tsaya) tsakanin Sama da Kasa.lallai(wadannan abubuwa) ayoyi ne ga mutane masu hankali) a cikin suratu Ali imrana Aya ta 190 da kuma ta 191 Allah madaukakin sarki ya ce (hakika a cikin halittar Sammai da kassai da sabawar Dare da Rana, lallai akwai ayoyi ga ma’abuta hankula*(su ne) wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma kishingide, suke kuma tunani a kan halittar sammai da Kassai (suna cewa) “Ya Ubangijinmu , b aka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata a gare ka,ka tserar da mu azabar wuta) har ila yau a cikin suratu kaf Aya ta 6 zuwa ta 8, Allahou tabaraka wa ta’ala ya ce:(Yanzu bas a duban sama da bisansu kaka muka ginata Muka kuma kawata ta ba ta kuma da wasu hudoji (tsage-tsage)* Da kuma kasa (irin yadda) muka shimfida ta da Muka kuma sanya duwatsu turaku a cikinta, Muka kuma tsirar da duk wani iri,mai kyau a cikinta.*Aya ce (abar lura) da kuma gargadi ga duk wani Bawa mai komawa ga Allah). Masu saurare, bayan wadannan Ayoyi masu albarka, akwai ayoyi da dama da suke bayyani da kuma amsa tambayar da ta gabata bisa asasi guda biyu, na farko amfani da ni’imar hankali kan abinda muke gani da idanunmu kan yadda aka tsara halittu daga cikin ayoyin da suke bayyana dalilin cewa a kwai asalin samuwa ga ya halice ta wato shine Allah madaukakin sarki, na biyu kuwa sanin cewa wanda ya halicci wannan halitta mai kyau na da ikon shaida a kanta wajen bayyana halitarta, amma abin muka fahimta a cikin fadar Allah madaukakin sarki(Aya ce (abar lura) da kuma gargadi ga duk wani Bawa mai komawa ga Allah) suratu kaf Aya ta 8 shine yin dogaro da abinda yake na zahiri da Allah madaukakin sarki ya horewa bayinsa a cikin fitirar su domin cimma hakikanin sanin Allah ta hanyar tunani ga kuduransa na zahiri tabaraka wa ta’ala.
***********************Musuc*******************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai koma bangaren nauyi na biyu domin amsar wannan tambaya, hakika hadisai da dama na iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka sun yi bayyani kan yadda za a cimma sahihin sanin ubangiji ta hanyar tunani ga halitarsa da kuma komawa zuwa ga sahihiyar fitira domin tabbatar da sakamako mai kyau.a cikin littafin Nahjul-balaga, shugaban masu kasdaita Allah,Aliyu bn abi talib (a.s) ya ce (daga halitar Allah ake gabatar da dalili a kansa, da kuma hankula ake fahimtar saninsa ,da kuma tunani ake tabbatar da hujjarsa)har ila yau Imam (a.s) ya ce (godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yi tajalli ga halitunsa ta hanyar halitarsa, ya bayyana ga hankula kan ababen da suka gani na alamomin hakikanin tsarinsa da kuma abinda ya kaddara na hukuncinsa.har ila yau a cikin wata riwayar Imam Ali(a.s) ya ce (ya bayyana cikin hankula bisa abinda suke gani cikin halittarka na alamomin tadbirinka,babu wani kokari da hankulan masu tunani za su iya dangane da milkinka domin duk wanda ya kyago samai da kasai da abinda ke tsakaninsu da na cikinsu kuma shine yake ra su babu wanda zai iya kalubalantar kudurarsa.
A cikin wata khudubarsa ta daban,Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) yayin da yake bayyana girmar Allah madaukakin sarki:ya kuma goda wa milkin kudurarsa da abubuwan mamaki da suka bayyanai daga hikimarsa da kuma tabbacin hujarsa ga halittu har zuwa da ya tsayar da ita da rikon karfinsa, abinda ya shiryar da mu,na tsayar da hujja a kansa bisa saninsa sai alamomin milkinsa ,halitarsa da kuma hikimarsa suka bayyana, har ila yau Imam (a.s) ya ci gaba da cewa duk abinda ya halitta da kuma dalilansa suka zamanto hujja a gare shi, kuma wanda ya kasance ma’abocin shuru, to hujjarsa shine tsarin da ya yi na yadda zai firta magana daga cikin bakinsa ta yadda ya tsarawa kansa tun daga farko.a wani bangare na Khudubarsa kuma ya ce ya kuma tsaida shaidun hujjojinsa a bisa lutifin halitarsa da kuma girmar kudirarsa ga abinda hankula suka gano na saninsa kuma ta sallama a kan hakan, sannan kuma ta tabbatar da sunayansa kyawawa a matsayin cikekkiyar hujja a kan cewa shi daya ne da babu na biyunsa. Har ila yau Imam Ali (a.s) a cikin wata khudubarsa ya ce daukaka ga mamallaki wanda ya fi karfin a siffanta shi da ma’auni ko kuma a cimmasa da kuma a daidaita shi da Mutane, hanyar kuma saninsa,halitunsa da suka yi fice ga hankula, wannan dalili ne ga masu zurfin tunani.
Masu saurare, hakika,abinda iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka suka bari na ilimi shi ke tabbatar da cewa sanin Allah madaukakin sarki ta hanyar halitunsa na da mahimancin gaske kuma hakan shike shiryar da Mutane hakikanin hanyar sanin Allah madaukakin sarki kamar yadda aka ruwaito cikin khudubobin Imam Ali (a.s) cikin littafin Nahjul-Balaga, daga cikin misalan hakan a kwai khuduba jami’a da aka ruwaito cikin Littafin Attauhid wanda Imam Sadik (a.s) ya fadawa Mufadal bn Amru shi kuma ya rubuta.haka zalika wasikar da ya rubuta masa wacce aka fi sani da wasikar Al-ahlilaja dukkaninsu suna kumshe da fa’idodi da dama na sannin Allah madaukakin sarki, domin haka ne ma babban malamin ne arifi Sayyid bn Tawus cikin littafinsa Kashful-Gumma ya yiwa dansa da mumunai baki daya wasicin karanta shi domin sanin Allah ta hanyar ayoyinsa da kuma halitunsa.
************************Musuc***************************
Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.