May 21, 2016 03:22 UTC
  • Hanya Mafi Kamala Da fifiko ta Sanin Allah

Tambayarmu ta yau ita ce wace hanya ce mafi kamala da fifiko na sanin Allah hakikanin sani?


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, tambayarmu ta yau ita ce wace hanya ce mafi kamala da fifiko na sanin Allah hakikanin sani? Wannan tambaya na da mahimancin gaske, domin a shirin da ya gabata Ayoyi da daman a cikin Alkur’ani mai tsarki gami da hadisan ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka sun shiryar da mu hanyoyi da dama na sanin Allah hakikanin Sani wanda hakan kuma shine asalin Usuluddin na gaskiya da ta hanyarsa mutune zai samu tsira da sa’ada a rayuwar duniya da Lahira, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, a shirin da ya gabata , da farko mun bayyana cewa komawa zuwa ga fitira ko kuma ilimin da Allah madaukakin sarki ya sanyawa Dan Adam tun daga halittarsa da kuma taskokin sani gami da alakar dake tsakanin Bawa da Allah madaukakin sarki, sai kuma na biyu yin tunani ga halittun Allah da kuma girmansa gami da girman tsarin sa, girmar halittarsa madaukakin sarki na daga cikin hanyoyin sanin Allah hakikanin Sani,sannan sanin Allah ta hanyar mafi kamalar hanya, wacce ita ce mutune da Allah tabaraka wa ta’ala ya karramashi kuma ya zabe shi a matsayin khalifa ko kuma mataimakinsa a doron kasa, shin wannan ita ce hanya mafi girma da kuma fifiko na sanin Allah hakikanin Sani? Masu saurare, hadisai da dama masu inganci sun bayyana cewa mafi kamalar hanyoyi na sanin Allah hakikanin Sani shine sanin zababbun Allah daga cikin halitunsa Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma da iyalan gidansa tsakaka baki dayansu, har ma hadisan sun bayyana cewa sanin Allah hakikanin Sani ba zai cika ba , ba tare da saninsu ba,(amincin Allah ya tabbata a garesu), a cikin littafin Kifayatul Asar fi A’imatil Isna Ashara, Hafiz Kharaz ya ruwaito wani hadisi mai tsaho  daga Ma’aikin Allah (S.a.w) inda a cikin sa yake cewa :(Ya Ali kai ne shugaba kuma khalifa bayana, yakarka kamar yaka na ne, zama lafiya da kai kamar zaman lafiya da ni ne, daga zuriyarka ne shugabanin shiriya m’asumai, kuma ba don mu ba da Allah bai halicci wuta da Aljanna ba, da kuma ba a halicci Annabawa da mala’iku ba,Ya Ali mu ne mafi alherin khalifofin Allah  bisa shufudar kasa, kuma mune  mafi alkheri daga Mala’iku makusanta, ta yaya ba za mu kasance mafi alheri da su ba, alheri mun gabace su sanin Allah da kuma kadaita shi, ta hanyarmu ce aka san Allah kuma ake bauta masa, ta hanyarmu ce kuma suka shiryu zuwa hanyar sanin Allah).har ila yau masu saurare makamantan  wannan hadisi ya zo cikin riwayoyi da dama masu inganci da suke ishara zuwa gabatuwar Annabi Muhamad da iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a garesu wajen sanin Allah  da kuma kadaita shi a kan dukan  halittu tun kafin wannan Duniya kamar Duniyar haske da kuma ta Zarra,shekh Saduk yardar Allah ta tabbata a gareshi ya yi bayyani kalkashin wannan hadisi dake  cewa ma’anar  haka kuwa shine in ba don su ba a matsayin hujjojin Allah a doron kasa ba, mutane ba za su san Allah hakikanin sani ba, haka zalika ba don Allah madaukakin sarki ba da ba a son su ba  a matsayin hujjojin Allah ba.


***********************Musuc***************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,a cikin littafin da ya gabata an ruwaito wani hadisi na daban , inda a cikinsa, Imam Ali Alhadi (a.s)  yake cewa duk wanda bai san su ba (amncin Allah ya tabbata a garesu) bai san Allah hakikanin Sani ba,) kamar yadda ya zo cikin littafin Masharikul Anwaril Yakin na Hafiz Rajab Albarsi.masu saurare , a cikin Tafsiru NuruSakalain da waninsa daga cikin Tafsirain  Riwaya an ruwaito hadisi daga Jabir, inda ya ce wani Mutune ya tambayi Imam Bakir (a.s) kan fadar Allah madaukakin sarki (Ya Kuma cika muku Ni’imominsa na sarari da na boye )suratu Lukman Aya ta 20 sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa ni’imar sarari shine Ma’aikin Allah da kuma iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a garesu da kuma abinda ya zo na sanin Allah da kuma kadaita shi,amma ni’imar na boye wulayarmu ko kuma biyayya a garemu mu iyalan gidan ma’aikin Allah da kuma kula soyayarmu, ku kula wannan  ita ce ma’anar ni’imar Allah ta zahiri da ta boye, domin wasu Mutane sun kula wannan  ni’imar ta sarari , suka ki kula kuma ta boyen sai Allah madaukakin sarki ya saukar da wannan Aya ( Ya Kai wannan Manzo, kada wadanda suke gaggawa cikin kafirci su bakanta maka rai,su ne wadanda suka ce:Mun ba da gaskiya da bakinsu (amma) zukatansu ba su ba da gaskiya ba..)suratu Ma’ida Aya ta 41sannan sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa bayan saukar wannan Aya Sai Ma’aikin Allah (s.a.w) yay i farin ciki da cewa Allah tabaraka wa ta’ala ba zai karbi imaninsu ba matukar ba sun kulla biyayyarmu da kuma soyayyarmu , mu iyalan gidan ma’aikin Allah ba, wannan shine ma’anar sanin Allah da kuma kadaita shi .a cikin Littafin Ma’anil Akhbar, shekh Saduk ya ruwaito wani hadisi daga Mufadal bn Amru ya ce:(an tambayi baban Abdallah Imam Sadik (a.s) kan ma’anar Siradi sai ya ce siradi shine  hanyar sanin Allah madaukakin sarki, domin siradi hanyoyi guda biyu, hanyar duniya da kuma hanyar lahira,amma hanyar ta duniya ita ce shugaba wanda aka wajabta yin biyayya a gare shi, wanda ya san shi a duniya kuma ya yi koyi da shiriyarsa zai fice ta kan wannan hanya wato ita ce gadar da ta saman  wutar jahannama a Lahira, duk kuwa wanda bai san haka ba a nan duniya zai kasa ficewa ta kan  wannan siradi, ya fada cikin wutar Jahannama)


Masu saurare irin wadannan hadisai da makamantansu nada yawan gaske da ya fice hadin tawaturi, kuma wannan shi ke kara bayyanar fiyeyar kamala na hanyoyin sanin Allah madaukakin sarki domin zababbun Allah daga cikin talikai sune Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma da iyalan gidansa tsarkaka sune tabbaci da misdakin mutune kamili kuma khalifar ubangiji a doron kasa, daga cikinsu ne dabi’un Allah suka bayyana , domin haka ne ma suka kasance madubin Sanin Allah hakikanin Sani.da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon saninsu da kuma yin koyi da biyayya kan abinda suka sanar da mu.


************************Musuc***************************


Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.