Siffofin Sanin Allah Ta Hanyar Annabi
Tambayarmu ta yau ita ce wasu siffofi ne suka kebanta na sanin Allah ta hanyar Annabi Muhamad tare da iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a garesu?
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, tambayarmu ta yau ita ce wasu siffofi ne suka kebanta na sanin Allah ta hanyar Annabi Muhamad tare da iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a garesu?hakika a makun da ya gabata, mun yi bayyani kan hanya mafi kamala da cika ta sanin Allah madaukakin Sarki hakikanin sani, minene zai banbanta shirin na yau da wanda ya gabata?zai kasance karin bayyani ne ga shirin da ya gabata ko kuma zai kasance ya fishi ne? sai a biyo mu sanu a hankali domin jin amsar wannan tambaya.
******************************Musuc****************************
Masu saurare, hadisai da dama sun bayyana cewa muhiman siffofin da suka kebanta na sanin Allah madaukakin sarki hakikanin sani ta hanyar zababbun Allah Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka shine wannan sani cikekkiyar hanyar cimmawa Ibada khalisa da tauhidin Allah madaukakin sarki cikin martabarsa da kamala.a cikin Littafin Ilalu shara’I’I, shekh Saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s)ya ce(wata rana Imam Husain Dan Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya fita wajen sahabansa sai ya ce musu hakika Allah madaukakin sarki bai halarci bayi ba sai don su sanci , idan kuma suka sanci sais u bauta masa , idan kuma suka bauta masu sun wadatu daga bautar waninsa, imam Sadik (a.s) ya ce sai wani mutune ya tashi ya ce Ya Dan Ma’aikin Allah yaya ne sanin Allah?Imam Husain (a.s) ya ce sanin mutanan ko wani zamani shugabansu da ya wajabta a yi masa da’a da biyayya) ,a cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir(a.s)ya ce :(duk wanda bai san Allah ba kuma bai san shugaba daga cikinmu mu iyalan gidan Ma’aikin Allah ba,to hakika ya san cewa yana bauta wanin Allah ne). a cikin Littafin Kurbul Isnad, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ridha ,daga Imam Bakir (a.s)ya ce:(duk wanda ke son kada ya kasance tsakaninsa da Allah hijabi ko shamaki har sai ya ga Allah, kuma Allah ya gansa to yayi biyayya ga Iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka ya kuma kauracewa makiyansu, kuma ya cika biyayarsa da shugaba daga cikinsu, idan ya kasance hakan, Allah zai gansa kuma shima zai ga Allah) masu saurare a bayyane yake abinda ake nufi da ganin Allah a wannan hadisi ne ishara na ganin zuci ba ganin idanu ba, Allah madaukakin sarki ya daukaka da hakan,kuma ba boye yake ga kowa ba wannan gani na zuci na daga cikin mafi daukakar sanin Allah madaukakin sarki hakikanin sani, kuma wannan sani shike yiwa mutune jagora zuwa mafi girman martaba na Ibadar Allah madaukakin sarki, a cikin Suratu A’arafi Aya ta 180 Allah madaukakin sarki ya ce:(Allah kuma yana da sunaye kyawawa,saboda haka ku roke Shi da su,kuma ku rabu da wadanda suke fandarewa game da sunayansa da sannu za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa) hakika maluman tafsiri sun bayyana cewa sunayan Allah kyawawa sune wadanda suke sanar da halittu,mahalicinsu tabaraka wa ta’ala kuma kalkasa shi kashi-kashi kamar su mai ji, mai tausayi, mai gani, mai jin kai da makamantansu.kuma dukkanin wadannan sunaye halittu ne, ya sanya su da kuma kyautata su wajen muhimmancin sanar da zababbunsa daga cikin halittu gaba daya Muhamad da iyalan gidansa amincin Allah su tabbata a gareshi.
**************************Musuc********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,a cikin littafin Kafi da Tafsiru Ayyashi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) yayin da yake fassara wannan Aya mai Albarka: :(Allah kuma yana da sunaye kyawawa,saboda haka ku roke Shi da su,kuma ku rabu da wadanda suke fandarewa game da sunayansa da sannu za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa) suratu A’arafi Aya ta 80, imam (a.s) ya ce:(mune wallahi sunayen Allah kyawawa, da Allah bay a karbar Aiki daga bayansa saida saninmu). Babban Arifin nan Ayatullahi Khumaini cikin muhadararsa ko kuma mu ce a yayin da yake bada ilimi darasi na tafsirin Ayar Basmala wacce tanada dangantaka da wannan hadisi ya ce isin ko suna ma’anarsa Alama, kuma yanada martabobi,a kwai sunan da yake wakiltar dukkanin alama(ma’ana na sanin Allah) kuma hakika ya yazo cikin hadisi cewa (mune sunayen Allah kyawawa) sunan da yake mafi girma a matsayin bayyanar (ubangiji) shine samuwar Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma da iyalan gidansa tsarkaka, domin sune suka sadar daga martabar tafiya zuwa ta karshe)
Masu saurare, bisa hasken da muka fahimta na hadisan da suka gabata,ya bayyana cewa Ahlulbait (a.s) sune mafi girman martaba da sunayen Allah kyawawa da Allah madaukakin sarki ya umarce mu kira shi da su, ta hanyarsu ne ,ma’ana kasancewar saninsu ta wannan hanya ibadar da ake bukata ta Allah madaukakin sarki za a cimmawa.kuma wannan shine abinda za mu fahimta cikin wani bangare da Addu’ar da shugaban muwahidai kuma shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya koyawa salihin sahabinsa Nawif Bukali yardar Allah ta tabbata a gareshi, ita dai wannan addu’a tana ishara kan sanin Ahlulbait amincin Allah ya tabbata a garesu da sune bayin Allah da waliyansa na musaman ta hanyarsu da a fahimci hakikanin gaskiyar imani da ibada, Imam Ali (a.s):( Ya Ubangijina ina kuma tambayarka sunanka da ka bayyana shi ga kebebun waliyanka da suka kadaitaka suka kuma sananka sannan suka bauta maka hakikanin bauta, da ka sanar da ni kanka domin in tabbatar maka da rububiyarka bisa hakikanin imani da kai, kada kuma ka sanya ni ya Ubangijina ga wanda yake bautar sun aba tare da ma’anarsa ba,ka wadatani ko da da sakan guda ka haskaka zuciyata da saninka na musaman da kuma sanin waliyanka, hakika kai mai iko ne a bisa dukkanin komai)
Masu saurare da fatan Allah madaukakin sarki ya arzutamu da gaskiyar Imani da Allah, tabbatar da rububiyarsa, bautarsa da kuma kadaita shi, domin albarkar sani, biyayya da kuma soyayar kebabun waliyanka Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a garshi tare kuma da na iyalan gidansa tsarkaka.
***********************Musuc*******************************
Masu saurare, anan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin dukkanin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, ni madugun shirin nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.