May 21, 2016 03:26 UTC
  • Ma'anar Tauhidi

Tambayarmu ta yau ita ce minene ma’anar tauhidi ko kuma kadaita Allah madaukakin sarki da shine asali daga cikin shika-shikan musulinci

Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur’ani  mai girma da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, tambayarmu ta yau ita ce minene ma’anar tauhidi ko kuma kadaita Allah madaukakin sarki da shine asali daga cikin shika-shikan musulinci, amma kafin shiga cikin shirin ga wannan.
************************Musuc***************************
Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba, domin amsa tambayar mu kan komawa kan hasken shiriya nauyaya guda biyu Alkur’ani mai tsarki da tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka, abin fahimta daga Ayoyin Alkur’ani da kuma hadisan da dama, ma’anar tauhidi shine kadaita Allah madaukakin sarki wajen bauta shine ya haliccemu kuma shi kadai ne ya ceccanci a bauta masa tare kuma dakore duk wani nau’I na tashbihi ko kuma kotamta shi da halittu da kuma makamantan haka, masu saurare ma’anar tauhidi shine kadaita Allah madaukakin sarki wajen bauta a nma’anar Khas, ma’anarsa kuma Am shine da’a da kuma meka wuya ga Allah madaukakin sarki, a wannan shine na yau za mu fara da kukunan tauhidi domin a hakikanin gaskiya sunada alaka da rukunan sanin Allah hakikanin sani kamar yadda muka ambata cikin hadisai na shirye-shiryen da suka gabata, a cikin suratu An’ami daga Aya ta 100 zuwa ta 104 Allah madaukakin sarki ya ce:(suka kuma sanya Aljannu abokan tarayya da Allah, alhali kuwa shi ya halicce su,suka kuma kirkira masa ‘ya’ya Maza da Mata ba tare da sani ba.tsarki ya tabbata a gareshi kuma ya daukaka daga irin abin da suke siffantawa* wanda ya kyagi sammai da kassai ta yaya da zai kasance a gareshi, bayan kuwa bai kasance  yana da Mata ba? (shi ne) kuma ya halicci komai, kuma shi masanin komai ne*wannan (shi ne) Allah Ubangijinku, babu wani sarki sai shi, mahaliccin komai, to sai ku bauta masa . kuma shi mai kiyayewa ne a bisa komai*Gani ba ya riskar Sa, shi kuwa yana riskar maganai, kuma shi ne Mai tausasawa Masani* hakika Hujjoji sun zo muku daga Ubangijinku, sannan wanda ya gansu(watau ya bi su)to ya kautatawa kansa,wanda kuma ya makance (wato ya ki bi) to kansa ya yi wa.Ni kuwa ba mai gadunku ba ne) har ila yau Allah tabaraka wa ta’ala ya wassafa zatinsa mai tsarki a cikin suratu Shura Aya ta 11 da kuma ta 12 yana mai cewa:((shi ne) mahaliccin sammai da kassai. Ya halitta muku mataye daga kawunanku, daga dabbobi ma (Ya haliyya su) Maza da Mata, yana yada ku ta hanyarsa (wato hadin jinsin biyu), babu wani abu da ya yi kama da shi, kuma shi Mai ji ne Mai gani*mabudan taskokin sammai da kassai na sa ne,Yana shinfida Arziki ga wanda ya so, yana kuma kuntatawa.hakika Shi masanin komai ne) masu saurare wadannan Ayoyi masu albarka sun hada mafi girman ma’anar tauhidi tsarkakekke na cikin zuciya ko kuma na aikace, ganin lokaci ba zai bamu damar bitar daya bayan daya ba, bari mu yi ishara da guda daya daga cikinsu, ma’anar sa kuma shine hakika Allah madaukakin sarki sarki shine kadai ne dayan da bas hi da na biyu, makadaici ne mai rinjaye, kuma shine abin nufi da bukata, ba shi da makamanci, ba a kuma kwatamta shi da komai cikin siffofinsa daukaka da kuma sunayansa kyawawa. kuma  shine  madaukakin sarki da ba babu wani abu da ya yi kama da shi cikin dukkanin Al’amuransa , milkinsa ya daukaka , shine kuma wanda Gani ba ya riskar Sa, shi kuwa yana riskar maganai, kuma shi ne Mai tausasawa Masani.
****************************Musuc*********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai koma bangaren hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka domin su ne nauyi na biyu da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi wasici da su bayan nauyi na farko wato Alkur’ani mai tsarki, a cikin Littafin Attauhid na shekh Saduk (r.a) an ruwaito hadisi daga Abdurrahaman bn Abi Najran ya ce na tambayi Aba Ja’afar Assani wato Imam Jawad (a.s) dangane da tauhudi? Na ce masa ina cikin kokonto dangane da wani abu? Ma’ana ya halarta in yi kokonto dangane yanayi ko kuma kamarnu kebabbu ga Allah madaukakin sarki? Sai Imam Jawad (a.s) ya amsa masa da cewa ( duk abinda wahminka ko kokontonka yayi dangane da Allah madaukakin sarki shi sabanin haka ne, ba a kwatamta shi da komai, kuma kokonto bay a riskar sa, ta yaya kokonto zai riske sa, alhali, shi sabanin abinda hankali zai yi tunani ne, kuma sabanin abinda kokonto zai yi tasawarinsa ko kuma tunaninsa ne), a cikin wani hadisi na daban, Imam (a.s) ya bayyana cewa (sake-saken zukata ya fi  zama gabskiya ga abinda idanuwa za su gani, mai yuyuwa cikin sake-saken zuciyarka ka , ta saka maka kasashe kamar su Indiya da wasu kasashen da ba ta taba sa kafafuwanka ba,kuma ganinka ba zai riske sa ba, to sake saken zuciya bas a riskar Allah madaukakin sarki, to ta yaya ganin idanuwa za su riski Allah madaukaki).a cikin wani hadisi na daban da aka ruwaito daga shugabanmu , Limami na takwas daga limamai iyalan Ahlulbait tsarkaka yayin da yake bayyani kan siffar Allah madaukakin sarki ya ce:( shi ya daukaka daga riskar idanu da kuma sake-saken zukata ko kuma rudun tunani).har ila yau a cikin Littafin Attauhid an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya ce:(a wajen mutane, tauhidi mazhaba uku ne,korewa,kwatamtawa, da tabbatarwa ba tare da kwatamci ba, mazhabar korewa, ba ta halarta ba, mazhabar kwatamtawa ba ta halarta ba saboda Allah ya daukaka da a kwatamta shi da wani abu,hanyar kuma wato ta aminci a cikin wadannan mazhabobi ita ce ta uku wato tabbatarwa ba tare da kwatamci ba).
Masu saurare hadisai da dama da aka ruwaito ta hanyar Ahlulbait (a.s) su nada yawan gaske da suke tabbatar da hanya ta uku wato (tabbatarwa ba tare da kwatamci ba) a matsayin sahihiyar hanyar ta kadaita Allah madaukakin sarki, domin ita wannan mazhaba ita ce ke tabbatar da duk wata kamalar Allah madaukakin sarki tare kuma da kore duk wani nau’I na kwatamci da halitunsa, kuma shi madaukakin sarki da gani ba da kuma rudu gami sake-saken zukata bas a riskar sa domin shi ya tsarkaka daga duk wata kama ta halitunsa,saidai zuciya na ganinsa ta yadda basira ta zo mata daga Ubangijinta, kuma ta wannan hanya take fahimta wujudinsa ko kuma samuwarsa da kuma kadaitarsa na cewa lallai shi bay a kama da komai cikin rahama, tausayi,kudura,aiyuka, rayuwara da dukkanin halittarsa ubangijin Talikai.
*************************Musuc*************************
Masu saurare, ganin lokacin da ake debawa shirin ya kawo jiki, sai kuma a Maku mai zuwa da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, ni madugun ni ke muku fatan Alkheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.