May 21, 2016 03:30 UTC
  • Rukunan Sanin Allah

Tambayarmu ta yau ita ce minene rukunan sanin Allah hakikanin Sani?


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau ita ce minene rukunan sanin Allah hakikanin Sani?sai abiyo mu domin jin amsar wannan tambaya daga cikin nasossi na Alkur’ani mai girma da hadisan ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka.


***********************Musuc**************************


Masu saurare, Ayoyi da dama na Alkur’ani mai tsarki sun bayyana rukunan sanin Allah madaukakin sarki, a cikin wannan shiri mun zabi nassi biyu da suka hada dukkabnin rukunan sanin Allah hakikanin sani, da za mu yi bayyani a kansu ta hanyar hadisan ma’aikin Allah da kuma na iyalan gidansa tsarkaka.nassi na farko shine suratu Tauhid ko kuma Ikhlas wacce ko wani musulmi ya hardance ta , da farko bari mu fara diba irin bayanan da hadisan iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka suka yi a kanta, a cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:( yahudawa sun tambayi ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, suka mas aka bayyana mana ko kuma ka siffanta mana Ubangijinka, imam sadik (a.s) ya yi shuru har so uku suna masa wannan tambaya, sai Allah madaukakin sarki ya saukar da wannan sura, (ka ce, shi Allah daya ne (tak)*Allah abin nufi da bukata*bai aifa ba kuma ba aife shi ba*kuma wani Kini bai kasance a gare shi), a cikin Littafin shara'i ‘I bisa wani dogon hadisi da aka ruwaito, an ce Allah tabaraka wa ta’ala ya ce wa masoyinsa Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ka karanta suratu Ikhlasi domin ita ce kusanci da kuma  siffata ta) har ila yau cikin littafin Uyunul Akhbaru Ridha an ruwaito hadisi daga Abdul-aziz Almuhtadi ya ce:( na tambayi Imam Ridha (a.s) dangane da tauhidi, sai ya ce min duk wanda ya karanta suratu Ikhlasi kuma yaya imani da ita, hakika ya san tauhidi)


Masu saurare, rukunan sanin Allah hakikanin sanin da za fahimta a wannan Aya mai albarka, a jumulce shine, ikrari ko kuma amincewa da cewa Allah madaukakin sarki daya ne tak da babu mai kama da shi, babu daya da kuma ya kasance tamkarsa, shi Tabaraka wa ta’ala shine wanda dukkanin halittu ke nufi da bukatunsu, kuma shi bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba, shine mahilicin da babu wanda ya halicce shi, kuma shine wanda mahilicin da halitunsa ba su rabu da shi ba,da makamantansu, a cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi, inda a cikinsa aka tambayi Imam Zainul abidin (a.s) kan tauhidi sai ya ce :Hakika Allah ya san cewa zai kasance a karshen zamani wasu mutane masu zurfin tunani, sai ya saukar da suratu Ikhlas da kuma wasu ayoyi na cikin suratu Hadid har zuwa fadar Allah madaukakin sarki(shi masanin abubuwan da suke cikin Kiraza ne) duk wanda ya tafi koma bayan wannan hakika ya hallaka.


***********************Musuc************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa nassi na biyu da ya yi bayyani kan rukunan sanin Allah hakikanin sani shine wanda Imam Zainul abidin (a.s) ya yi ishara da shi a shirin da ya gabata, wato Ayoyi guda shida na farko na cikin Suratu Hadid, inda Allah madaukakin sarki yake cewa:(abin da ya ke cikin sammai da kassai ya yi tasbihi ga Allah, kuma shi ne mabuwayi Gwani* milkin sammai da kassai na sa ne, yana raya wa yana kuma kashe wa, kuma shi mai iko ne a bisa dukkan komai* shi ne farko kuma (shi ne)na karshe,(sannan) kuma shine zahiri da badini, shi kuma masani ne da dukkan komai* shi ne wanda ya halicci sammai da kassai cikin kwana shida, sannan ya daidaitu a kan Al’arshi, ya san abin da yake nitsewa cikin kasa da abin da yake fito wa daga cikinta, da kuma abin da yake sauko wa daga sama da abin da yake hawa cikinta, kuma shi yana tare da ku a duk inda kuka kasance,Allah kuma Mai ganin abin da aikata wa ne*Mulkin sammai da kassai nasa ne,kuma ga Allah al’amura za su koma*Yana shigar da dare cikin wuni yana kuma shigar da wuni cikin dare,kuma  shi masanin abubuwan da suke cikin Kiraza ne) masu wadannan ayoyi masu albarka sun tsarkaka Allah daga duk wani raki ko kuma kaidi, domin shine ya hada dukkanin kamala kuma shine ya halicci komai, mai raya wa kuma mai kashe wa  da kuma sauren siffofinsa kamar yadda wadannan ayoyi suka bayyana.masu saurare, da dama daga cikin hadisan iyalan gidan Rahama (a.s) sun bayyana mana wadannan rukunai na ayoyin Alkur’ani domin sanin Allah hakikanin Sani, amma ganin lokacin da muke da shi , za mu takaita ga wadannan nassosi guda biyu, na farko, riwayar da sikkatu Islam kulaini ya ruwaito a cikin Littafinsa Alkafi, inda acikinta aka ce wani mutune ya Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ta yaya kan san Ubangijnka? Sai Amiru mumunin ya ce ta yadda ya sanar da ni kaina,sai Mutuman ya ce ta yaya ya sanar da kai kanka? Sai Imam (a.s) ya ce:babu wata sura da take kama da shi,ba a kuma jin sa da gani, ido ko kuma daya daga cikin abin da ake ihsasi guda biyar, kuma ba a kiyasta shi da Mutane,kusa a cikin nisa, kuma nesa ne a cikin kusa, shine sama da komai, ba a fadar wani abu samansa, yana gaban dukkanin komai,ba a fadar wani abu a gabansa, yana cikin komai, ba kamar wani abu cikin wani abu ba,kuma ya na waje daga komai, ba kamar fitar wani abu daga komai ba, tsarki ya tabbata ga wanda yake haka, babu kamar haka ga waninsa, domin kuma ga wani abu ya nada mafari)


Masu saurare nasinmu na biyo shine wanda aka ruwaito cikin littafin Kafi da waninsa, inda aka ce wasu mutane daga cikin kuraishawa sun tambayi Imam Ali Assajad (a.s) kan cewa ta yaya za su rika zuwa ga Addini? Sai Imam (a.s) ya bayyana musu rukunan Addini, daga jawabin da ya basu yayi ishara da cewa daga cikin rukunan sani, imani da Annabta Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, imam (a.s) wani bangare daga cikin jawabinsa: abin da ya hada Addini abu biyu ne,na farko sanin Allah madaukakin sarki, kuma na biyun sa aiki da yardarsa,sanin Allah madaukakin sarki shine  mutune ya san kadaitakarsa, tausayi, rahama, buwaya, ilimi, kudura da kuma girmansa a kan komai, kuma shine wanda yake anfanarwa, mai cutarwa,kuma shine mai karfi a kan komai,gani ba ya riskarsa, shi kuma yana riskar gani kuma shine mai tausayi masani, kuma Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka bawansa ne kuma ma’aikinsa, duk abinda ya zo da shi gaskiya ne daga wajen Allah madaukakin sarki, kuma duk abinda yake koma bayan wannan bata ne)


**************************Musuc****************************


Masu saurare, ganin lokacin da ake debawa shirin ya kawo jiki, sai kuma a Maku mai zuwa da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, ni madugun ni ke muku fatan Alkheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.