May 21, 2016 03:33 UTC
  • Kadaita Allah A bangaren gudanar da halitta

Tambayarmu ta yau ita ce minene ma’anar kadaita Allah a bangaren gudanar da halitta


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur’ani  mai girma da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, tambayarmu ta yau ita ce minene ma’anar kadaita Allah a bangaren gudanar da halitta, ma’ana ta yaya za mu amince da cewa Allah madaukakin sarki shine ya halicci komai, yayin da a bangare guda mu na ga wasu mutane suna kirkiro wasu ababe ko kuma suna halittu kwayoyin wani abu sabo a ko wata rana, kuma a cikin Alkur’ani mai tsarki, muna karanta cewa hakika Allah ne mafi gwanintar masu  halitta, Alkur’ani ya tabbatar da wadansu masu halitta na daban, saidai ya ce Allah madaukakin sarki shine mafi gwanintar su.ta yaya za mu hada wannan da kadaita Allah a bangaren gudanar da halitta? Domin amsar wannan tambaya za mu koma kan hasken shiriyar ubangiji da kuma mu’ijizar Annabi da ya fi kowa karamci tsira da amincin Allah su tabbatar a gareshi da iyalan gidan tsarkaka, wato Alkur’ani mai girma da kuma tafarkin iyalan gidansa tsarkaka, amma kafin nan ga wannan.


***************************Musuc*******************************


Masu saurare ma’anar kadaita Allah a bangaren gudanar da halitta a jumulci , shine Allah madaukakin sarki shi ya halicci komai  ba tare da bukatar taimakon waninsa ba,kuma shi madaukakin sarki shine farko da asalin wanda ya halicci duk wani nau’in halittu.Ayoyi da daman a cikin Alkur’ani mai tsarki sun tabbata da wannan, a cikin suratu Ra’adi Aya ta 16 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce Allah ne mahaliccin komai, kuma shine makadaici mai rinjaye), a cikin Suratu An’ami Aya ta 102, Allah madaukakin sarki ya ce:(wannan (shi ne) Allah Ubangijinku, babu wani sarki sais hi, mahaliccin komai, to sai ku bauta masa, kuma shi Mai kiyayewa ne a bisa komai) har ila yau a cikin suratu Fadiri Aya ta 2 Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(Abin da Allah yake yi wa Mutane budi da shin a rahama, ba mai iya rike shi, abin da kuma yake rikewa babu mai iya sakin sa in ba shi ba. Shi kuma mabuwayi ne Gwani) kazalika cikin wannan sura mai Albarka Aya ta 3 Allah tabaraka wa ta’ala ya ci gaba da cewa:(Ya Ku Mutane, ku tuna ni’imomin Allah a gare ku.Yanzu a kwai wani mahalicci wanin Allah wanda zai arzuta ku daga Sama ko daga Kasa?babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, to ta yaya ake karkatar da ku), masu saurare , hakika wadannan ayoyi masu albarka da ma makamantansu sun tabbatar mana da cewa Allah madaukakin sarki shine ya halicci komai,don haka ya wajabta mu kadaita shi madaukakin sarki a bangaren gudanar da halitta, kuma dukkanin halittu na komawa ne ga resu tabaraka wa ta’ala.hakika Allah madaukakin sarki shi kaidai ne da idan ya saukar da Rahamarsa babu wani da isa ya hana ta sauka, kuma idan ya rike babu wani da isa da ya watsata kamar yadda muka bayyana a baya,don haka duk wani yanayi na gudanar da halitta na komawa ne gareshi da kuma izininsa, kuma dukkanin halittu wajensa ne makomarsu.saidai wannan na nufi da cewa babu masu halitta bayansa tabaraka wa ta’ala? Bari mu koma cikin littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki domin  samun amsar wannan tambaya, a cikin suratu Ali Imran Aya ta 49, yayin da aka Ambato kissar Annabi Isa (a.s) Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma (zai aiko shi) Manzo zuwa Bani-Isra’ila (ya sanar da su) cewa: hakika ni na zo muku da wata Aya daga Ubangijinku (cewa) hakika  ni zan halitta muku  (wani abu) daga tabo kamar tsuntsu in yi busa a cikinsa ya zama tsuntsu da izinin Allah, zan kuma warkar da wanda bait aba gani ba,da mai cutar baras ko kuturta , in kuma raya matattu da izinin Allah, kuma in baku labarin abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a cikin gidajenku. Hakika kame da wadancan da akwai aya a gare ku idan kun kasance mumunai ).


*******************Musuc******************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, a cikin Suratu Sad Aya 71 da kuma ta 72, Allah madaukakin sarki ya ce:((ka tuna) lokacin da Ubangijnka ya ce da mala’iku : hakika Ni mai halittar mutum ne daga tabo*sannan idan na daidaita shi Na kuma busa masa daga ruhina, sai ku fadi kuna masu yi masa su sujada).har ila yau cikin suratu mumunin Aya ta 14, Allah madaukakin sarki ya ce:(sannan muka mayar da maniyyin ya zama gudan jinni,sai gudan jinin ya zama tsoka, sai muka mai da tsokar kasusuwa, sannan muka lullube kasusuwan da nama , sannan kuma Muka mai da shi wata halitta daban, to alhairan Allah sun daukaka,Wanda shi ne  mafi gwanintar masu halitta)


masu saurare idan muka tunani da nazari ga wadannan Ayoyi masu albarka da makamantansu za mu sami amsar tambayar da ta gabata,da farko imani a kan kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren gudanar da halitta, ba ya nufin kore tsarin sanadi, don haka Allah madaukakin ya gudanar da al’amuran halitta ta hanya sanadi daban-daban da kuma ta kumshi tsarin halitta na dabi’a, kamar yadda wasu Ayoyi na suratu Mumunin suka yi da hakan.


Da halitta ne daga bangaren ma’aifansa a tsarin dabi’a, amma  wannan a tsarin sanadiya na zahiri, amma abinda ya shafi halittar mu’ijiza, kamar yadda Annabi Isa (a.s) ya halicci tsuntsu , Ayoyi sun bayyana cewa hakan ya faru ne da izinin Ubangiji, Allah shine ya gudanar da kudurarsa wajen busawa wannan halitta rai,don haka Allah shi kadai mahaliccin komai tabaraka wa ta’ala Ubangijin Talikai.