May 21, 2016 03:37 UTC
  • Kadaita Allah A Bangaren Bauta

Tambayarmu ta yau ita ce minene ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bauta?


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce minene ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bauta?ma'ana ta yaya bawa zai fahimci cewa dukkanin Al'amuran tarin rayuwarsa ,da yadda take gudana daga Allah ne kuma ya kasance mai kadaida ubangiji a kan wannan, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


*****************************Musuc*****************************


Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba , mu kan amsa wannan tanbayar ne bisa bincike a cikin nauyaya guda, Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da na iyalan gidansa tsarkaka, da farko idan muka koma cikin Alkur'ani mai tsarki, wasu Ayoyi sun bayyana cewa Allah madaukakin sarki shine mai tsara Al'amuran bayinsa kamar yadda yake so, kuma shi kadai ne ba shi da abokin tarayya, a bangare guda wasu Ayoyi na daban sun bayyana cewa tsarin Al'amuran halittu na gudana ne daga mala'iku da saurensu, ta yaya za mu hada wadancan da kuma wadannan gungun ayoyi guri guda,domin samun amsar wannan tambaya da farko bari mun Ambato dukkanin sashin ayoyin domin yin nazari, da farko, a cikin suratu yunus Aya ta 3 Allah madaukakin sarki ya ce:(hakika Ubangijinku shi ne ya halicci sammai da kassai cikin (gwargwadon) kwana shida, yana tsara Al'amura(kamar yadda yake so) Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan shi ne Allah Ubangijinku.to sai ku bauta masa Me ya sa ba kwa wa'anzantuwa?)wannan Aya mai albarka tana bayyanin cewa dukkanin tsari na Al'amuran halittu na komawa ne ga Allah madaukakin sarki domin shi ne Ubangiji komi da komai tabaraka wa ta'ala.a cikin Littafin Uyunul Akhbarurridha, yayin da yake fassara wannan Aya (Dukkan yabo  ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai) suratu fatiha Aya ta 2, shekh Saduk ya bayyana cewa ma'anar(Dukkan yabo  ya tabbata ga Allah) ishara ne ga cika alkarin godiya bisa abinda Allah madaukakin sarki  ya horewa bayinsa kuma ya wajabtawa musu na da su godiyarsa, kuma godiya ga abinda Allah ya horewa Bawansa na alheri. Bangaren (Ubangijin talikai) ishara ne ga kadaita shi, gode masa da kuma tabbacin cewa babu wani mahalicci, mai milki bayansa.idan kuma hakan ya bayyana, masu saurare za mu fahimci cewa ma'anar tauhidi a kadaita ubangiji wajen bauta shine  tabbaci ga cewa Allah madaukakin sarki shi kadai ne yake tsara Al'amuran bayinsa ga abinda yake maslaha ne a gare su, domin haka ya wajaba a kansu su gode masa. Hakika hadisai da dama sun shirya da mu inda suka Ambato musalai da dama na tsarin ubangiji ga Al'amuran Bayi da kuma abinda yake maslaha a garesu, misali sheihk Saduk yardar Allah ta tabbata a gareshi cikin littafinsa mai suna kitabu tauhid ya ruwaito hadisin kudusi daga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, daga Allah tabaraka wa ta'ala, hadisin na tsayo amma ga fasarra wani bangare daga cikinsa, Allah madaukakin sarki ya ce: (kuma hakika daga cikin bayina mumunai, duk wanda yake son Bauta,zan kiyaye masa ita domin kadda al'ajabi ya shiga cikinta ta bace,kuma hakika daga cikin bayina mumunai a kwai wadanda imaninsu ba zai cika zai da wadata, da zan talauta su da imaninsu ya bace, kuma hakika daga cikin bayina mumunai a kwai wadanda Imaninsu ba ya gyaruwa saida rashin lafiya, da za a warkar da su, da warakar ta bata imaninsu, kuma hakika daga cikin bayina mumunai a kwai wadanda imaninsu ba ya gyaruwa saida Lafiya, da za a dora masu rashin laifiya, da ta bata imaninsu, hakika ina tsara Al'amuran bayina a kan sanina da zukatansu, kuma hakika Ni Masani gwani ne).


******************************Musuc****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,Ayoyi da dama na Alkur'ani mai girma sun yi bayyani dangane da kadaita Allah madaukakin sarki da kuma kyakkyawan tsarinsa na Al'amuran bayinsa,daga cikinsu akwai wadanda suke bayyani kan arzikinsa ga bayinsa da kuma yadda yake baiwa wasu arziki mai yawa madaukakin sarki, wasu Ayoyin kuma su yi bayyani kan Allah madaukakin sarki ya horewa bayinsa Ababen dake cikin Sammai da Kassai yake kuma tafiyar da su daidai da bukatun bayinsa ta yadda Mutune zai iya rayuwa mai kyau ya kuma bautawa Allah madaukakin sarki har ta kaisa ga cikar kamala daidai gwalgwado, idan mun fahimci hakan, masu saurare, za mu fahimci ayoyi da suke Magana dangane da tsarin Al'amuran halittu na gudana ne daga mala'iku da saurensu, kamar yadda Aya ta 5 cikin suratu Nazi'at, inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Sannan da (mala'iku) masu tsara al'amura iyakar tsarawa), tsara Al'amuran halittu daga bangaren mala'iku na kasancewa ne da shiriyar Ubangiji Allah madaukakin sarki da izininsa da kuma umarninsa tabaraka wa ta'ala, domin haka wannan shine ma'anar komai na Allah na gudana ne bisa tsari da kuma sababi, ma'ana ba wai Allah madaukakin sarki ba ne yake gudanar da Al'umma kai tsaye, yana bayar da umarni ga wasu halitunsa su gudanar da wasu lamuran.


A takaice, amsar tambayar ta yau ita ce, ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bauta, shine mu yi tabbacin cewa Allah madaukakin sarki shi kaidai yake tsara Al'amuran bayi bisa maslaharsu da kuma yadda za su gudanar da rayuwa mai kyau, su kuma baitawa mahalicinsu har sukai ga kamala daidai gwalgwado.


*****************Musuc*******************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala musaman ma, Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamullahi ta'ala wa barkatuhu.