May 21, 2016 03:39 UTC
  • Kadaita Allah A Bauta Da Tsarin Rayuwar Dan Adam

tambayarmu da yau kuwa ita ce minene ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a Bauta da kuma tsarin rayuwar Dan Adam, alhali kuma muna ganin ko wani mutune shi ke tsara rayuwarsa da kansa, ma'ana ko wani mutune ya nada zabi kan yadda zai tsara rayuwar sa da kansa,


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a cikin shirin da ya gabata mun yi bayyani kan  ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bauta?tambayarmu da yau kuwa ita ce minene ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a Bauta da kuma tsarin rayuwar Dan Adam, alhali kuma muna ganin ko wani mutune shi ke tsara rayuwarsa da kansa, ma'ana ko wani mutune ya nada zabi kan yadda zai tsara rayuwar sa da kansa, to ta yaya zai kasance mutune zai yi imani da kadaita Ubangiji a bangaren tsarin rayuwarsa? Kafin amsa wannan tambayabari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.


*****************************Musuc*****************************


Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba , za mu fara da Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki, Aya ta 1,ta 2 da ta 3 cikin suratu A'ala Allah madaukakin sarki ya ce:(ka tsarkake sunan Ubangijnka madaukaki*wanda Ya Halicci (halitta) sannan ya daidaita (ta))*Wanda Ya gwargwada (abubuwa)sannan ya shiryar (da su)).har ila yau cikin wannan sura daga aya ta 6 zuwa ta 8, Allah madaukakin sarki ya ce:(Da sannu za Mu karantar da kai sannan ba za ka manta ba*sai dai abin da Allah Ya So hakika Shi yana sanin (abin da) yake bayyane da kuma abinda yake Buye*Kuma za mu saukaka maka hanya mai sauki) har ila yau cikin wannan surat mai albarka   Aya ta 14 da kuma ta 15 Allah tabaraka wa ta'ala yace:(Hakika wanda ya tsarkaka ya rabauta* Ya Kuma ambaci sunan Ubangijinsa ,sannan ya yi salla.)masu saurare, idan muka yi nazari, za mu fahimci cewa hakika Allah ya halicci halittu ne a kan tsari mafi kyawan daidaito sannan kuma ya kaddara musu  abubuwa dadai bukatunsu domin isa zuwa ga kamala, kuma hakika Ayoyi da dama sun shiryar da mu dangane da hakan,masu saurare ma'ana kadaita Allah madaukakin sarki a bauta,kamar cikamakin  kadaishi a bangaren haliita, kuma daga cikin  tsarinsa ga Al'amuran halitunsa shine ya aiko musu ma'aika domin su fadakar da su manufar da ta sanya ya halicce su ,kuma da wannan misdakin ne, na yadda ya  shiryar da bayinsa zuwa ga hanya da za ta  isar da su  zuwa ga cikar kamala ke  bayyana da kuma tabbata, daga cikin bayyanar  rububiyarsa , ya shiryar da bayinsa zuwa gayadda za su isa zuwa ga hanya madaidaiciya, ma'anar hakan kuwa shine ya saukaka musu hanya mai sauki da kuma taimakonsu a raywa ta yadda za su bauta masa su cimma manufar da aka halice su saboda ita .amma fadar Allah madaukakin sarki (Hakika wanda ya tsarkaka ya rabauta* Ya Kuma ambaci sunan Ubangijinsa ,sannan ya yi salla.) suratu A'ala Aya ta 14 da kuma ta 15, a cikin wadannan Ayoyi a kwai fadakarwa kan cewa tsari na Al'amuran rayuwan Bawa ya kasance a kan tsarin da Annabawan Allah su ka zo da shi da kuma taimakon Allah madaukakin sarki, domin haka ne ma ko wani mumuni ya kamata ya kasance mai kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren Bauta,tare da sanin cewa Allah tabaraka wa ta'ala shine ubagijinsa madaukaki.


****************************Musuc******************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, idan Bawa ya juya Al'amuran tsarin rayuwarsa sabanin abinda Allah madaukakin sarki ke so,ya bi son ransa ko kuma ya bi shugabanin sabo hakika yayi shirka,domin haka ne ya bayyana cewa yanayin tsarin rayuwar da Bawa ya tsarawa kansa ta kan kasancewa tauhidi, idan ta kasance bisa haske da iradar Allah madaukakin sarki da kuma shiriyarsa.a bangare guda kuma ya kan kasancewa shirka idan ya yi hanun riga da hasken shiriyar Allah tabarka wa ta'ala.shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya ce:( ya girmama tabbacin kadaita Allah a bauta da ya kewaye zukata da gani ,idan ka fahimci haka, sai ka aikata kamar yadda ya kamata wanininka ya aikata kuma duk wanni girma  bukatar da kake da shi  yana wajen Ubangijinsa)


Masu saurare, wannan hadisi na ishara kan ababe kamar haka, na farko shine batun kadaita Allah a bangaren bauta abu ne mai girman gaske da kuma fadi ga dukkanin halittu ta yadda ba zai yuyuwa ilimin Dan Adam na zahiri ko badini ya isa fassara shi, kuma  sanin hakan ya ke banta ne  ga Allah shi kadai da babu wani abin bauta bayansa, ma'ana Allah tabaraka wata'ala shi kadai ne ubangiji madaukaki,da shine ke tsara al'amuran bayinsa ga dukkanin bukatunsu domin isa zuwa kamala da ya kaddara musu ya kuma shiryar da su zuwa gareshi,kuma shine madaukakin sarki da yake tsara al'amuran bayinsa da shiriyar shari'a, ma'ana shiriyarsu ta hanyar ma'aikansa da kuma dokokin da suka zo da su na shari'a, ga abinda yake maslaha ne a garesu, da kuma isar da su zuwa ga rabauta da kamala.


Kamar yadda Allah tabaraka wa ta'ala shine Ubangiji masani ga maslahar bayinsa da kuma dukkanin halitunsa,yana tsara dukkanin Al'amuran bayinsa da shiriya takwuniya ma'ana shi ba ya shiryar da bayinsa ba ne kawai zuwa hanya madaidaiciya da shiriya ta tsarin rayuwa ba, ya shiryar da su a aikace , domin haka idan muka fahimce tsarin da aka tsara bayi da za su bi zuwa ga isa hanya madaidaiciya, tare kuma da kore duk wata Ukuba da  Bawa zai fuskanta sanadiyar aikinsu, domin haka ne shugabanmu Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib(a.s) a karshen hadisin da ya gabata, yayi ruju'I zuwa ga Ubangijinmu madaukakin sarki a dukkanin Al'amuranmu , da kuma cika gurbin 'yar kudirarmu , yawan kasawarmu da kuma karamcin iliminmu wajen gudanar da tsarin rayuwarmu da fadin kudirarsa madaukakin sarki, da kuma yadda iliminsa ya kewaye komai da komai domin mu yayi mana abinda ya dace da mu da Rahamarsa da kuma yadda yake ga ya dace da mu.


*********************Musuc*****************************


Masu saurare a nan za mu dasa , sai kuma a shiri na gaba za a jimu dauke da wani shirin da yardar Allah, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.