Tauhidi a Hakimiya
Tambayarmu da yau kuwa ita ce minene ma'anar tauhidin Allah madaukakin sarki cikin hakimiya wato minene kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren hukunci ?
Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a cikin shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bauta?tambayarmu da yau kuwa ita ce minene ma'anar tauhidin Allah madaukakin sarki cikin hakimiya wato minene kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren hukunci ?wannan na daga cikin misdakin ma'anar tauhidi da Ayoyi da dama na Alkur'ani mai tsarki suka yi ishara da su, so da dama Allah subhanahu wa ta'ala na cewa (hukunci na Allah ne kawai) suratu Yusuf Aya ta 40, domin amsa wannan tambaya da muka gabatar bari mu saurare tanadin da aka yi mana kan faifai.
********************Musuc*************************************
Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba , za mu fara da Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki, a cikin suratu Ali Imrana Aya ta 79 Allah madaukakin sarki ya ce: (Ba zai yiwu ga Mutum idan Allah y aba shi Littafi da hikima da annabci sannan ya ce da Mutane:Ku zama bayina ba na Allah ba, sai dai (ya ce) Ku zama malamai na Allah saboda Kasantuwarku kuna koyar da Littafin(Allah) kuna kuma masu karantar (da shi)), masu saurare idan muka yi Nazari za mu fahimci cewa tsarin rayuwar na bukatar Ubangijinsa shine manufar da Allah madaukakin sarki ya aiko da mursalai domin su isar da wannan sako, ma'ana tsarin rayuwar Dan Adam ta bukatar Ubangijinsa, domin idan ba hakan ba sai ka ga mutune ya kauce ya na bauta wa wanin Allah, amma manufar Allah madaukakin sarki na aiko mursalai shine isar da sakon cewa babu wani abin bauta bayan Allah subhanahu wa ta'ala kuma su koyar da su kyawawen dabi'u domin sun dabi'antu da dabi'un Allah madaukakin sarki.a cikin suratu Yusuf Aya ta 39 da kuma ta 40 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya Abokina na kurkuku, Yanzu iyayen giji barkatai su suka fi, ko kuwa Allah daya mai rinjaye?*Abin da kuke bauta wa wand aba shi ba,ba komai ba ne face wasu sunaye da kuka kago ku da iyayenku, wadanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba.Hukunci na Allah ne kawai, ya yi umarni cewa kada ku bauta wa komai sai shi kadai, wannan shi ne addini mikekke, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka)). Masu saurare abin fahinta a wadannan Ayoyi da suka gabata, shine killace hukunci ga Allah madaukakin sarki ya na nufin tauhidi ko kuma kadaita Allah tabarka wa ta'ala a hukunce hukuncen Addini mikekke wato Addinin Allah subhanahu wata'ala da ta binsa ne Mutune zai kasance ya bi Ubangiji, a bangare guda kuma yayin da Mutune zai bi wani hukunci da bautar wasu aloli na daban, bas a batun Allah daya, kuma bas a hukunci da abinda Allah ya saukar, shi ke nufin cewa sun kaurace ko kuma sun nisanta daga cikar kamala da Allah ya kaddara musu mahilincinsu tabaraka wa ta'ala, masu saurare wannan ma'anar tana fadakar da mu ga wasu Ayoyin na daban da suke bayyanin cewa rashin kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren shara'a, da hukunce-hukunce wato komawa gareshi madaukakin sarki wajen sanin Addini mikekke, shine bin hukuncin Jahiliya,a cikin Suratu Ma'ida Aya ta 49 da kuma ta 50 Allah madaukakin sarki ya ce:( kuma ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah ya saukar, kada kuwa ka bi son ransu, ka kuma yi takatsantsan da su don kada su fitine ka (wato su batar da kai) ga sashin abin da Allah ya saukar a gare ka.Idan suka ba da baya to ka sani cewa lallai Allah yana so ne ya kama su da sashin zunubansu. Hakika kuma yawancin Mutane fasikai ne*shin hukuncin jahiliyya suke nema ne?Ai kuwa ba wanda ya fi Allah nagartaccen hukunci ga mutane masu sakankancewa (watau masu yarda da gaskiya))
**********************Musuc*******************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, a cikin gaban shirin za mu koma kan nauyi na biyu wato tafarkin iyalen gidan ma'aikin Allah tsarkaka, hadisai da daman a iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka sun yi bayyani kan misdakin kadaita Allah madaukakin sarki a aikace na manufar hukunce-hukunce ko kuma mice a shari'a, misali a cikin Littafin Nahjul Balaga, shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yana yiwa Dansa Imam Hasan Mujtaba (a.s) wasiya, inda a cikin ta yake bayyana hakika da misdakin wannan bangare daga bangarorin Tauhidi ko kuma kadaita Allah na gaskiya, Imam (a.s) ya ce: ka mayar da zuciyarka ga Al'amuranta gaba dayansu zuwa ga Ubangijinka, domin idan kayi hakan ……kuma ka zamanto mai ikhlasi ga Ubangijnka a ko wata mas'ala, domin bayarwa da hanawa na hanunsa kuma ka yawaita yin Istikhara), a cikin khuduba ta 24 Imam Aliyu bn Abi Talib(a.s) y ace:(ku ji tsoron Allah , bayin Allah, kuma ku gudu zuwa ga Allah,ku tabbatu a kan hanyar da ya shata muku,a gare ni tabbacin rabautar ku a ranar gobe idan har ba ku batasu ba a nan duniya).
Masu saurare, bisa Ayoyi da hadisan da muka gabatar za mu fahimci cewa, ma'anar tauhidin Allah madaukakin sarki a bangaren hukunci, shine mumuni ya mayar da dukkanin Al'amuransa zuwa ga Allah madaukakin sarki,da kuma wadanda suke jibintar Al'amuransa daga cikin Annabawa da wasiyai amincin Allah ya tabbata a garesu domin sanin hukunce-hukuncensa a dukkanin komai wanda hakan shi zai bashi dama yayi aiki da shi ya zamanto mutuman Allah, kuma mai gyara a doron kasa.
***********************Musuc***************************
Masu saurare,a nan za mu dasa Aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.