Kadaita Allah A bangaren Shari'a
Tambayarmu da yau mine dalilin da ya sanya Allah madaukakin sarki yay i umarni da aka kadaita shi a bangaren hukunci da shara'a kuma ya umarci Mutum da ya koma zuwa ga abinda ya saukar (wato Littafinsa mai tsarki) domin daukan duk wasu hukunce hukuncen da ya kamata a cikin dukkanin Al'amuransa?
Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,?tambayarmu da yau mine dalilin da ya sanya Allah madaukakin sarki yay i umarni da aka kadaita shi a bangaren hukunci da shara'a kuma ya umarci Mutum da ya koma zuwa ga abinda ya saukar (wato Littafinsa mai tsarki) domin daukan duk wasu hukunce hukuncen da ya kamata a cikin dukkanin Al'amuransa? Kafin nazari ga wannan tambaya bari mu saurari wannan.
********************Musuc******************************
Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba ya kan yin nazari ga nauyaya guda biyu wato Alkur'arni mai tsarki da kuma tafarkin Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka domin neman amsar wannan tambaya, Alkr'ani mai girma ya bayyana masa Asalin illar wacce domin ita ne , Allah madaukakin sarki ya umarce mu da ruju'u zuwa gare shi wato Addini mikekke da Ma'aikansa suka zo da shi, A cikin suratu Ma'ida Aya ta 50, Allah madaukakin sarki ya ce:(Shin hukuncin Jahiliyya suke nema ne?Ai kuwa ba wanda ya fi Allah nagartaccen hukunci ga Mutane masu sakankancewa (watau masu yarda da gaskiya)).domin haka, rashin kadaita Allah a bangaren hukunci da shara'a da kuma koma wa zuwa ga abinda ya saukar (wato Littafinsa mai tsarki) domin daukan duk wasu hukunce hukuncen da ya kamata a cikin dukkanin Al'amuransa yana nufin fadawa cikin tarkon jahiliya da kuma hakan shi zai jefa mutane cikin shakiyanci. Domin hukuncin Allah da shara'arsa, makomarsa shine gwani masani ga dukkanin abinda yake maslaha ga ko wani mutum, kuma shi madaukakin sarki Adali ne da babu zalinci a cikin hukuncinsa, domin haka ne ma wadanda suka bin mikekken Addini na gaskiya su nada tabbaci na isa zuwa ga dukkanin kamalu, Albarkatu da Alkhairu dawamammu da Allah ya halicci Mutune domin isa zuwa garesu, a bangare guda kuma duk wanda ya bi wani tsarin da ba wannan ba ya zabi hukunci jahiliya,shi kuma hukunci jahiliya rageggen hukunci da bashi da tabas kuma hakan na zuwa ne sakamakon bin son rai da sauransu. Kuma wannan shine abinda tsahon tahiri ya shaida ,domin shi Addinin jahiliya, Mutune ne ya kirkiro sa da kansa don haka ba zai kasance kammalalan Addini ba domin shi kansa mutum din ba kamili ba ne, face wanda Allah madaukakin sarkin ya sanya ya zamanto kamili sakamon da'a da biyayyarsa ga shi subhanahu wa ta'ala.
Masu saurare, a bangare guda Alkur'ani mai tsarki ya siffanta wadanda ba sa hukunci da Abinda Allah ya saukar da siffofi uku, kafiri, Azzalimi da kuma fasiki, kamar yadda ya zo cikin Suratu Ma'ida Ayoyi na 44,45, da kuma 47,domin haka duk wani hukunci da ba na Allah ba sunansa kafirci ,kuma yaki ne ga ni'imar mikekken Addinin da Allah ya saukarwa bayinsa, kamar yadda yake zalinci ne, zalinci ga kai saboda an haramta mata ni'ima da kuma Albarkar aiki da mikekken Addini da shara'ar Allah mai albarka, ko kuma zalinci ne ga wasu domin an bata musu lokaci kuma an toshe musu hakkokinsu daga wani sashe da suka kirkiro musu bata , da hakan ya hana su bin Addinin Allah madaukakin sarki, kuma kamar yadda yake hukunci da ba na Allah ba, fasikanci ne, saboda shi fita ne daga hanya madaidaiciya da Allah madaukakin sarki ya saukar wa Bayinsa domin cimmawa sa'ada ga mutum da Al'umma gaba daya.
*******************Musuc*********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai koma ne kan nauyi na biyu wato tafarkin Manzon Allah da na iyalan gidansa tsarkaka,a cikin Littafin Nahjul-Balaga khuduba ta 150, shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) y ace:(Hakika Allah madaukakin sarki ya zaba muku musulinci ya kuma zaba muku a matsayin Addini, domin a cikin sa a kwai sunan Aminci ,kuma shi ya hada dukkanin karamci, ya zaba muku hanyarsa ya kuma bayyana hujojinsa, cikinsa da kwai …..Ni'imomi da kuma fitilan dake haskaka duhu, babu wani Alheri da zai budu sai da makulansa, kuma duhu ba zai yaye ba sai da haskensa, a cikinsa ne ke da waraka ga neman warakar).A cikin khuduba ta 18 Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) y ace:(shin Allah madaukakin sarki ya saukar da rageggen Addini ne ya kuma nemi taimakonsu domin ciki shi?Allah subhanahu yana cewa (Ba mu yi sakacin barin komai a cikin Littafin nan ba) suratu An'ami Aya ta 38 kuma ya ce:(a cikinsa a kwai bayani na ko wani abu)). A cikin khuduba ta 118, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Ku saurara!Hakika hukunci Addinin Allah guda ne kuma hanyarsa gangarawa ce, duk wanda ya dauke ta zai cimmawa, kuma duk wanda ya ki ta ya bace kuma zai yi nadama).
A karshe cikin Khuduba ta 159 Imam Ali (a.s) ya ce:(an bayyana masa dokokin da ba su da tushe, an tusa bidi'oi a cikin Addini, an bayyana hukunce-hukunce da dokoki filla-filla, duk wanda ya nemi wani Addini ba musulinci ba, shakiyancin sa ya tabbata…….. kuma makomarsa za ta kasance cikin dogon bakin ciki da Azaba mai radadi)
Masu saurare takaicecciyar amsar wannan tambaya a cikin wannan shiri shine sirrin kadaita Allah madaukakin sarki a hukunci da dokoki shine hakika Addininsa na gaskiya shi kadai ne mikekken Addini kuma cikekke, da ya tsarkaka daga duk wani tasirin son Rai, Zalinci, duhun jahilci, kuma shi kadai ne yake sanya Mutune ya samu sa'ada a nan Duniya da kuma Lahira, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon aiki da hukunce-hukuncensa na mikekken Addinin da ya saukar mana ta hanyar Annabawansa tsarkaka domin mu rabauta da sa'adarsa a nan duniya da kuma Lahira.
************************Musuc***********************
Masu saurare, a nan zamu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shirin ya kamala, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.