Kadaita Allah A Bangaren Biyayya
Tambayarmu ta yau minene ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren Da'a ko biyayya
Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau minene ma'anar kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren Da'a ko biyayya,kuma ta yaya za mu kasance masu kadaita shi a kan haka? Kafin nan ga wannan.
***********************Musuc************
Masu saurare , da farko abinda za mu fahimta a cikin Ayoyin Alkur'ani mai tsarki shine wajibcin da'a ga Allah madaukakin sarki shi kadai , domin haka I'itikadi na kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren da'a ko biyayya shine Imani, ma'ana shi kadai madaukakin ya wajabta a yi masa da'a wannan shine bangaren I'itikadi Nazari, amma kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren da'a ko biyayya a aikace ya na tabbatuwa ne yayin da Bawa yayi riko da kuma iltizami ga abinda Allah yayi umarni da shi, da kuma kaucewa ko kiyayye abinda ya yi hani da shi, kuma da meka wuya ga hukunce-hukuncensa a dukkanin Al'amuran Dan Adam na ruyuwarsa, Aya ta 16 cikin suratu Tagabun ta yi ishara ga wannan hukunci wato biyayya ga Allah ta hanyar kaucewa saba masa shine (tsoron Allah) da kuma yi masa biyayya wajen amsa Umarninsa, Allah madaukakin sarki ya ce:(Saboda haka ku ji tsoron Allah iya kokarinku,kuma ku ji, ku bi, ku kuma ciyar, (shi) ya fi alheri a kanku,duk wanda kuwa ya danne kwadayinsa to wadannan su ne marabauta) suratu Tagabun Aya ta 16.Masu saurare cikin Littafin Allah mai tsarki wato Alkur'ani mai girma mu kan karanta cewa Allah madaukakin sarki ya yi tabbacin biyayyarsa bisa biyayyar ma'aikansa da kuma majibinta Al'amuransa,hakan ya sa muka fahinci cewa yin biyayya ga ma'aikansa da kuma majibinta Al'amuransa amincin Allah ya tabbata a garesu shike tabbatar da misdakin yiwa Allah madaukakin sarki biyayya, a cikin Suratu Nisa'I Aya ta 64 da kuma ta 65 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ba Mu aiko wani Manzo ba sai don a bi shi da izinin Allah,Da dai a ce lokacin da suka zalunci kansu sun zo maka sannan suka nemi gafarar Allah, Manzo kuma ya nema musu gafara, to lallai da sun sami Allah mai yawan yafewa ne Mai yawan Rahama*Na rantse da girman Ubangijinka ba za su ba da gaskiya ba har sai (lokacin da) suka sanya ka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba za su sami wata tababa ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma mika wuya gaba daya) har ila yau cikin suratu Nisa'I Aya ta 59 Allah madaukakin sarki y ace:(Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku bi Allah ku kuma bi Manzo,da kuma majibinta al'amuranku(watau shugabanin Addini).sannan idan kuka samu sabani game da wani Abu, to sai ku mai da shi zuwa ga Allah (wato Littafin Allah Alku'ani) da Manzonsa (lokacin da yake raye ko kuma sunarsa bayan fakuwarsa), idan kun kasance kun ba da gaskiya da Allah da ranar Lahira.(Yin ) wancan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawar makoma) har ila a cikin suratu Nisa'I Aya ta 83 Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan kuma wani Labari ya zo musu na aminci (cikin nasara) ko na tsoron (rashin nasara), sai su watsa shi, (don su raunana zukatan mumunai). Da dai za su komar da shi (watsa labaran) zuwa ga Manzo ko kuma zuwa ga masu hankali daga cikinsu, lallai da wadanda suke tace shi (labarin) daga cikinsu sun gane shi(labarin da ya kamata su watsa). Da ba don falalar Allah ba a gare ku da kuma Rahamarsa, da ba shakka kun bi shaidan (kan abin da yake kawata muku na miyagun abubuwa) in ban da 'yan kadan daga cikinku).masu saurare abin fahimta ga wadannan Ayoyi masu Albarka shine biyayya ga Annabin Rahama ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma da yin biyayya ga majibinta Al'amura cikin dukkanin umarninsu amincin Allah ya tabbata a garesu suna a matsayin yin Da'a da biyayya ga Allah madaukakin sarki .
***********************Musuc********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Hakika ya tabbata cikin hadisai masu inganci kamar hadisin Qadir, da kuma hadisai da dama na iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka na cewa majibinta Al'amura da Aya ta 59 cikin suratu Nisa'I ta yi ishara da su sune iyalan gidan Annabin Rahama (S.A.W) kuma wasiyansa su 12 amincin Allah ya tabbata a garesu, sakamako zai kasance cewa yi musu da'a da biyayya amincin Allah ya tabbata a gare su cikin komai bisa hukuncin wannan Aya shine da'a ga Allah madaukakin sarki da kuma Ma'aikin sa (s.a.w).
A bangare guda Allah madaukakin sarki yayi umarni da a yi biyayya ko da'a ga wani gungu da ya bayyana misali kamar iyaye, biyayarsu za ta kasance kayyadadiya ce daga umarnin Ubangiji, kin yi musu biyayya ko da'a zai kasance sabawa Allah madaukakin sarki,a bangaren dake karo da wannan, shine, Allah madaukakin sarki ya yi hani ga yin biyayya ga wani gungu na daban kamar wadanda zukatansu suka gafala da ambaton Allah madaukakin sarki, yin biyayya garesu zai kasance haramun ne, kuma duk mumuni da ya kasance mai kadaita Allah wajen biyayya da da'a wajibi ne ya sabawa wadancan gungu.
Masu saurare zuna nan, za mu fahimci takaicecciyar amsar tambayarmu da ta gabata cikin wannan shiri, Hakika kadaita Allah madaukakin sarki a bangaren Da'a ko biyayya , yana tabbatuwa ne ga yin biyayya ga umarnin da Ma'aikansa amincin Allah ya tabbata a garesu suka zo da shi, yin da'a da umarnin Allah na tabbatuwa ne ta hanyar yimu da'ar da ba iyaka wato Annabin Rahama da iyalan Gidansa tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya, kamar yadda yin da'a da biyayya ga umarnin Allah wajen yiwa iyaye da msu Nasiha biyayya da makamantansu na daga cikin biyayya ga Umarnin Ubangiji da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu damar yi masa biyayya da da'a kamar yadda ya umarce su ta hanyar yin da'a ga umarnisa, Annabawansa da kuma majibta Al'amuransa.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.