Yiwa Annabi Adamu (a.s) Sujada
Tambayarmu ta yau ita ce yaya za mu fahimci umarnin da Allah madaukakin sarki ya baiwa mala'ikunsa na su yiwa Annabi Adam (a.s) sujuda, alhali sujuda na daga cikin misdakin bauta
Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce yaya za mu fahimci umarnin da Allah madaukakin sarki ya baiwa mala'ikunsa na su yiwa Annabi Adam (a.s) sujuda, alhali sujuda na daga cikin misdakin bauta? Yayin kuma da Allah madaukakin sarki ya yi umarni na cewa kada a bautawa kowa face shi kadai.kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
****************Musuc************************
Masu saurare, idan muka koma cikin Alkur'ani mai tsarki za mu ga cewa hakika Allah madaukakin sarki ya umarci Mala'ikai da su yiwa Annabi Adamu (a.s) sujada, a bangare guda kuma ga hikayar Annabi Yusuf (a.s) inda Ma'aifinsa Annabi Yakuba (a.s) tare da sauren 'ya'yansa suka yi wa Annabi Yusuf (a.s) sujada kamar yadda yazo cikin suratu Yusuf. Domin haka, a zahiri, Mala'iku sun yiwa wanin Allah wato Annabi Adam (a.s) sujada kuma Annabin Allah Ya'akub (a.s) yayiwa Dansa Annabi Yusuf (a.s) sujada, to ta yaya hakan ya kasance ba shirka ba? Domin amsa wannan tambaya ba ri mu koma cikin Alkur'ani kansa kuma cikin suratu Yusuf din da kanta cikin muhawarar da Allah tabaraka wa ta'ala ya nakalto wacce ta gudana tsakanin Annabi Yusuf da abokaninsa na gidan yari a yayin da suka bukaci ya yi musu fassarar mafalkinsu. Ya zo cikin Aya ta 39 da kuma 40 na suratu Yusuf, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya abokaina na kurkuku, yanzu iyayen giji barkatai su suka fi,ko kuwa Allah daya mai rinjaye?Abin da kuke bauta wa wanda ba shi ba, ba komai ba ne face wasu sunaye da kuka kago ku da iyayenku, wadanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba. Hukunci na Allah ne kawai, ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kadai.wannan shi ne addini mikakke, sai dai yawancin mutane bas a sanin (haka)) masu saurare, idan muka yi nazari cikin wadannan ayoyi biyu masu albarka za ma fahimci cewa , an hana bautar alloli ne saboda illoli guda biyu, da farko saboda kasancewarsa bautar wanin Allah ne, ma'ana girmama wasu alloli barkatai a matsayinsu na koma bayan Allah madaukakin sarki, na biyu ya kan kasancewa girmama su a matsayinsu na alloli masu ci gishin kansu koma bayan Allah madaukakin sarki, domin haka wannan illoli biyu wajen gudanar da ibada shirka ne saboda kasancewar abin bautar a nan alloli barkatai koma bayan Allah da kuma Allah madaukakin sarki bai yi umarni da a girmama su ba, kuma su allolin girgirar Dan Adam ne kamar yadda Alkurni mai tsarki ya ce:( wadanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba) domin haka za mu samu takaiceciyar amsa cikin wadannan Ayoyi masu albarka kamar haka: girmama wani mahluki, rusanawa da kuma kaskantar da kai a gareshi ba zai kasance shirka ko kuma bauta ga wanin Allah ba ko da ya kasance yin sujjada a gareshi tare da sharuda guda biyu na farko kadda ya kasance kaskantar da kai a matsayin mai cikekken 'yanci na ganin ya caccanta a yi masa hakan ba, koma bayan Allah kamar yadda Alkur'ani ya bayyana, na biyu idan kaskantar da kai ko kuma rusanawa wani bawan ya kasance bias bin Umarnin Allah madaukakin sarki da kuma yardarsa, sai ya zamanto bautar Allah madaukakin sarki ba shirka ba.
*************************Musuc***********************
Masu saurare, Barkanmu da sake saduwa ,idan muka yi nazari zai mu fahinci cewa, hakika Alkur'ani mai girma ya yi kakausar suka kan tawayen da Iblis La'ancecce ya yi ga umarnin Allah na kin yi sujjada ga Annabi Adamu (a.s) sannan ya bayyana hakan a matsayin girman kai da jiji da kai tare da ganin fifiko a kansa , wadannan munanan halaye na shaidan sune sandiyar tushe duk wata Ibadar Allah madaukakin sarki, kamar yadda Hadisai suka bayyana , hakika Sujadar Mala'iku ga Annabi Adamu (a.s) ibada ne ga Allah madaukakin sarki, a cikin Tafsirin Ayyashi, an ruwaito hadisi daga shugaban masu kadaita Allah (a.s) ya ce:(farkon gurin da aka bautawa Allah madaukakin sarki shine garin kufa, yayin da Allah ya umarci Mala'iku su yi wa Annabi Adamu (a.s) sujada atudun garin kufa), a cikin Littafin Al'ihtijaj, an ruwaito wani hadisi da sanadinsa ke komawa ga Imam Husain (a.s), inda aka ce wani Bayahude daga cikin maluman garin Sham ya ce wa Imam (a.s) hakika Allah ya umarci Mala’ikunsa da su yi wa Annabi Adamu (a.s) Sujada, shin an yiwa Annabinku Muhamadou wani abu mai Kamar haka? Sai Imam Ali(a.s) ya amsa masa da cewa:(Hakika hakan ya kasance, ko da kuwa Allah madaukakin sarki ya sanya mala'ikansa sun yiwa Annabi Adamu (a.s), hakika ka sani cewa Sujadar su ba ta kasance sujada ta bauta ba,ba su bautawa Annabi Adamu koma bayan Allah ba, hakan kuwa, ya kasance a matsayin I'itirafi na bayyana fifikonsa da rahama daga Allah a gareshi, sai Imam (a.s) ya ce: shi kuma Annabi Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka an bashi abinda ya fi wannan, hakika Allah madaukakin sarki ya yi masa salati tare da mala'ika baki daya sannan ya sanya shi a matsayin bauta ga dukkanin mumunai wato ya umarci dukkanin mumunai da su yi masa salati, wannan kari ne gare shi, amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka).
Masu Saurare, takaicecciyar amsar da zamu dauka ga tambayar dake wannan shiri, shine kamar haka, da farko: Hakika Nassosi Alkur'ani sun bayyana cewa kaskantar da kai da kuma girmama wanin Allah madaukakin sarki zai kasance shirka idan ya kasance an yiwa makiyan Allah wadanda ba su tsantsanci girmamawa ba. Na biyu kuma shine hakika girmamawa daga Umarnin Allah na girmama wasu bayin Allah zai kasance bauta ne da Ibada ga Allah madaukakin sarki misali kamar da'a da biyayya daga umarnin Allah na yiwa wadanda Allah madaukakin sarki yayi umarni da a yi musu da'a ko kuma a yi musu biyayya,halkan kuwa yin biyayya da da'a ne ga Allah tabaraka wa ta'ala.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.