May 21, 2016 03:50 UTC

Tambayarmu ta yau ita ce minene dalilin da ya sanya Allah madaukakin sarki ya umarci Mala'iku su yiwa Annabi Adamu (a.s) sujada, shin ma minene ake nufi da sujada a gareshi?

Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce minene dalilin da ya sanya Allah madaukakin sarki ya umarci Mala'iku su yiwa Annabi Adamu (a.s) sujada, shin ma minene ake nufi da sujada a gareshi? Domin amsa wannan tambaya bari mu koma ga hasken shiriya wato Littafin Allah mai tsarki da tafarkin manzon sa gami na iyalan gidansa tsarkaka, amma kafin nan bari mu saurari wannan.

 

**************************Musuc********************************

 

Masu Saurare, Hakika Allah tabarka wa ta'ala mai Hikima ya Ambato umarnin da ya baiwa mala'iku na yiwa Annabi Adamu (a.s) sujada cikin gurare da dama a Littafinsa mai tsarki wato Alkur'ani kamar cikin surorin Bakara,A'arafi, Isra'I, Hijir,kahafi da kuma Taha, wannan shike nuna mahimancin maudi'in da kuma irin darunsan dake ciki da ya shafi dukkanin shiriyar halittu, sa'adarsu da kuma samun tsirarsu daga farkon mutane zuwa karshensu har ranar kiyama.idan mu kayi nazari a cikin kuraren da Allah madaukakin sarki ya Ambato hikayar umarnin da ya bayar na yin sujada ga Annabi Amadu (a.s), za mu fahimci matsayin da Iblis la'anceccen Allah ya dauka na yin tawaye ga umarnin Allah madaukakin sarki tare da  bayyana girman kai ga iradar mahalicci mai hikima madaukakin sarki.a cikin wannan a kwai darasi na cewa mu yi hattara wajen bin aiyukan shaidan da suke toshewa mutum hanyar bautar Allah, domin haka Allah tabaraka wa ta'ala yake fadakar da mutane na su nisanci asalin illar da ta sanya Iblisi ya yi tawaye ga bautar Allah madaukakin sarki wajen kin kaskantar da kai ga wanda ya fifita daga cikin halitunsa, kuma wannan ba komai ba ne face girman kai, kamar yadda Alkur'ani mai tsarki ya bayyana, cikin Suratu Bakara Aya ta 34 Allah madaukakin sarki ya ce:((kuma (ka tuna Ya Muhamadu) lokacin da Muka ce da Mala'iku Ku yi sujjada ga Adamu,sai suka yi sujjada in ban da Iblis da ya ki,ya kuma yi girman kai kuma ya kasance a cikin kafirai) , a cikin suratu   A'arafi Aya da 12 da ta 13 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya ce (da shi) "Me ya hana ka ka yi sujada lokacin da Na umarce ka? Sai ya ce Ai ni na fi shi (domin kuwa ) ka halicce ni ne daga wuta (shi) kuwa ka halicce shi ne daga tabo*(Allah) ya ce:To sai ka sauka daga gare ta(watau Aljanna),bai kamata ba ka yi girman kai a cikinta, saboda haka a fita, hakika kai kana cikin kaskantarttu)

 

Masu saurare, idan muka yi nazari, za mu fahimci cewa wannan ayoyi masu albarka sun bayyana mana hakikanin  al'amari, na umarnin Ubangiji da ya bayar na yiwa Annabi Adamu (a.s) sujada, tare da bayyana hakikanin shaidan a bangare guda, tare kuma da yin galgadi na nisantar asalin illar da ta toshe bautar Allah madaukakin sarki wacce ita ce son kai  da kuma girman kai. Idan muka yi nazari za mu fahimci cewa Ayoyin da suke Magana kan umarnin yiwa Annabi Adamu (a.s) sujjada wadanda suke cikin suratu Bakara sun zo ne bayan Ayoyin da suke bayyani kan koyar da Annabi Adamu sunayen Ubangiji kyawawa, da hakan shike tabbatar mana da cewa illar da ta sanya aka bada umarnin yiwa Annabi Adamu sujjada shine Ibadar Allah madaukakin sarki ba ta tabbatuwa saida girmama sunayansa, kuma wannan shine abinda hadisai da dama masu inganci suka yi bayyani a kansa.

 

****************************Musuc******************************

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a ci gaban shirin  zai koma tafarkin Manzon Allah tsira da amincin Allah tare kuma na iyalan gidansa tsarkaka, misali shekh Saduk cikin Littafin Uyunul Akhbaru Ridha ya ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Hakika Allah   tabaraka wa ta'ala ya halicci Adamu sai sanyamu cikin tsatsonsa sannan kuma ya umarci Mala'iku su yi masa Sujjada domin girmamawa da kuma karramawa a gare mu, kuma Sujjadar ta kasance ga Allah madaukakin Ibada ne, ga Annabi Adamu kuma karamci ne da kuma biyayya saboda kasancewarmu cikin tsatsonsa).A cikin Littafin Sharhul Ayat an ruwaito wani hadisi daga Imam Husain (a.s) na cewa hakika kafin waki'ar Ashura cikin tausayi ya bayyanawa sahabansa cewa, Ya ku masoyanmu da masu biyayya ga Al'amuranmu , masu kiyayya da makiyanmu shin kuna so in  fada muku farko Al'amuranmu da Al'amuranku na abinda kuke a kai domin ya kasance sauki a gareku, sai suka ce Na'am ya dan Ma'aikin Allah (amincin Allah ya tabbata a gareka) Sai Imam (a.s) ya ce :Hakika Allah madaukakin sarki yayin da ya halicci Annabi Adamu ya daidaita shi, ya sanar da shi sunayen komai sannan ya bukaci Mala'iku da su sanar da shi wadannan sunaye, ya sanya Annabi Muhamadu, da Ali, Fatima, Hasan da Husain cikin tsatson Annabi Adamu , ya kasance haskenmu  na haskakawa cikin Al'amurra na cikin Samai da Aljanna, kudura da kuma Al'arshi, Imam (a.s) ya ci gaba da cewa sannan sai Allah ya umarci Mala'iku suyi masa Sujada domin giramamawa da kuma yadda ya fifita shi bayan da ya sanya shi garkuwa ga wadannan tsarkakakun bayi wadanda haskensu ya mamaye dukkanin al'amurra, sai suka yi masa sujada face Iblis da ya ki ya kaskantar da kai ga bayyanar girman Allah,ko kuma ya kaskantar da kai ga bayyanar haskenmu iyalan gidan Annabta, hakika kuma dukkanin Mala'iku sun yi tawadu'I ko kuma kaskantar da kansu saidai shi Iblis ya yi giraman kai da kuma  dagawa, wannan ya kasance daga iyayensa kuma girman kan nasa ya sanya yana daga cikin 'yan wuta). A cikin Littafin Ilalu Shara'I'I shekh Saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(yayin da aka yi isra'I da Annabi Muhamad (s. a.w) ,da Lokacin Salla ya yi sai Mala'ika Jibrilu (a.s) ya yi kiran salla ya kuma meke domin ya yi salla sai ya ce Ya Muhamad ka shiga gaba ga bamu salla domin mu ba ma gabatar Dan Adam tun lokacin da aka umarcemu mu yi sujjada ga Annabi Adamu(a.s)).

 

Masu Saurare, takaicecciyar amsar da za mu  fahimta cikin wannan shiri shine hakika umarnin Ubangiji na yin sujada ga Annabi Adamu ya hada da fadakarwa na cewa bautar Allah tana tabbatuwa ga girmama bayyanar girmansa da kuma kyawansa madaukakin sarki, kuma wannan ba komai ba ne face Annabi Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.

 

*******************************Musuc*************************

 

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.