Ma'anar Bautar Wanin Allah
Tambayarmu ta yau ita ce mi ake nufin da bautar koma bayan Allah wato wasu alloli ne aka hanemu da bautawa,alhali muna rayuwa a wannan zamani na rashin allolin da aka sassaka su da itace kamar yadda ya kasance mushrikai suna bautawa a lokacin jahiliya?
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce mi ake nufin da bautar koma bayan Allah wato wasu alloli ne aka hanemu da bautawa,alhali muna rayuwa a wannan zamani na rashin allolin da aka sassaka su da itace kamar yadda ya kasance mushrikai suna bautawa a lokacin jahiliya? Sai a biyomu domin jin amsar wannan tambaya, amma kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
********************************Musuc**************************
Masu Saurare,da farko abin fahimta cikin nassosi da dama shine hakika Allah madaukakin sarki ya hane mu da bautarwa alloli da mutum ya sassaka da hanunsa daga Itace kuma ya dawo yana bauta musu a matsayin abin bauta a zamanin jahiliya,bautar gumaka ko kuma wanin Allah shike aifar da alloli masu yawa da ya yi daidai da ko wani lokaci sabanin tunanin wannan Al’umma da kuma al’adunsu.domin haka muka ga ya dace ga mai neman tsira da fadawa cikin ko wani irin nau’I na shirka da ya fahimci wannan al’amari domin kauce musu, idan muka koma cikin Alkur’ani mai tsarki za mu fahimci cewa a matakin farko Allah madaukakin sarki ya yi mana hanuka mai sanda na mafi kusancin bautar wanin Allah ko kuma mu ce shirka wannan Al’amari ba ko mai bane face bin son rai, A cikin suratul Furkan Aya ta 43Allah madaukakin sarki ya ce(ka ba ni labarin wanda ya riki son zuciyarsa (shi ne) Ubangijinsa, to yanzu kai ka zama mai kiyaye shi(daga bin son zuciyarsa)) cikin suratu kasas Aya ta 50 Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(To idan ba su amsa maka ba,sai ka tabbatar da cewa ba abin da suke bi sai son ransu kawai; ba kuwa wanda ya fi bacewa kamar wanda ya bi son ransa ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Hakika Allah ba ya shiryar da mutane kafurai) har ila yau cikin suratu Jasiya Aya ta 23 Allah madaukakin sarki ya ce:(Shin yanzu ba ka ganin wanda ya riki Ubangijinsa, son ransa, Allah kuma ya batar da shi a kan sani ya kuma rufe jinsa da kuma zuciyarsa, kuma ya sanya rufi a ganinsa, to waye zai shiryar da shi bayan Allah !Me ya sa ba kwa wa’azanta ne(watau ba mai shiryar wa sai Allah)) Masu saurare, idan muka yi nazari cikin wadannan Ayoyi masu albarka za mu fahimci cewa duk mutuman da ya riki son ransa a matsayin abin bautarsa ma’ana yake biyewa son ransa maimakon ya bi hukunci da Allah madaukakin sarki ya saukar zai fada cikin hallaka na bautar wanin Allah, ma’anar riko da son rai a matsayin abin bauta, shine mutum ya yiwa son zuciyarsa biyayya ya so abinda take so ba tare da ya kiyaye muradin Allah madaukakin sarki ba,wannan shike nuna cewa bin son zuciya shine koyi da aiyukan jahiliya ba tare da sani ba, kuma yin hakan na sanya idanuwan mutum su rufe ba ya ganin gaskiya da kuma abinda zai sanya ya daukaka har zuwa cimma kamala.kamar yadda hadisin Imam Bakir(a.s) ya bayyana cikin riwayar da aka ruwaito cikin Tafsirin Aliyu bn Ibrahim Alkummi kalkashin tafisirin Aya ta 43 cikin suratur furkan da ta gabata, Imam Bakir (a.s) ya ce:(wannan Aya ta sauka ne kan kabilar kuraishawa, yayin da kuncin rayuwa ya riske su sai suka fita daga cikin garin Makka suka watsu cikin Daji, daga cikinsu duk wanda ya ga wata Itaciya mai kyau ko kuma wani Dotsi mai kyau ya da birgeshi sai ya bauta masa) har ila yau Imam (a.s) dangane da sababin saukar Aya ta 23 cikin suratu Jasiyar da ta gabata ya ce: (wannan Aya ta sauka ne a kan kabilar kuraishawa duk lokacin da wani abu ya birgesu sai su bauta masa, kuma hakan ya ci gaba har bayan kaurar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan gidansa tsarkaka daga nan duniya ,inda suka ci gaba da bin son zuciyarsu da kuma ra’ayinsu)
*************************Musuc*******************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, wannan batu da ya bayyana shi ke nuna cewa bautar zukata ko kuma son rai da kuma bautarsa bai takaita ba ga wani zamani ko lokaci, haka zalika bautar gumakan da Dan Adam ya sassaa su da hanunsa ya shafi maliman Addinan da aka saukar daga sama. Hakika Alkur’ani mai tsarki ya Ambato mana kisar Bal’ama bn Ba’ura wanda ya kasance daya daga cikin maluman bani Isra’ila saidai bautawa zuciyarsa da yayi da kuma son kai ya haramta masa samun daukaka da zai yi masa jagora zuwa ga kamala, a cikin suratu A’arafi Aya ta 175 da kuma ta 176, Allah madaukakin sarki ya ce:(ka kuma karanta musu labarin wannan da Muka bai wa ayoyinmu, sai ya salube daga gare su,sannan shaidan ya bi shi,sai ya zamanto daga tababbu*Da kuwa mun so da lallai Mun daukaka shi (ta yin aiki) da su(ayoyin) sai dai kuma shi ya karkata zuwa ga Duniya ya bi son ransa.Saboda haka, misalinsa kamar misalign kare ne,idan ka fafare shi ya yi lallagi (watau ya rika yin haki yana zaro harshe) idan ma ka kyale shi zai yi lallagin .Wannan shine misalin mutanen da suka karyata Ayoyinmu.saboda haka ka ba su labari don ko sa yi tunani).A cikin tafsirir Majma’ul bayyan, kalkashin tafsirin wannan Ayoyi masu albarka, an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) ya bayyana cewa:(wadannan Ayoyi sun sauka kan Bal’ama bn Ba’ura, Allah madaukakin sarki ya buga misali da shi, kuma amma wadannan Ayoyi sun kasance ga duk wanda yake bautawa son zuciyarsa, ya zabi bautawa son zuciya daga shiriyar Allah daga cikin dukkanin masu kallon Alkibla suna salla).
Masu saurare, takaicecciyar amsar wannan tambaya ita ce hakika mafi hadari daga cikin bautar gumaka da Allah madaukakin sarki ya ja hankalinmu da kadda mu bauta musu shine bin zuciya kan abinda take muradi ko kuma mu ce bautar zuciya, kuma wannan hadari ne kuma babbar barazana ce ga kowa har da wadanda aka bawa ko kuma aka sanar da su sunaye masu girma wato Ismul A’azam kamar yadda ya kasance ga Bal’ama bn Ba’ura. Baya ga haka sai wadannan tambayoyi su biyo baya minene tabbacin bautar son rai,kuma ta yaya za mu tsira daga gare ta? Kuma ta yaya za mu tabbatar da cewa mun nisantu daga sharinta? Domin jin amsar wannan tambayoyi sai a tarbemu a maku mai zuwa da yardar Allah za muyi kokarin nazari a kansu.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.