May 21, 2016 03:54 UTC

Tambayar mu ta yau ita ce mine ne misdaki to kuma tabbacin bautar son rai ko kuma bin zuciya tare da rike ta a matsayin abin Bauta?

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayar mu ta yau ita ce mine ne misdaki to kuma tabbacin bautar son rai ko kuma bin zuciya tare da rike ta a matsayin abin Bauta? A shirin da ya gabata mun bayyana cewa mafi hadari a bautawa wanin Allah shine bin son rai da yiwa zuciya biyayya domin ita zuciya tafi komai kusa ga Mutu, domin haka ne ma Allah madaukakin sarki ya galgade mu da yi kadda muyi biyayya a gareta,domin yi mata biyayya zai yi sanadiyar fadawa cikin bata mabayyani da kuma kasa cimma kamalar da aka halicci mutum domin ya cimmawa kuma ya kasance mai kadaita Allah madaukakin sarki, amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

 

*************************Musuc***************************

 

Masu saurare,kamar yadda shirin ya saba za mu fara da Littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki, A cikin Suratu Kahfi Aya ta 28 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka kuma Hakura wa kanka (da zama) tare da wadanda suke bauta wa Ubangijijnsu safe da yamma suna neman yardarsa, kar kuma ka kawar da idanuwanka daga gare su kana neman adon rayuwar duniya, kada kuma kabi wanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonmu ya kuma bi son ransa,wanda kuma al’amarinsa ya zama ketara haddi ne). a cikin suratu Taha daga Aya ta 13 zuwa ta 16, Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma Ni Na zabe ka daga Mutananka, sai ka saurari abinda za a yi ma wahayi(da shi)*Hakika Ni ne Allah,babu wani sarki in ban da Ni, to ka bauta mini,kuma ka tsaida salla don tuna Ni.*Hakika Alkiyama za ta zo, ina nufin boye ta ne don a sakawa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa.*To wanda bai ba da gaskiya da ita ba, ya kuma bi son ransa sannan ya bata,to kada ya hana ka tuna ta (idan ka bi shi) sai ka hallaka).Masu saurare, idan muka yi nazari da kyau, wadannan Ayoyi masu albarka suna ishara ne kan bautar son rai a bangaren Akida wato bin son rai da kuma abinda zuciyar mutum ta raya masa a bangaren tunaninsa da akidarsa sabanin shiriyar tsarkakekken hankali da kuma kyakkyawen tunani. Ayoyin Alkur’ani mai tsarki sun sanya son  rai da kuma biyayya ga zukata a matsayin abinda ke kalubalantar Wahayin Ubangiji, cikin surtu Najmi daga Aya ta 1 zuwa4 Allah madaukakin sarki ya ce:((Allah) yana rantsuwa da Tauraru a yayin faduwarsu,*Mutuminku bai bata ba kuma bai kauce hanya ba.*Kuma ba ya yin Magana bisa son rai.*Ba wani abu ba ne shi face wahayi da ake yuwo (masa)).

 

Har ila yau Masu saurare, wasu Ayoyi da dama sun bayyana misdakin bautar son rai a yayin mu’amala da mutane kamar yadda aka Ambato cikin Litattafan Ihkakul hukuk da Ikamatu kawaninil Adali, cikin suratu Sad Aya ta 26, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya Dawuda, Hakika mun sanya ka halifa a cikin kasa, sai ka yi hukunci a tsakanin mutane da gaskiya,kada ka bi son rai, sai ya batar da kai daga hanyar Allah.Hakika wadanda suke bacewa daga hanyar Allah suna da (sakamakon) azaba mai tsanani saboda mantawar da suka yi da ranar hisabi).a cikin suratu Nisa’I kuwa, kira ne da Allah madaukakin sarki ya yi ga mutane gaba daya na su kaucewa bautar son rai kamar karkata ga abinta zuciya ta raya wajen karkatar da hukunci ga makusanta ko masu kudi da sauraransu a yayin da ake gudanar da hukunci a tsakanin Mutane, kamar Aya ta 135 cikin suratu Nisa’I ta bayyana, Allah madaukakin sarki  ya ce:(Ya Ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku zama masu tsai da adalci masu bada shaida don Allah, ko da kuwa a kanku ne, ko kuma (a kan) ma’aifa ko dangi na jika. Idan ya zamanto mawadaci ne ko matalauci, to Allah (shi) Ya fi sanin maslaharsu, saboda haka kada ku bi son zuciya ku ki yin adalci.Idan kuwa kuka karkatar da (shedar) ko kuka ki ba da ta,to ku sani cewa Allah ya kasance Masanin abin da kuke aikatawa ne)

 

*****************************Musuc*****************************

 

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da  Aya ta 8 cikin Suratu Ma’ida ,inda a cikinta Allah madaukakin sarki ya fadakar da mu cewa a wasu lokutan son rai  da makamantan hakan ya kan biyo bayan  kiyayya  ne da take tsakanin wasu Mutane, wanda kuma bai kamata ba mu bari hakan ya yi tasiri a yayin yanke hukuncin Ubangiji da kuma cikin mu’amalarmu ta yau da kulun ba , ya kamata mu baiwa mai hakki hakinsa, idan kuma ba haka ba za mu kasance daga cikin masu bautawa son ransu da kuma biyayya ga zukatansu a aikace koma bayan bautar Ubangiji Allah subhanahu Wata’ala .A cikin Suratu Ma’ida Aya ta 8 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya Ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku zama masu tsaida hakkokin Allah sosai, masu bada shaidar gaskiya kada kin wasu mutane ya hana ku yin adalci, ku yi adalci, shi ya fi kusa da tsoron Allah.Hakika Allah masanin abin da kuke aikatawa ne)domin haka Masu saurare idan muka yi nazari za mu fahimci cewa wadannan Ayoyi masu Albarka sun bayyana misdakin bautar son rai a fuskoki guda uku : na farko kaskantar da kai domin abin duniya, kuma wannan shine abinda hadisai suka siffanta shi da bautar dukiya ko kuma bautar son rai da yin biyayya ga abinda zuciya ta raya , kuma wannan shine darasi mafi hadari ga Mutum, kamar yadda Hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka suka yi  ishara da hakan, na biyu kuwa, a bangaren Akida, wato yadda mutum zai dauki ra’ayi da kuma maganganun da suka yi daidai da ra’ayinsa ba tare da ya kiyaye dokokin kyakyawan hankali da kuma tunani mai kyau ba.amma bangare na uku shine yadda Mutum zai kasance mai bautar son ransa a aikace koma bayan Allah madaukakin sarki, ta yadda mu’amalarsa tare da Al’umma a bangarorin daban daban za ta kasance bisa yadda yake so da kuma son ransa, soyayya ko kiyayya a kan yadda yake so, ba bisa ma’aunin da Allah madaukakin sarki mai adalci ya shata ba. Dukkanin wadannan ababe su kan kasancewa bautar wanin Allah a boye da kuma hakan zai fitar da mutun daga fagen tauhidi da kuma kadaita Allah tabaraka wa ta’ala a aikace.

 

*******************************Musuc*************************

 

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.