May 21, 2016 03:57 UTC

Tambayarmu ta yau kuwa ita ta yaya za mu kaucewa Son rai da kuma bautar sa


Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan mafi hadarin bautar wanin Allah shine Son Rai, tambayarmu ta yau kuwa ita ta yaya za mu kaucewa Son rai da kuma bautar sa, domin Alkur’ani mai girma ya jan hankalin mu da mu kauce masa tare da bayyana shi a matsayin mafi hadarin bautar wanin Allah, amma kafin nan bari mu saurari tanayin da aka yi mana kan faifai.


**************************Musuc*********************************


Masu saurare, kamar shirin ya saba za mu da littafin Allah wato Alkur’ani mai girma, a cikin Suratu Hajji Aya ta 31 Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuna masu mika wuya ga Allah, ba masu tarayya da shi ba.Wanda kuwa duk ya yi tarayya da Allah, to kamar ya fado ne daga sama,sai tsutsaye suka fauce shi, (suka yanyana shi) ko kuma iska ta jefa shi cikin wani wuri mai zurfi (ta rugurguzashi) a tafsirin wannan Aya mai girma Shekh Saduk ya ruwaito hadisi cikin Littafin Attawhid daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(mika wuya ga Allah shine halittar da Allah madaukakin sarki ya halicci mutane a kansa kuma babu wani canji ga halittar Allah, sannan Imam (a.s) ya ci gaba da cewa Allah ya halicce su a kan sani).abinda Imam (a.s) yake nufi da sani wato ya halicci mutane domin su san shi idan kuma suka sanci su bi shi, kuma su bauta masa wanda hakan shi ke ceton Bawa daga bautar son rai da kuma bin sha’awarsa kamar yadda karshe wannan Aya take ishara.A cikin Suratu Bakara Aya ta 135, Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma sai suka ce : “ku zama Yahudawa ko Nasara kwa zama shiryayyu.” Ka fada (musu Ya Muhamadu) A’a (sai dai mu bi )hanyar Ibrahimu mai kaucewa (Yahudanci da Nasaranci),kuma bai kasance daga masu shirka (da Allah) ba) dangane da tafsirin wannan Aya Imam Ja’afaru Sadik (a.s) cikin Tafsiru Ayyashi ya bayyana cewa (mike wuya ga Allah shi ne musulinci) har ila yau cikin wannan Littafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce (babu abinda mike wuga ga Allah wato Addinin musulinci ya rage hatta da hukunci aske gashin baki, yankan farce da kuma sallatu), wannan hadisi na Imam Bakir (a.s) yana ishara ne kan cewa babu wani Abu na tsarin rayuwar Dan Adam da Addinin musulinci ya bari face ya bayyana hukuncin sa. A cikin Suratu Ali Imrana Aya ta 67 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ibrahimu bai kasance  Bayahude ba kuma shi ba Banasare ba ne, sai dai ya kasance mai bin hanya ta gari (kuma) Musulmi, bai kasance daga masu shirka ba) ya zo cikin Littafin Usulul kafi kan tafsirin wannan Aya Shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(ma’anar fadar Allah madaukakin sarki mai bin hanya ta gari (kuma) Musulmi shine mai ikhlasi cikin al’amuransa da babu kamshin bautar gumaka ko wanin Allah a cikinsu. Har ila yau cikin suratu Ali Imrana Aya ta 95 Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(Ka ce:”Allah ya yi gaskiya (a labarin da ya bayar) saboda haka sai ku bi Addinin Ibrahimu mai bin hanya ta gari kuma bai zamanto daga mushrikai ba) A cikin Tafsiri Ayyashi,an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Husain (a.s):(ban san wani da ya fi sanin tafarkin Annabi Ibrahimu ba kamar mu da Mabiyanmu)


***************************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Aya ta 125 cikin suratu Nisa’I, Allah tabaraka wata ala ya ce:(Ba kuma wanda ya fi kyakkyawan Addini sai wanda ya mika wauyansa ga Allah,yana mai kadaita shi ya kuma bi hanyar Ibrahimu mikekkiya. Allah kuwa ya rike Ibrahimu badadayi), cikin suratu Yunus Aya ta 105 Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma (an umarce ni ) da cewa “ka tsai da fuskarka ga Addinin Allah madaidaici, kada kuma ka kasance cikin mushrikai) cikin wadannan Ayoyi masu girma da makamantansu za mu iya samun amsar tambayarmu kamar haka: da farko hanyar tsira daga bautar son rai ko bin zuciya da dukkanin nau’in shirka zai kasance ta hanyar mika wuya ga Allah wato shine tauhidi, ma’ana aikin da shari’ar Addinin musulinci, biyayya ga Umarnin Allah da kuma kaucewa saba masa a dukkanin Al’umuran rayuwar Dan Adam, wanda kuma yin hakan zai sanya duk wani shiri da kuma aiyukansa su karkata zuwa sahihiyar hanya wacce za ta yi masa tabbacin samun sa’ada a nan duniya da Lahira.kuma wannan shine abinda Addu’o’I na iyalan gidan Annabin Rahama amincin Allah ya tabbata a gare su, suka yi ishara da shi, yayin da Bawa ya san cewa ya kamata ya meka bukatar sa wajen Allah madaukakin sarki na ya sanya sonka bisa abinda Allah madaukakin sarki yake so, misali cikin Addu’ar  da aka son ko wani mumuni ya karanta bayan ya ziyarci Imam Jawad (a.s) ga Addu’ar (Ya Ubangiji ga yi Salati ga Annabi Muhamadou da iyalan gidansa tsarkaka kuma ga gwada mini gaskiya gaskiya in bita, ga gwada mini karya karya in nuisance ta, kada ka sanya na kasa gane ta in bi son rain aba tare da shiriya daga gareka , ka sanya abinda nike yi biyayya ga umarninka, ka kuma sanya yardarka a gareni, ka shiryar da ni daga abinda ya sassaba na gaskiya domin yardarka, hakika kaine mai shiryar da wanda yake so zuwa ga hanya madaidaiciya) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzita mu da shiriyar sa domin darajar ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.


*******************************Musuc*************************


Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.