Abin Bauta Da Aka hana A Bauta Musu
a shirin da ya gabata mu yi bayyani kan yadda za mu kaucewa bin son rai saboda mumunar makonsa,sai kuma a yanzu ganin cewa lokaci ya canza ba a bautar gumaka da ake sassaka da hanu, shin a wannan zamani wasu irin abinda bauta ne da Allah madaukakin sarki ya hanemu da bautawa cikin Alkur’aninsa mai girma, domin haka masu saurare tambayarmu ta yau nada matukar mahimancin domin sanin amsarta shi zai shiryar da mu wajen tabbatar da Tauhidi na gaskiya da aka umarce mu da shi,
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mu yi bayyani kan yadda za mu kaucewa bin son rai saboda mumunar makonsa,sai kuma a yanzu ganin cewa lokaci ya canza ba a bautar gumaka da ake sassaka da hanu, shin a wannan zamani wasu irin abinda bauta ne da Allah madaukakin sarki ya hanemu da bautawa cikin Alkur’aninsa mai girma, domin haka masu saurare tambayarmu ta yau nada matukar mahimancin domin sanin amsarta shi zai shiryar da mu wajen tabbatar da Tauhidi na gaskiya da aka umarce mu da shi, amma kafin nan bari mu saurari wannan.
**************************Musuc******************************
Masu saurare, a shirin da ya gabata mun bayyana cewa bin son rai tare da yiwa zuciya biyayya ga Mutum ba tare da la’akarin hukuncin ubangiji ba shine mafi hadari bautar wanin Allah domin haka ne ma Nassosi da dama suka umarce mu da abinda muke so ya kasance bisa tsari da kuma abinda Allah madaukakin sarki ke so, don haka son rai da bin abinda zuciya ke so shine ubangijin ciki da bautarsa ta katange bautar Allah madaukakin sarki, kuma shine abinda bauta na farko koma bayan Allah madaukakin sarki kuma shine mafi hadari daga Aloli barkatai.Abin bauta na biyu daga Alloli barkatai shine Shaidan jefeffe, hakika Nassosin Alkur’ani da na hadisai sun ja hankalinmu game da bautamasa, a cikin suratu An’ami Aya ta 100 Allah madaukakin sarki y ace:(Suka kuma sanya Aljannu abokan tarayya da Allah, alhali kuwa shi ya halicce su, suka kuma kirkira masa ‘ya’ya maza da Mata ba tare da sani ba, tsarki ya tabbata a gareshi, kuma ya daukaka daga irin abin da suke siffantawa) domin haka mafi hadari daga wadancan da aka rika abokanin tarayya da Allah daga cikin Aljannu shine shaidan jefeffe,kuma shine ya yi rantsuwa a kan cewa zai duk iya kokarinsa domin batar da Bani Adama ya kuma toshe musu hanyar isa zuwa ga rahamarsa da kuma mikekiyar hanya ta kadaita Allah tabarka wa ta’ala.A cikin Suratu Nisa’I daga Aya ta 116 zuwa 120 Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika Allah ba ya gafarta a yi shirka da shi, yana kuma gafarta wanin wannan ga wanda yake so, wanda kuwa duk ya yi shirka da Allah to ba shakka ya bata manisanciyar Bata*Ba wanda suke bauta wa wanin (Allah)in ban da Mata, ba wanda kuwa suke bauta wa a hakika sai shaidan mai tsaurin kai*Allah ya tsine masa (shi) kuma ya ce Ba shakka zan sami wani rabo Kayyadajje daga Bayinka*Ba shakka kuwa zan batar da su, lallai kuma zan jefa musu guri a zukatansu, hakika kuma zan ingiza su (cikin munanan aiyuka), sannan za su rika gutsuttsure kunnuwan dabbobi, zan kuma ingiza su su canja halittar Allah, Duk wanda kuwa ya riki shaidan majibincin Al’amuransa ya bar Allah, to ba shakka ya tabe mabayyaniyar tabewa*Yana yi musu alkawari yana kuma sa musu guri, ba kuwa abin da shaidan yake musu alkawari da shi sai rudi kawai) Masu saurare wannan shi ke nuna cewa shaidan la’ancecce shine mafi hadari daga cikin allolli barkatai na wajen Dan Adam, yayin da Nafsul Ammaratun bi su’I wato ran da take karkata zuwa ga sharri ita ce mafi hadari shirka a cikin wujidin Mutum,kuma an saukar da Ayoyi da dama cikin Alkur’ani mai girma da suke galgadinmu na mu guji bin shaidan , bauta masa da karkata zuwa waswasinsa, wannan dalili ne kan rawan da yake takawa wajen kiyayya da Dan Adam da kuma yadda yake shiga cikin jikin mutum yana yi masa waswasi na katangeshi ga isa zuwa ga tsarkakekke tauhidi ko kuma kadaita Allah tabaraka wa ta’ala, baya ga haka Ayoyi da dama sun bayyana matsayin shaidan wajen ci gaba da dawama a kan batar da Bani Adama har zuwa bayyanar Imam Mahdi (a.s).
**************************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai koma kan haskeda kuma na biyu wata tafarkin iyalan gidan Annabta tsarkaka, a cikin Tafsiri Ayyashi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) Ya ce:(Hakika Allah ya jinkirtawa Iblis har zuwa lokacin da za a tayar da Imam Zaman (a.f)).kamar yadda Ayoyi da dama suka bayyana cewa Shaidan shine shugaban bata da kuma abin bauta barkatai wadanda suke nisantar da Bayin Allah suke kuma kiransu zuwa shirka ko kuma bautar wanin Allah a dukkanin bangarorinsa, a cikin Littafin Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Jawad (a.s) ya ce (duk wanda ya kira wani a matsayin wanda zai biya masa bukata, hakika ya bauta masa, idan ya kasance yana kirar Allah to hakika ya bautawa Allah, idan kuma ya kasance yana kirar Shaidan, hakikac ya bautawa shaidan) , Masu saurare shaidani, kamar yadda Ayoyin Alkur’ani masu tsarki suka bayyana wata halitta ce dake yin tasiri a jikin mutun wajen sanya masa kokonto game da mahalicinsa kuma yak an sanya mutum girman kai wajen bautar Allah madaukakin sarki da kuma kaskantar da kai ga iradarsa da kuma waliyansa masu gaskiya wanda suka cimma jarabawar Ubangijinsu suka samu matsayi na musaman a wajensa sune halifofin Allah a doron kasa ma’asumai amincin Allah ya tabbata a gare su kuma sune masu Magana da sunan Allah tabaraka wa ta’ala, domin haka ne ma shi shaidani ya kasance babban makiyin Allah madaukakin sarki, bautar sa kuma tana kai mai yenta zuwa ga aikata shirka.A cikin wata Khudubarsa yayin da yake bayyana girman Iblis wajen yiwa Annabi Adamu sujasa bayan ya bayyana halittar Annabi Adamu (a.s), shugaban Masu kadaita Ubangiji Imam Aliyu bn Abi talib (a.s) ya bayyana cewa:(makiyin Allah Iblis shugaban masu bangaranci, magabacin masu girman kai wanda shi ne ya sanya asalin ta’asubanci ko kuma bangarenci,ya yi jayayya da Allah yayin da yansa rigar girman kai, ya kuma tsire ma kansa rigar girma, shi bu ku k aba yadda Allah ya kaskantar da shi, saboda girman kansa sannan ya sanya shi a duniya a bin ki ya kuma tanadar masar wutar sa’ida a Lahira)
Masu saurare wannan bayani na Imam Ali (a.s) na bayyana mana mumunan karshe na bautar shaidan, wanda zai sanya mutum mai rauni a Duniya, a Lahira kuma Azaba mai radadi, da fatan Allah madaukakin sarki ya tsare mu da hakan domin albarkar riko da wulaya da kuma yin biyayya ga shugabanin masu kadaita Allah, masu shiryar da bayin sa mushlisai Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma da iyalan gidansa tsarkaka.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.